An Bude Cibiyoyin Ciyar Da Masu Azumi A Dan Modi Na Garin Kafin Hausa
Published: 7th, March 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi kira ga masu dafa abincin buda baki a karamar hukumar Kafin Hausa da su kasance masu gaskiya da adalci wajen ciyar da masu azumi a wannan watan na Ramadan.
Mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ayyuka na musamman, Alhaji Abdulkadir Bala T.O yayi wannan kiran yayin da yake duba cibiyoyin ciyar da masu azumi na Dan Modi a cikin garin Kafin Hausa.
Alhaji Abdulkadir Bala T.O ya yaba da kokarin wasu daga cikin masu dafa abincin, yayin da ya nuna rashin jin daɗi kan yadda wasu suka karya yarjejeniyar da aka gindaya masu.
A nasa jawabin, Shugaban karamar hukumar Kafin Hausa, Alhaji Abdullahi Sa’idu Nalayi, ya tabbatar da cewar, Karamar hukumar za ta ba da dukkan goyon bayan da ya dace don gudanar da shirin cikin nasara.
Shima a jawabin sa na godiyan masu dafa abincin, Abba Darakta Kafin Hausa ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa kaddamar da shirin ciyar da masu azumi.
Ya kuma yi alkawarin ci gaba da kasancewa masu gaskiya da adalci don cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
An Horas Da Mata 600 Kan Abincin Yara Mai Gina Jiki A Jigawa
A wani yunkuri na yaki da rashin abinci mai gina jiki da kuma karfafa tattalin arzikin mata a jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi ya jagoranci bikin yaye mata 600 da suka samu horo kan yadda ake sarrafa abincin yara mai gina jiki daga kayayyakin da ake samarwa a gida, wanda aka fi sani da “Tom Brown”.
Malam Umar Namadi ya bayyana wannan shiri a matsayin wata dabara ta cikin gida da aka kirkira domin shawo kan matsalolin rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara, da kuma karfafa tattalin arzikin mata.
“Muna matukar godewa Allah da ya ba mu hikima da basira don kirkirar wannan tsari wanda zai taimaka mana mu cimma manufofi da dama a lokaci guda.” In ji shi.
“Bayan bai wa wadanda aka horar damar samun ingantacciyar hanyar dogaro da kai, wannan kuma wata babbar dabara ce wajen yaki da rashin abinci mai gina jiki a cikin yara. Hakan kuma zai taimaka wajen hana matsalolin nakasa a kwakwalwa, domin kare damar girman yaron yadda ya dace.”
Gwamnan ya jaddada cewa Tom Brown, wanda wasu ke kira da Kwashpap, an tabbatar da ingancinsa wajen magance matsalar rashin matsakaicin abinci mai gina jiki (Moderate Acute Malnutrition – MAM) ta hanyar hadin kayan gida kamar gero, gyada da wake.
Ya kara da cewa wannan shiri na da cikakken daidaito da manufofin gwamnatin jihar na bunkasa abinci mai gina jiki, wanda ya fara haifar da sakamako mai kyau.
A cewarsa, kowace daga cikin matan 600 da suka amfana da shirin ta samu kayan fara sana’a da suka hada da injin rufe roba da kayan masarufi domin farawa da sarrafa Tom Brown a matakin gida.
Namadi ya bayyana cewa kananan hukumomi da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a fadin jihar za su hada gwiwa domin tabbatar da amfani da kuma shigar da wadannan kayayyaki cikin shirye-shiryen inganta abincin yara.
Ya ce, horar da wadannan mata 600 wani bangare ne na kokarin gwamnati wajen hanzarta samun ci gaba a fannin kula da rayuwar al’ummar, da ingantacciyar lafiyar yara.
Gwamna Namadi ya kuma sake jaddada kudirin gwamnatinsa na rage dogaro da kayan abinci masu tsada da ake shigowa da su daga kasashen waje, ta hanyar bunkasa hanyoyin cikin gida masu saukin samu da kuma arha.
Ya sanar da cewa jihar Jigawa na cikin jerin jihohin da ke amfana da shirin ANRiN na Bankin Duniya, wanda ke mayar da hankali kan kara samun damar kula da lafiyayyen abinci ga mata da yara ‘yan kasa da shekaru biyar.
“Babban burin wannan shiri shi ne kara yawan amfani da ingantattun hanyoyin kula da abinci ga mata masu juna biyu da masu shayarwa da kuma yara ‘yan kasa da shekaru biyar. Wannan yana da nasaba da hangenmu cewa shirin ANRiN zai taka rawar gani wajen hanzarta ci gabanmu ta bangaren samar da abinci mai gina jiki ga yara.”
Usman Muhammad Zaria