Jinkirta Sahur Da Gaggauta Buda-baki
An karba daga Anas, ya ce, Annabi SAW ya ce “ku dinga yin Sahur, domin shi yin Sahur akwai albarka a cikinsa”, ba burgewa ba ce mutum ya dinga cewa ‘ai ni ban yin sahur’ albarka mai yawa ta wuce shi.
An karba daga Sahlu dan Sa’adu Allah ya kara yarda da shi ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce “Mutane ba za su gushe ba cikin alkairi muddin sun gaggauta yin buda-baki” Ma’anar wannan hadisi, sabida Allah ya fada cikin Alkur’ani “summa atimmus siyama ilallai – sannan ku cika azumi zuwa dare” sai Annabi ya koya mana sunnarshi zuwa dai-dai lokacin da ya dace na buda-bakin (ba cikin dare Allah yake nufi ba), sai Annabi SAW ya bayyana da fadarsa ku gaggauta yin buda baki – da rana ta fadi, an sha ruwa.
Manzon Allah (SAW) ya kasance in an sha ruwa yana fara bude baki ne da addu’a inda yake cewa “Allahumma laka sumtu wa ala rizkika afdartu – Ya Allah a gareka nake Azumi kuma cikin arzikinka nake buda-baki” mai azumi cikin hadarar Allah yake don haka a wurin mai arziki mai azumi yake shan ruwa.
An karba daga Abi Zaidil Gifari ya daga hadisin zuwa ga Annabi SAW yace “Ma zala Ummati bi khairin ma anta … – Al’ummata ba za ta gushe ba tana cikin alkairi matukar tana yin buda-baki sannan kuma ta jinkirta sahur”. Shi buda-baki ana son gaggautawa, sahur kuma ana son jinkirtawa zuwa karshen dare.
An karba daga Abdullahi bin Maz’unu yana cewa Sahabban Manzon Allah (SAW) sun kasance mafi gaggawar mutane buda-baki sannan mafi jinkirin mutane sahur. Baihaki ne ya ruwaito hadisin da sanadinsa ingantacce.
Abu Dawud ya ce, Abu Abdullahi ya ce “Idan Mutum ya yi kokonto cikin alfijir to ya yi ta cin abincinsa har sai ya sakankance alfijir ya futo.” Wannan ita ce nasabar Abdullahi bin Abbas da Adda’u da Auza’i da Ahmadu bin Hambali.
An karba daga Anas Allah ya kara yarda da shi ya ce “Manzon SAW ya kasance yana buda-baki da danyen dabino, in ba a samu danye ba sai ya yi da busassshe idan ba a samu ba sai ya sha ruwa kadan”. Abi Dawud da Tirmizi suka ruwaito Hadisin. Addinin Musulunci balaraben addini ne, dabino yana daga cikin alamun addinin musulunci don haka ya dace gwamnati ta kula da sana’ar dabino musammam lokacin azumin watan Ramadan. Sabida wannan dabinon da muke buda baki da shi, ba musan shekararsa nawa da yanko shi kasa ba.
Amma akwai wata hikima da ake yi wajen maida busassshen dabino zuwa danyen dabino. Da safe, sai mutum ya dibo iya wanda zai yi buda baki da shi, ya wanke dabinon, sai ya nemo ruwan zafi, ya jika a ciki sai ya kulle robar da ya jika dabinon zuwa lokacin buda-bakin.
Kiyaye harshe daga alfasha
An karba daga Abi Huraira Allah ya kara yarda da shi, shi kuma ya karba daga Manzon Allah (SAW) ya ce “Azumi ba wai barin ci da sha ne kawai azumi ba, azumi barin maganar batsa da maganar da ba ta dace ba, idan wani ya zage ka ko ya dame ka, to ka ce masa ni ina azumi”, Hakim ya ce ingataccen hadisi ne.
“Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda bai bar gulma da kagen karya da kitsa sharri ba a azumi, Allah ba shi da wata bukata da azuminsa.”
Ya zo daga Annabi (SAW) yana cewa “da yawa wasu ba su da Ladan azumi sai dai wahalar kishirwa da shan yunwa kawai, da yawa mutum ke sallar dare amma ba su da ladan sallar sai dai wahalar tsayuwa kawai.” Hadisin Ingatacce ne abisa sharadin Bukhari.
Yin aswaki da azumi abu ne mai kyau
Asiwaki da kyauta da yawaita karatun Alkur’ani da yawaita ibadu a cikin watan Ramadan duk Allah yana son hakan musamman a goman karshe ta watan.
Ya zo a cikin ingatattun hadisai daga Amiru yana cewa “da yawa na ga Annabi (SAW) ba daya ba biyu ba kai ba za su kidayu ba yana yin asiwaki kuma yana cikin azumi.”
Sayyada A’isha uwar Muminai ita kuma ta saukaka ta ce mutum zai iya sa abun kamshin baki a bakinsa, don bakin ya zama ba ya wari ya yi kamshi, sabida su Larabawa al’adarsu suna sumba, sharadi dai kar ya shiga makogoro. Wannan ijtihadi ne na Sayyada A’isha. Mace mai girki ta iya dandanar gishiri sai ta tofar ko mai sana’a irin wacce sai an dandana ake gane ingancin sana’ar, za su iya dandanawa sai su zubar. Haka mai alwala, in ya tofar da ruwan bakinsa sau uku, abin da ya biyo baya ba ruwa ba ne, miyau ne.
Bukhari ya ruwaito daga Abdullahi bin Abbas cewa Manzon Allah (SAW) shi ne mafi kyautar mutane amma babban lokacin kyautar Manzon Allah (SAW) ita ce Ramadan, lokacin da Mala’ika Jibrilu ke zuwa su yi musaffar Alkur’ani.
Duk abin da Mala’ikah Jibrilu ya zo wa Annabi da shi a wannan shekara, to sai sun yi musaffar wannan karatun a watan Ramadan. Sabida haka ne Annabi (SAW) yake ninka kyautarsa a watan Ramadan.
An ruwaito daga Sayyada A’isha ta ce Annabi (SAW) idan goman karshen watan Ramadan ta shigo yana raya daren duka.
Mai azumi zai iya shiga Shawa ya yi wanka, zai iya shiga kogi matukar ruwa ba zai shiga cikinsa ba, mai azumi zai iya zuba ruwa a kansa don ya ji sauki, kuma zai iya kuskure bakinsa. Ba laifi don an yi kiran sallar fitowar alfijir, mutum ya yi wankan Janaba. Wanda ya yi mafarkin saduwar aure da rana a watan azumi bai bata masa azumi ba,. Wanda ruwa ya kubuce masa lokacin alwala, azuminsa bai lalace ba, amma zai rama daya bayan Ramadan. Kurar kan hanya ba za ta bata wa mutum azumi ba, duk abin kasuwancin da sai an dandana ake gane ingancinshi, dandanawar ba za ta karya azumin ba.
Abin da ke karya azumi sun hada da: janyo amai da gangan, zuwan haila, zuwan haihuwa, janyo maniyyi da gangan, ci ko sha daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana, saduwa da iyali daga futowar alfijir zuwa faduwar Rana.
Mutum wanda zai ba da zakkar buda-kai zai iya yin ta yanzun (farkon azumi) ya bai wa talakan da bai da dama don ya samu abun buda-baki da shan ruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani
Gwamnatin Jihar Jigawa ta horas da Malaman makarantun sakandare kimanin dubu 20 ilimin fasahar sadarwar zamani (digital).
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) da Cibiyar Zaman Lafiya ƙarƙashin jagorancin Farfesa Hauwa Ibrahim da take Amurka, a ziyarar ban girma da suka kai a gidan gwamnati da ke Dutse.
Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti AllahYa ce: “Mun gabatar da cibiya ta dijital don malamai, don sadarwa da kuma kula da ilmantarwa a matakin farko, mun sanya hannu kan haɗin gwiwa na shekaru biyar tare da NewGlobe don ƙarfafa ƙa’idojin rubutu da ƙididdiga ta amfani da kayan aikin dijital.
“Don haka shirin ku ya yi daidai da gyare-gyaren da muke da su kuma yana ƙara ƙimar ilimi matuƙa.” In ji Namadi.
Gwamna Namadi ya kuma nanata ƙudirin gwamnatin Jigawa na ɗorewar shirin, yana mai cewa, “Ina tabbatar muku: Za mu mallaki wannan shiri, za mu ci gaba da faɗaɗa shi, Kwamishinoninmu na ilimi a matakin farko da kuma na manyan makarantu za su sa ido a kansa.”
Darakta mai riƙon ƙwarya na dijital a Hukumar NITDA, Dokta Ahmed Tambuwal ya bayyana hangen nesa na ƙasa da ke jagorantar shirin.
“Muna nan a matsayin wani ɓangare na Hukumarmu ta NITDA na ci gaba da sadaukar da kai don aiwatar da ajandar Sabuwar Najeriya na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
“Babban ginshiƙi na wannan ajandar ita ce rarraba tattalin arzikin Najeriya ta hanyar fasahar dijital.”
Tambuwal ya bayyana cewa, NITDA tana ci gaba wajen cimma buri na kashi 70% na ilimin zamani a shekarar 2027, yana mai jaddada buƙatar haɗin gwiwa don cimma burin.