Hukumar Sibil Difens za ta ɗauki sabbin jami’ai
Published: 6th, March 2025 GMT
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta samu sahalewar Shugaban Ƙasa na ƙara daukar sabbin ma’aikata.
Babban Kwamandan Hukumar, Ahmed Aifi, na ya sanar da haka, a yayin ƙaddamar da Baban Ofishin Yanki na Hukumar a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke yankin Babban Birnin Tarayya a ranar Laraba.
“Nan gaba kaɗan za mu ɗauki ’yan Najeriya masu kyawawan ɗabi’u a matsayin jami’ai a Sibil Difens, kuma muna godiya ga shugaban ƙasa bisa wannan dama da ya ba hukumar,” in ji shi.
Ya bayyana cewa Hukumar ta fara shirye-shiryen ɗaukar sabbin, amma sai nan gaba za ta sanar da ranar fara ɗaukar tasu.
An yanke wa masu fyaɗe 3 hukuncin dandanƙewa da rataya a Kaduna An kama korarren jami’in tsaro da ke sayar wa ’yan ta’adda makamai NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba?Ya kuma yaba wa Majalisar Ƙaramar Hukumar Bwari bisa gina ofishin, wanda ya ce zai taimaka wajen inganta tsaro.
Olusola Odumosu, wanda shi ne Kwamandan Hukumar, ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar, John Gabata da ya samar da ofishin cikin kyakkyawan yanayi ga jami’an hukumar tsaron.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bwari daukar sabbin jami ai Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Yi Allurar Rigakafi Ga Dabbobi Sama Da Miliyan Daya A Babura
Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa.
Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana.
A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar.
Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar.
Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu.
Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin dadinsa game da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a yankin, yana mai kira gare su da su ci gaba da gudanar da rayuwa cikin fahimta da hadin kai.
Haka zalika, yayin taron, Shugaban Sashen Noma da Albarkatun Kasa, Malam Lawan Sabo Kaugama, ya bayyana cewa an ware cibiyoyi guda goma sha biyu domin gudanar da aikin rigakafin wanda ake sa ran zai dauki kwanaki hudu.
Ya yaba da kokarin gwamnatin jiha da ta karamar hukuma wajen samar da allurar rrigakafn da kuma duk wasu kayan aiki da ake bukata.
Usman Muhammad Zaria