Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio
Published: 5th, March 2025 GMT
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta gabatar da ƙorafinta a gaban Majalisar Dattawa kan Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, bisa zargin cin zarafi da kuma tauye mata haƙƙi a majalisa.
A ranar 20 ga watan Fabrairu ne rikici ya ɓarke a zauren majalisar, lokacin da Shugaban Majalisar, Akpabio, ya umarci wani ma’aikacin majalisa da ya fitar da Sanata Natasha daga zauren, bayan da aka ce ta ƙi komawa sabuwar kujerar da aka ware mata.
Wannan lamarin ya jawo suka daga ƙungiyoyi da mutane da dama, inda suka nemi a yi bincike kan abin da ya faru.
Abin da Sanata Natasha Ta Gabatar Wa MajalisaSanata Natasha ta gabatar da ƙorafinta ga Majalisar Dattawa, inda ta ce: ’Ina gabatar da ƙorafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, bisa cin zarafi na lalata da kuma amfani da muƙaminsa wajen tauye min haƙƙi na ’yar majalisa.”
Daga nan sai ta sauka daga kujerarta zuwa gaban Akpabio, inda ta rusuna sannan ta ajiye takardun ƙorafinta.
Shugaban Majalisar, Sanata Akpabio, ya karɓi ƙorafin, inda ya miƙa shi ga Kwamitin Ladabtarwa da Tsare-Tsare domin gudanar da bincike.
Ya ce: “Na miƙa wannan ƙorafi ga kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa domin yin bincike kuma su dawo mana da rahoto cikin gaggawa.”
Duk da haka, yayin da ake tattaunawa, Babban Mai Tsawatarwa na Majalisa, Sanata Mohammed Monguno, ya ce ba za a iya tattauna ƙorafin ba saboda yana da nasaba da shari’ar da ke gaban kotu.
Sai dai Sanata Natasha ta musanta hakan, inda ta bayyana cewa ƙarar da ake yi a kotu ba ta shafi ƙorafin da ta gabatar ba.
Ta bayyana cewa abin da ke gaban kotu na da nasaba da wani hadimin Akpabio, Patrick Mfon, wanda ya zarge ta da sanya kayan wanda ba su dace ba a majalisar.
Martanin Sanata AkpabioBayan karɓar ƙorafin, Akpabio ya musanta duk wasu zarge-zarge da Natasha ta yi masa.
Ya ce: “Dangane da zargin da ake yi min, babu lokacin da na taɓa yunƙurin cin zarafin Sanata Natasha ko wata mace.
“Mahaifiyarmu ta ba mu tarbiyya tun muna ƙanana, kuma ni ma ina da ’ya’ya mata huɗu. Bugu da ƙari, lokacin da nake gwamna, an taɓa karrama ni a matsayin gwamnan da ya fi kowa girmama mata.”
Akpabio ya kuma jaddada cewa lamarin na gaban kotu, don haka ya buƙaci kafafen watsa labarai da al’ummar Najeriya su jira sakamakon shari’a.
Sanata Natasha Ba Ta Samu Goyon Bayan ’Yan Majalisa BaBayan gabatar da ƙorafin, mafi yawancin ’yan majalisar dattawa da suka yi tsokaci ba su goyi bayan Natasha ba, har da sanatoci mata ’yan uwanta.
Wasu daga cikinsu sun ce ƙorafin ba shi da tushe, don haka bai kamata a tattauna shi a zauren majalisar ba.
Wasu kuma sun nemi a yi zaman sirri domin tattauna lamarin, amma Akpabio ya ƙi amincewa da hakan saboda akwai baƙo da ya ziyarci majalisar daga Birtaniya, wanda ke kallon yadda zaman majalisar ke gudana.
Daga ƙarshe, yayin da ’yan majalisar suka ci gaba da aikinsu, Sanata Natasha ta fice daga zauren majalisar domin nuna rashin jin daɗinta da yadda lamarin ya kaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwamiti Ƙorafi Majalisar Dattawa Zargin Cin Zarafi Shugaban Majalisar gaban Majalisar
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi: “Ba ma wasa game da batun inganta uranium, wanda hakkin al’ummar Iran ne”
Ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ba za ta amince da duk wata tattaunawa kan dakatar da shirinta na inganta makamashin Uranium gaba daya ba.
Ya bayyana hakan ne a gefen ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Oman, inda ya jaddada cewa, bai kamata tattaunawa da Amurka za ta hada da batun ba wanda Tehran ba za a amince da shi ba.
Araghchi ya ce, ana ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma batun tace uranium shi ne ya kasance babban abin da ake samun sabani.
Ya kuma kara da cewa, an yi shawarwari da ministan harkokin wajen Oman game da shirya wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da Amurka.
Ministan ya jaddada cewa Iran na daukar tace sinadarin Uranium a matsayin wani hakki na kasa wanda ba za’a iya tauye mata ba, kamar yadda yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta tanada.