Hamas Ta Bukaci Falasdinawa A Birnin Qudus Su Sabawa Dokar Takaita Yawan Masu Shiga Masallacin Al-Aksa A Kudus
Published: 2nd, March 2025 GMT
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kashe akalla yara 16 tun farkon wannan shekara ta 2025 a yankin yamma da kogin Jordan.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ayed Abu Eqtaish, daraktan kungiyar ‘ The Defense for Children International’ a yankin yamma da kogin Jordan yana fadar haka.
Eqtaish ya kara da cewa, rashin magana da kuma takawa gwamnatin yahudawan birki yana sa ta kara yawan kashe yara Falasdinawa a duk sanda ta ga dama.
Kafin haka wani rahoton MDDya bayyana cewa idan ba’a hana HKI da karfi ba, to ba za ta takaita kisan kiyanshi a Gaza kadai ba, zata fadadashi zuwa yankin yamma da kogin Jordan.
Sojojin HKI sun ta aikata kissan kiyashi a gaza a yain fin karfin da ta yi a Gaza na tsawon watanni 15, inda ta kashe fal;asdinawa fiye da 61,000 kafin a tsagaita wuta a ranar 19 ga watan Jenerun da ya gabata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa).
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“
Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman ayyuka da shirye-shirye tare da Bankin Duniya, Ma’aikatar Harkokin Waje, Harkokin kungiyar kasashen renon Ingila da Ci Gaban Birtaniya (FCDO), da Tarayyar Turai (EU), wanda hakan ya bata kwarewar da ta dace da sabon mukaminta.
Ya kara da cewa, Aisha Mujaddadi ta kasance a cikin kwamitoci da dama a matakin jiha da na tarayya, kuma ta taba zama memba a kwamitin gudanarwa na Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kaduna.
Sakataren Gwamnatin a jaddada cewa an yi nadin ne bisa cancanta, kwarewa da gaskiya, wanda ke nuna amincewar wannan gwamnati da kwarewar Aisha Mujaddadi.
Ya bayyana fatan cewa sabuwar Darakta Janar din za ta sauke nauyin da aka dora a kanta tare da kawo ci gaba mai ma’ana ga Jihar Jigawa.
Ya kara da cewa, nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin Darakta Janar na InvestJigawa ya fara aiki nan take.
Usman Muhammad Zaria