A wani bidiyo mai ban mamaki da Hukumar Kashe Gobara ta yankin Tulsa da ke kasar Amurka ta fitar ya nuna yadda wani kare ya yi sanadin tashin wuta a wani gida ta hanyar tauna fakitin batirin Lithium.
Hukuma ta kama karen bayan gano hakan a bidiyon mai ban mamaki, wanda ya nuna shi yana tauna fakitin batirin lithium-ion wanda mai shi ya bari.
Bayan dan lokaci da fara taunawa, baturin ya fara tarwatsin wuta, sannan ya yi bindiga, lamarin da ya sa karen da wata kyanwa da ke kwana a kusa da gidan tserewa don tsira da rayukansu.
An yi sa’a, duk dabbobin sun tsere ta kofar gidan, wutar ba ta yi musu lahani ba, amma gobarar ta yi mummunar barna a gidan.
Masu kashe gobara a yanzu suna amfani da bidiyon a matsayin gargaɗi game da barin batir lithium a wurin da yara da dabbobi za su iya kaiwa.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Kashe Gobara ta Tulsa ya ce, duk da irin barnar da gobarar ta yi, abubuwa na iya zama mafi muni idan akwai mutane da ke kwana a ciki, ko kuma yadda za a iya tsira da dabbobi marasa galihu.
“Lokacin da wannan wutar batirin ta fara ba tare da katsewa ba, ta haifar da zafi da samar da iskar gas mai konewa da guba har ma da tartsatsi,” in ji daya daga cikin ma’aikatar kashe gobaran, Andy Little game da makamashin da yake cikin kananan baturan lithium.
Ya ce, “Yana da mahimmanci ku bi ka’idojin masana’anta lokacin amfani da baturan lithium-ion, kawai amfani da caja da aka yarda da su da adana su a wajen da yara da dabbobin gida.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Jaridar The Guardian Mafi Yawan ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Ne A Gidan Yarin Kasar Girka
Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan
Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma dokar ta kunshi hukunta masu laifin daurin shekaru 25 a gidan yari.
Jaridar ta The Guardian ta ruwaito cewa: Masu fasakwaurin mutane da aka yanke wa hukunci sun zama rukuni na biyu mafi girma a gidajen yarin Girka, bayan masu safarar miyagun kwayoyi.
Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Sudan su ne rukuni na hudu mafi girma na masu neman mafaka a kasar Girka, inda suka zarce ‘yan ciranin gargajiya na wasu kasashe kamar ‘yan Siriya da Falasdinawa.