HausaTv:
2025-07-26@18:21:45 GMT

Iran A Shirye Take Ta Kare Kanta Cikin Karfi Daga Duk Wani Hari Da Za A Kawo Ma Ta

Published: 13th, February 2025 GMT

Kwamandan sojan na Iran  Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa, Iran tana da cikakken shirin na aiwatar da umaranin babban kwamandan sojin kasa, kuma akidarmu ta yaki, ta ginu ne akan kariya, amma kuma a lokaci daya za mu fuskanci duk wanda ya kawo mana hari, da karfi.

Birgediya  janar Hamid Wahidi ya bayyana hakan ne dai a lokacin bikin kaddamar da lambobin yabo da sadaukarwa ga iyalan shahidai na sojan sama, inda ya ce: “A wannan lokacin da ake ciki, Muna cikin wani yanayi mai matukar hatsari a duniya, amma a ranar sojan sama jagoran juyin juya halin musulunci ya shata mana ka’idoji masu kima da za mu yi aiki da su da, kuma za su kasance wadanda za mu yi aiki da su a kodayaushe.

Kwamandan sojan saman na Iran ya kara da cewa; A halin da ake ciki a yanzu sojan saman Iran suna da karfi sosai, sun kuma dogara ne da kansu wajen kera abubuwan da suke da bukatuwa da su.

Har ila yau Birgediya Janar Hamid Wahidi ya ce, yana alfahari da dukkanin abokan aikinsa sojojin sama masu jarunta wadanda su ka tabbatar da hakan a lokacin farmakin “Wa’adus-sadiq”. Haka nan kuma  ba za su taba ja da baya ba a karkashin kowane yanayi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid A Borno

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matashi ya tono gawar kakarsa don yin tsafin kuɗi da ƙoƙon kanta
  • ‘Yan Jarida Da Suka yi Shahada A Gaza Sun Kai 232, Yayin Da Wadanda Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Yunwa Suka Kai 122
  • An kashe mata da yara a sabon harin Filato
  • Iran Ta Jaddada Wajabcin Daukan Matakin Kawo Karshen Dakatar Da Laifukan Kisan Kare Dangi A Gaza
  • Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu
  •  An Jikkata  Sojojin Sahayoniya 9 Ta Hanyar Take Su Da Mota
  • Ayatullahi Makarem Shirazi Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Hadin kai Da Suka Bayar Lokacin Yakin Kwanaki 12
  • Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
  • Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid A Borno