NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?
Published: 10th, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizanin tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja, inda ke da mawadata da kuma matalauta.
A tsakanin al’umma kuma akwai ajin mutane masu matsakaicin samu waɗanda ake kira “Middle Class”.
Akan sanya mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kuɗin da suke samu, da matakin ilimin da suka kai, da ma matsayinsu a tsakanin al’umma.
Sai dai a baya-bayan nan irin wadannan muntane sun bi sahun matalauta wajen korafi game da yadda suke dandana kudarsu saboda tsadar rayuwa.
NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’Shin a iya cewa har yanzu akwai wannan aji na mutane a Najeriya ke nan?
Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya Tattalin Arziki
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria