Wakilin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Iraki Ya Ya Jaddada Rawar Juyin Juya Halin Musulunci
Published: 9th, February 2025 GMT
Wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iraki ya ce: Juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wani sabon samfuri na hadin kan al’umma
Ayatullah Mojtaba Hosseini, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iraki ya bayyana muhimmancin hadin kan al’ummar musulmi da kuma nauyin da ya rataya a wuyan musulmi na daidaiku da na al’umma dangane da manufofin juyin juya halin Musulunci, yana mai cewa: juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wani sabon salo na hadin kan al’ummar musulmi.
A jawabin da ya gabatar na zagayowar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran da aka gudanar a tsohon gidan da Imam Khumaini (r.a) da ya zaune a birnin Najaf, Ayatullah Husaini ya jaddada muhimmancin hadin kan al’ummar musulmi da kuma irin nauyin da ke wuyan musulmi na daidaiku da na zamantakewa da suka dace da manufofin juyin juya halin Musulunci.
Har ila yau Ayatullah Mojtaba Hosseini ya tabo batun juyin juya halin Musulunci a Iran yana mai bayyana hakan a matsayin wata mu’ujiza ta Ubangiji, sannan ya kara da cewa: Batun juyin juya halin Musulunci yana nan a kan tafarkinsa kuma Allah ya nufa ya zama wani gagarumin yunkuri na jama’a wanda ya iya haifar da gagarumin sauyi a Iran da kuma duniyar musulmi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: juyin juya halin Musulunci a
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas ga manufofinta na ketare.
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Rudun gwamnatin yahudawan sahayoniyya, wadda take ganin za ta iya gindaya wa Iran abin da ya kamata ko kuma bai kamata ba, rudun tunani ne da ya yi nesa da hakikanin gaskiya, ta yadda bai cancanci mayar da martani ba.
Araqchi ya kara da cewa: “Duk da haka, jajircewar Netanyahu wani abin lura ne, a yayin da yake kokarin neman bayyana wa Shugaba Trump abin da zai iya ko kuma ba zai iya yi a diflomasiyyarsa da Iran ba!”
Ministan harkokin wajen ya yi nuni da cewa: “Abokanan Netanyahu a cikin tawagar Biden da ta gaza – wadanda suka kitsa makarkashiyar hana cimma yarjejeniya da Iran – suna kokarin nuna zaman tattaunawar da ake yi ba na kai tsaye ba da gwamnatin Trump a matsayin wani kuskure ne kuma tamkar hoton sauran yarjejeniyar nukiliya ce da aka gudanar.”