Sin Za Ta Mai Da Martani Kan Dukkanin Cin Zalin Ciniki Da Aka Yi Mata
Published: 6th, February 2025 GMT
Kwanan baya, kasar Amurka ta sanar da kara harajin kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar, tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl. Bayan haka, nan take kasar Sin ta sanar da daukar matakan mayar da martani a kan karin harajin Amurka domin kare hakki da moriyarta yadda ya kamata.
Abubuwan da suka faru cikin shekarun baya bayan nan, sun nuna cewa, daga karshe dai, kasar Amurka ce za ta yi fama da mummunan tasirin yakin haraji da ta tayar. Bayan matakan cin zalin ciniki da ta dauka kan kasar Sin, ba gazawa wajen cimma burinta na farfado da aikin kere-kere da rage gibin kudi kadai Amurka ta yi ba, har ma da rasa damarta a muhimman kasuwannin kasa da kasa.
Matakan mayar da martani a kan karin harajin Amurka da kasar Sin ta dauka, su kasance matakai na wajibi domin dakile raayin Amurka da fifiko da hana yaduwar kariyar ciniki, ta yadda za ta kiyaye hakkinta na neman ci gaba yadda ya kamata, tare da kare tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, da kuma kaidar adalci ta kasashen duniya. Babu wanda zai ci nasara cikin yakin ciniki da yakin harajin kwastam. (Mai Fassara: Maryam Yang)
কীওয়ার্ড: kasar Sin ta
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun.
Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin Huangyan Dao.
Lin ya ce “Mun gabatar da kakkarfan korafi a yau, dangane da kuskuren da Amurka ta tafka. Tsibirin Huangyan Dao yankin kasar Sin ne tun fil azal”, kuma kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin na karkashin ikon mulkin kai na Sin, wanda hakan ke nufin yana bisa turba, ya dace da doka, bai kuma cancanci suka ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp