Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansa a Adamawa
Published: 31st, January 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana kan zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake masa tambayoyi.
Garba wanda ɗan asalin garin Tappare Kona Uku ne a ƙaramar hukumar Jada ta jihar, ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan rasuwarsa.
Shekara guda bayan binne shi, ɗan ya dawo ya nemi kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafin al’adun gargajiya.
Garba ya yi iƙirarin cewa ɗan mijin mahaifiyarsa ne ya matsa masa lamba, wanda ya yi imanin matsafi ne kuma zai iya cutar da shi ko kuma ‘ya’yansa idan ya ƙi bin umarninsa.
Ya ce, “Na ɗauki fartanya da misalin ƙarfe 4:00 na asubahi, na je maƙabarta, na tona kabari, na yanke kan sa.
Sai ya dawo gida ya ba wa yaron kan a cikin jakar leda.
Wanda ake zargin ya ci gaba da bayanin cewa bayan mako biyu, matar marigayin ta zo wurinsa inda ta shaida masa cewa ta yi munanan mafarki tun lokacin da aka ajiye kan a ɗakin kwanansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Adamawa kabari mijin mahaifiyarsa
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina
Wasu mazauna Jihar Katsina sun yi zaman sulhu da wasu shugabannin ’yan daban daji da suka addabe su.
Wakilinmu ya ruwaito cewa an yi taron sasanci da ’yan bindigar daji ne a Ƙaramar Hukumar Danmusa, wanda rundunar sojoji ke shiryawa, inda Adamu Aliero ya jagoranci sashen ’yan bindigar.
BBC ya ruwaito Kwamishinan Tsaro da Harkokin Ciki Gida na Katsina na cewa al’ummar garin Bicci da ke yankin Ƙaramar Hukumar Danmusa sun zauna tare da Ado Aliero da sauran wasu shugabannin ’yan bindigar aƙalla goma.
“An zauna da Ado Aliero da Kamilu Buzaru da Dogo Nahali da Wada Jargaba da Dahiru Buzu haka ma da Nagoggo,” in ji shi.