An Tsamo Gawakin Mutane 30 A Karon Da Wani Jirgin Fasinja Ya Yi Da Wani Jirgi Mai Saukar Ungulu A Birnin Washinton
Published: 30th, January 2025 GMT
Kamfanin dillancin labaran BBC ya bayyana cewa mutane 64 ne suke cikin jirgin fasinja na kamfanin American Airline, sannan mutane 3 ne a cikin jirgin yaki mai saukar ungulu samfurin Black Hawk suka yi karo a birnin washinton a safiyar yau Alhamis.
Labarin ya kara da cewa, a halin yanzu sun tashi daga kubutar da wadanda suke da rai zuwa neman gawaki kawai, tunda ana ganin da wuya a sami wani da rai a cikin fasinjojin jirgin.
Jami’an gwamnatin kasar Amurka sun bayyana cewa jirgin fasinjar ya rabu zuwa kasha ukku sannan ya fada cikin wani ruwa mai zurfin mita 7.
Shugaba Trump dai ya bayyana cewa, hatsarin wanda za’a iya kauce wa ne, idan da kowa yayi aikin da ya dace. Don haka kuskuren dan’adama ne.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha Ta Kai Munanan Hare-hare Akan Birnin Kiev Na Ukiraniya
Wani jami’in kasar Ukiraniya ya bayyana cewa, a kalla mutane 8 ne su ka jikkata sanadiyyar munanan hare-haren da Rasha ta kai wa birnin Kiev ta hanyar amfani da makamai masu linzami.
Shugaban sha’anin tafiyar da Mulki na soja a birnin Kiev Taimur Tikatishinko ya wallafa sanarwa a shafinsa na “Telegram’ cewa; A tsakanin wadanda su ka jikkata din da akwai karamin yaro dan shekaru 3, kuma tuni an dauki mutane 4 zuwa asibiti, daya daga cikinsu yana cikin mummunan hali.
Shi kuwa magajin birnin na Kiev Fitali Kikitshiko cewa ya yi, mutanen da su ka jikkata suna zaune ne a cikin gidaje mabanbanta a unguwa daya.
Har ila yau ya kara da cea; Harin ya haddasa fashewa mai karfi wacce ta sa tagogin gidaje su ka fashe, har zuwa gine-gine masu hawa 11.
A wani labarin daga jami’an kasar ta Ukiraniya, Rasha ta kai wasu hare-haren da jirage marasa matuki a garin Kirofifitsky wanda ya haddasa fashewa mai yawa.
A cikin makwannin bayan nan dai Rasha ta tsananta kai hare-hare a fadin kasar Ukiraniya ta hanyar amfani da makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuki.
Tun a 2022 ne dai Rasha ta fara kai wa Ukiraniya hare-hare bisa dalilin cewa tana son shiga cikin kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato.
Kasar ta Ukiraniya dai tana samun taimakon makamai da bayanai na sirri daga kungiyar ta Nato.