NAJERIYA A YAU: Dabarun Noma Don Samun Kuɗaɗen Shiga
Published: 28th, January 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Akan ce ‘Noma tushen arziƙi’ kuma mutane da dama za su iya bayar da labarin da ke tabbatar da hakan; domin kuwa ko ba komai idan mutum ya samu abinci ya ci ya ƙoshi babban arziƙi ne.
Wasu ’yan Najeriya kan shuka kayan abinci a unguwanninsu don sama wa kansu abincin da za su ci.
Sai dai masana na ganin da waɗannan mutane za su inganta wannan noma da sun sama wa kansu kuɗaɗen shiga. NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan hanyoyin da ’yan Najeriya za su iya bi don sama wa kansu kuɗaɗen shiga bayan sun noma abin da za su ci.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi
Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a Ƙaramar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi a wani mataki don bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa.
Hakan na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami’an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin Jihar Kebbi.
Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta ’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwaSojojin sun kai ziayarar ne ƙarƙashin jagorancin Rear Admiral Patrick Nwatu – wanda ya wakilci babban hafsan sojin ruwan ƙasar.
Rundunar ta ziyarci Kebbi ne domin duba yadda za ta samar da sansaninta a jihar.
Patrick Nwatu ya yi tir da harin ta’addanci a kogin Neja, yana mai cewa yankin ya zama maɓoyar masu safarar makamai da sauran masu aikata laifuka.
Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce ta kammala shirye-shiryen kafa sansanin sojin ruwa a garin Yauri da ke jihar.
Babban Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla ne ya bayyana hakan a wata ziyarar ban girma da suka kaiwa Gwamnan Kebbi, Nasir Idris a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi a ranar Alhamis.
Da yake jawabi yayin ziyarar, jagoran tawagar Rear Admiral Patrick Nwatu, ya ce ziyarar wani ɓangare ne na faɗaɗa dabarun teku na sojojin ruwan Najeriya.