2025-09-17@22:14:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5277
«Mariya Sanusi»:
Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi. Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo...
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki. A ranar 4 ga Satumba, 2025,...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne...
Dan kasar Iran Aryan Salawati ya sami kyautar tagulla a wurin gasar kirkire-kirkire ta kasa da kasa wacce aka yi a kasar China. A yayin wannan bikin dai masu kirkira daga kasashe masu yawa ne su ka gabatar da abubuwan da su ka kirkira. Matashin dan kasar Iran ya kirkiri karamar na’ura wacce take iya...
Shugabgan kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gana da fira ministan kasar Iraqi Muahmad Shi’a Sudani a taron Doha na kasashen musulmi ya bayyana cewa; Wajibi ne kasashen musulmi su hada kai idan har suna son kawo karshen laifukan da HKI take tafkawa. Bugu da kari, shugaban kasar ta Iran ya kuma tattaunwa wasu hanyoyin...
Ya ƙara da cewa ‘yan’uwa da abokan arziƙi da suka shirya wannan biki na karrama Farfesa Armaya’u Bichi tare da bashi lambar yabo tare da wasu muhimman mutane waɗanda suka taimaimake shi wajen gudanar da shugabanci sun kyauta sannan sun ajiye ƙwarya a gurbinta. Shima da yake gabatar da jawabinsa, shugaban riƙo na jami’ar...
Fitacciyar mai girkin nan, Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta sake kafa tarihi a duniya ta hanyar girka tukunyar dafa-dukar shinkafa mafi girma bayan shafe awa takwas tana girkin. Hakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon taya murna da Kundin Bajinta na Guinness ya wallafa a shafukan sada zumunta....
Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa. Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne...
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta shiga tsakani don sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO). Rikicin ya samo asali ne daga katse wutar lantarki da asibitin ya zargi KEDCO da yi, inda ya ce hakan ya kawo cikas ga ayyukan...
Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa. Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne...
Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East. A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah,...
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) ya ƙaryata zargin da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya yi masa, dangane da mutuwar wasu marasa lafiya sakamakon katse wutar lantarki da aka ce kamfanin ya yi. Asibitin na AKTH ya bayyana damuwarsa a ranar Lahadi kan abin da ya kira abin takaici yana mai...
Gwamnan Jihar Neja, Umar Mohammed Bago, ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin Najeriya bayan da ya sake jaddada cewa duk wani malamin addini da ke shirin yin wa’azi dole ne ya gabatar da rubutaccen wa’azinsa domin tantancewa kafin ya gabatar da shi ga jama’a. A cewar gwamnatin jihar, wannan mataki na da nufin daƙile kalaman ƙiyayya,...
Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce fiye da sojojin kasar 20,000 ne suka ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon damuwa. A cewar sashen bayar da shawarwari na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya koka bisa yawan bashin da Najeriya ke ciyowa da kuma yadda gwamnati ke facaka da kuɗaɗen. Sarkin wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya kuma bayyana cewa cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi shi ne mafi alheri, yana mai cewa da Gwamnatin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya. Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11. Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar...
Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura. Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda...
Sarakunan suna bada haɗin kai wajen tafiyar da harkokin gwamnatin ƙasarsu, suna kuma jin basu tare da wata matsala ba tare da matsayinsu. Yawancin Sarakuna da kuma wasu manyan msu Sarautar gargajiya bugu da ƙari suna cikin majlisar dattawa a lokacin. Duk kuma wani lokaci da Sarakunan gargajiya suka fahimci suna fuskantar barazana dangane da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙwallon ɗaya tilo da kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars Ahmed Musa ya ciwa ƙungiyar tayi sanadiyar samun nasarar farko da ƙungiyar tayi tun bayan fara wannan kakar wasannin ta bana. Pillars ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 1-0 a wasan da suka buga a filin wasa na Sani Abacha dake...
Tun daga ranar 18 ga wata, za a kaddamar da fim mai taken 731 a sassan duniya da dama, fim din da ya bayyana yadda rundunar sojojin kasar Japan da suka kutsa kasar Sin suka gudanar da nazari a kan hada makamai da cututtuka tare da gudanar da gwaje-gwaje a jikin al’ummar kasar Sin, a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima na kasa da kasa wato CIFTIS a takaice na shekarar 2025 da aka rufe a yau Lahadi, ya ja hankalin masu saka jari daga tarin kasashen waje. Manyan jami’an kamfanoni na kasashen waje sun bayyana cewa, suna daukar bikin a matsayin wata babban dandamali na more damammaki tare...
Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Samun Lambar Tantance Haraji (Tax ID) zai zama wajibi ga duk ƴan Nijeriya da ke hulda da bankuna da sauran ayyukan hada-hadar kudi daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon umarni yana cikin Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, 2025, wacce shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kwanan...
A yau Lahadi ne aka kammala baje kolin kasa da kasa na hada-hadar cinikayyar hidimomi na kasar Sin na shekarar 2025, ko CIFTIS a takaice a nan birnin Beijing. A cewar mashirya bikin, baje kolin ya cimma manyan nasarori sama da 900 a fannonin gine-gine, da fasahar sadarwa, da hada-hadar kudade da sauransu. CIFTIS na...
A cewar sanarwar, bisa wannan sanarwar, fadar ta shugaban ƙasa, ta yanke duk wata huɗɗa da Umunubo. Sanawar ta kuma jaadda cewa, ya zama wajbi ɗaukacin masana’antun da ke a ƙasar nan, su nesanta kansu, da yin dukka wata huɗɗa da Umunubo da sunanan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu. Idan za a iya tunawa, Jaridar...
An gano gawar Haneefa, yarinya ’yar shekara uku da ruwa ya tafi da ita lokacin da yayarta Fatima, ke goye da ita yayin ambaliyar da ta rutsa da su a Tudun Jukun da ke Zariya, a Jihar Kaduna. An tsinci gawar ne bayan kwanaki shida da aka kwashe ana nemanta, a gangaren ƙasan Kilaco, unguwar...
Sama da kashi casa’in (90%) na kabilu da mabiya addinai da ke raye cikin Nijeriyar yau, ba su damu da samar da shugabanci nagari cikin Kasar ba a aikace, sai dai kawai a mafarkance. Za a iya gane hakan ne ta hanyar nazartar aiyukansu hada da furuce-furucensu!!!. Da daman mutane ba sa zaɓar wani kansila...
“Shawarar tsarin shugabancin duniya” ta zama kalmar da aka sha karanta a rahotannin kafofin watsa labaru na duniya cikin kwanakin baya. Shugabannin wasu kasashe da dama suna ganin cewa, wannan shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron koli na SCO da aka gudanar a kwanan baya a birnin Tianjin, tana...
Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila. Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da...
An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar...
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta raba wa mutum 2,261 da ambaliyar ruwa ta shafa a Potiskum, Nangere da Jakusko a Jihar Yobe, kayan agaji. An raba kayan ne a unguwanni 21 na Potiskum, ƙauyukan Kolo da Ajim a Nangere, da kuma kauyukan Dachia, Yim, Saminaka, Garin Maji da Amshi a Jakusko. Gwamnati...
An karrama fitattun fina-finai daban daban a bikin “Golden Panda” da ya gudana jiya Asabar a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kasar Sin. A bana, an gudanar da bikin ne a karo na biyu, wanda kuma gungun sassan bunkasa harkokin adabi da al’adu da gwamnatin lardin Sichuan suka dauki nauyin shirya shi. Bikin na...
A cikin sanarwarsa, Daso ya ce: “Rundunar Ƴansanda ta Jihar Borno na sanar da jama’a cewa an gano gawar wani mutum da ba a tantance ba a kusa da na’urar sauya wuta (transformer) a Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri. “Binciken farko ya nuna cewa marigayin ya mutu ne sakamakon jan wutar lantarki yayin da yake ƙoƙarin...
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi cewa jihohi 11 na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda ka iya haddasa ambaliya daga ranar Lahadi zuwa Alhamis. A cikin sanarwar da Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa, ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli, ta fitar, jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Benuwe, Nasarawa, Taraba da Delta. An yi...
Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga a Tashar ta Apapa. “Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba 001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma...
An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar...
Masu lura ko sa ido kan harkokin ilimi sun ce biyan kuɗaɗen cikin lokaci za su taimaka matuƙa wajen samun matsin da takurar da ƴan makaranta ko Iyayensu ke fuskant, bugu da ƙari kuma za su kasance a wuraren da suke karatu domin maida hankali kan abinda ya sa suke a makarantar ko kwalejin Hukumar...
Cikakkun bayanai kan halartar Iran zuwa taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya na kasar Iran Muhammad Islami ya yi karin haske kan yadda Iran za ta halarci taron shekara -shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA. Mohammad Eslami ya bayyana dangane da...
Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Nakwango, ɗaya ne daga cikin jiga-jigan da aka kafa masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood da su. A cikin wannan tattaunawar, ya bayyana cewa bai taɓa yin da-na-sanin shigarsa sana’ar ba, sannan ya bayyana dalilin da yanzu ba a cika ganin sa sosai a fina-finai ba, da...
Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin...
Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara bayan kwanaki biyu kacal. Sai dai ƙungiyar ta sake bai wa Gwamnati Tarayya mako biyu ta biya buƙatunta ko ta sake tsunduma yajin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara ne ya bayyana haka a ranar Asabar tare da umartar...
ADC ta ce, “APC tana tsoron ƙaruwar shaharar ADC a faɗin ƙasar nan ne, kuma yana bayyana cewa shi ne kawai hanyar da za su iya bi wajen tarwatsa ƴan adawa a ƙasar nan. “An fara ne a Jihar Edo da gargaɗin shugabannin ADC kan ka da su ziyarci jihar, sannan Kogi ta biyo baya,...
Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da...
Wani mutum mai shekara 67 aka kai asibiti da raunuka masu barazana ga rayuwa, abin takaici kuma ya rasu a asibiti a ranar Juma’a, 5 ga Satumba. An bayyana sunansa da James Gbadamosi.” Bayan faruwar lamarin, ƴan sanda sun bayyana cewa sun kama Wright-Walter mai shekaru 37, suka gurfanar da shi bisa laifin kai hari...
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni waɗanda ba su da nagarta. Ya bayyana haka ne a bikin “Kano International Poetry Festival” da aka yi a Kano a ranar Asabar. Gini mai hawa 3 ya rufta kan mutane a Legas HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani...
A yau Asabar aka kaddamar da tashar watsa labarai ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ta Sichuan, tare da kaddamar da wasu jerin ayyuka na CMG din a Chengdu babban birnin lardin Sichuan. Daraktan CMG Shen Haixiong ya halarci taron, inda a ciki jawabinsa ya ce kafar CMG za ta...
Yau Asabar, an gudanar da taron dandalin tattauna al’adu na kasa da kasa na Golden Panda na 2025 a birnin Chengdu. Li Shulei, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS, ya halarta tare da sanar da bude taron. Mahalarta na kasar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa alakar iran da Tunusiya wani babban misali ne na irin yadda kasar iran ke son su fadada dangantaka da sauran kasashen musulmi bisa girmamawa da mutunta juna. Haka zalika Araqchi ya jinjinawa kasar Tunusiya game da irin matakin da ta dauka musamman a lokacin harin...
Rahotanni sun bayyana cewa babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince daftarin kudirin dake nuna goyon bayan kafa kasar falasdimu mai cin gashin kanta, inda ka samu kasashe 142 suka kara kuri’ara amincewa yayin da kasashe 10 kuma sun nuna rashin amincewa sai kuma guda 12 da suka kauracewa kada kuria. Wannan daftarin kudurin ya...