2025-11-15@10:46:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1375

«azumin Ramadan»:

    An sanya ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a fara shari’arsa kan zargin karkatar da biliyoyin kuɗi da EFCC ta gabatar. Obiano ya yi gwamna a Jihar Anambra daga 2014 zuwa 2022. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano November 14, 2025 Manyan Labarai Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci November 14, 2025
    Bayan hukunci, kwamitin gudanarwa karkashin shugabancin Damagum ta dakatar da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu da mashawarcin shari’a na kasa, Kamaldeen Ajibade da sakataren shirye-shirye na kasa, Umar Bature na tsawon wata guda saboda zargin ayyukan da ke goyon bayan abin da ya saba wa jam’iyya. Bayan awanni 24, Anyanwu da magoya bayansa sun hadu a Abuja suka sanar da dakatar da Damagum da dukkan mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar. Sun kuma bayyana sunan mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Arewa ta tsakiya, Abdulrahman Mohammed, a matsayin sabon mukaddashin shugaban jam’iyya kasa. Yayin da bangarorin biyu suke kalubalantar junansu, bangaren da Damagum ke jagoranta ya samu umurnin alkalin babban kotun Jihar Oyo, Ladiran Akintola, wanda ya umartar PDP da...
    Shugaban Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya soki Shugaban Amurka Donald Trump saboda kin halartar taron shugabannin G20 da ke tafe, yana mai gargadin cewa yunkurin ware kasar da ke karbar bakuncin taron ba zai yi wani tasiri ba ga taron ko sakamakonsa. Trump ya sanar da cewa shi ko wani jami’in Amurka ba za su je Johannesburg don taron na 22-23 ga Nuwamba ba, yana mai jayayya cewa bai kamata Afirka Ta Kudu ta dauki nauyin taron ba kwata-kwata. Ya ba da hujjar kauracewa taron ta hanyar maimaita zarge-zargen da aka musanta cewa fararen fata ‘yan Afirka Ta Kudu na fuskantar zalunci mai tsanani. A cikin wani rubutu da ya yi a yanar gizo, Trump ya bayyana shi a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk shekara bayan girbin damina, ana sa ran manoma su ci gaba da noma a lokacin rani domin tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arziki. Sai dai hakan na fuskantar kalubale da dama da ke hana yawancin manoma shiga noman rani.   Kamar yadda masana suka sha bayyanawa, akwai dalilai da dama dake hana manoma shiga noman rani a duk lokacin da aka ce damina ta tattara inata intat. Shin ko wadanne kalubale ne ke hana manoma shiga noman rani bayan damuna ta wuce? NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar...
    Rahotanni sun bayanna cewa kakakin fadar kremlin Dimitry peskov yayi gargadi game da barazanar baya yana nan da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubios yayi da cewa akwai yiyuwa Amurka ta koma gwajin makaman nukiliya. Ci gaba da gwajin nukiliya ga Amurka zai kara fadada zaman dardar a duniya, kuma zai kawo cikasa ga kokarin shawo kan yaduwar makamai na tsawon shekaru da ake yi, sannan ya sake farfado da fargabar sake shiga sabuwa gasar makamai a dangantakar Amurka da rasha da ta riga ta tabarbare Idan ana iya tunawa a ranar 29 ga watan oktoba ne shugaban Amurka Donald trump ya umarci maaikatar tsaron  Amuka da ta ci gaba da gwajin nukiliya  wanda yake nuna yiyuwar samun sauyi...
    Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta fitar da wani rahoto da shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya fitar da a ciki yake tabbatar da cewa, Iran tana aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Rahoton dai ya kunshi cewa, tun bayan yarjejeniyar birnin Alkahira na kasar Masar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran da kuma shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa Refael Grossy, Iran din ta yi aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Grossi ya rubutawa Iran wasika a ranar 7 ga watan Nuwamba na 2025 yana mai cewa; Bayar da dama ga hukumar domin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a cikin Iran, yana...
    Ministocin harkokin wajen Iran da na Rasha sun tattauna ta  wayar tarho gabanin taron kwamitin gwamnonin IAEA A yayin tattaunawar Araghchi da Lavrov, sun yi musayar ra’ayi kan batutuwa daban-daban, ciki har da rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan, tare da jaddada muhimmancin yin shawarwari don warware batutuwan da ba su dace ba. Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya kuma jaddada bukatar tuntubar juna tsakanin Iran da Rasha da ma sauran kasashen duniya domin lalubo hanyoyin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A yayin da yake ishara da matakin da Amurka da kawayenta na Turai suka dauka a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dangane da Falasdinu, da wani daftarin kuduri na kafa rundunar kasa da kasa...
    A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar.   Kazalika a yanzu gwamnatin na saudiyya ta bayyana cewa idan har maniyyatan Najeriya basu biya cikakken kudaden hajjin bana ba, to akwai alamun sake rage yawan kujerun zuwa dubu hamsin. NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma Ko yaya...
    Daga Bashir Meyere Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na neman rancen Naira Tiriliyan 1.15 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2025. Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da lamuran bashi na cikin gida da na waje. Yayin da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, wanda mataimakinsa Sanata Haruna Manu ya wakilta, ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 59.99 da Majalisar ta amince da shi, ya karu da Naira tiriliyan 5.25 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 54.74 da gwamnatin tarayya ta fara gabatarwa. Ya ce an riga an amince da Naira tiriliyan 12.95 a cikin kasafin, wanda hakan ya...
      An umarci shugaban karamar hukumar da ya mika harkokin majalisar ga mataimakiyarsa, Mrs Victoria Okolo, har sai an kammala binciken.   Majalisar ta bai wa kwamitin binciken wata daya don kammala aikinsa tare da bayar da rahoto kan matakin da ya dace. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Bisa Zargin Rashin Ɗa’a November 12, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka November 12, 2025 Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025
    An umarci shugaban karamar hukumar da ya mika harkokin majalisar ga mataimakiyarsa, Mrs Victoria Okolo, har sai an kammala binciken.   Majalisar ta bai wa kwamitin binciken wata daya don kammala aikinsa tare da bayar da rahoto kan matakin da ya dace. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka November 12, 2025 Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025 Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da twakaransa na kasar Rasha Sergei lavrov inda suka mayar da hankalin kan batutuwan da suka shafi yankin dama na kasa da kasa  Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta bayyana cewa Iraqchi ya jaddada game da muhimmancin zaman lafiya a yammcin Asiya lokacin da yake ishara game da rikicin baya bayan nan  da ya faru tsakanin Pakistan da Afghanistan, Da ya koma bangaren batun falasdinu kuma Araqchi ya soki matakin da Amurka da kasashen turai suka dauka a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya na gabatar da daftarin kuduri na neman a tilasta tura dakarun kasa da kasa zuwa yankin gaza na falasdinu, yace wannan kuduri yayi hannun...
    Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), ta ayyana Najeriya ɗaya daga cikin jerin ƙasashen da za su fuskanci matsananciyar yunwa. Ta kuma yi gargaɗin cewa ƙarin mutane a duniya na iya fuskantar yunwa saboda ƙarancin kuɗin tallafi. Rahoton da Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da WFP suka fitar, ya nuna cewa rikice-rikice da tashin hankali ne ke jawo matsananciyar yunwa a ƙasashen da ke cikin hatsari. DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotu Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP Rahoton ya bayyana ƙasashen Haiti, Mali, Falasdinu, Sudan ta Kudu, Sudan da Yemen a matsayin waɗanda ke cikin mafi munin...
    Hukumar Kula da jin dadin mahajjan Jihar Taraba ta bayyana 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe ga masu niyyar yin hajji don kammala biyan kuɗin tafiyar hajji ta shekarar 2026. A cewar wata sanarwa da Sashen Bayani na Hukumar ya fitar ta bakin Mataimakin Daraktan Hamza Baba Muri, an ƙayyade sabon kuɗin hajjin 2026 a Naira miliyan 7,630,000, kamar yadda Hukumar Hajj ta Kasa (NAHCON) ta amince. Hukumar ta yi kira ga duk masu shirin yin hajji ta wannan tsari su tabbata sun biya kuɗin gaba ɗaya kafin ƙarshen wa’adin domin samun tabbacin shiga cikin masu sauke farali shekara mai zuwa. Mai magana da yawun Hukumar ya jaddada cewa dukkan biyan kuɗi dole ne a yi su ta...
    Gidauniyar Tallafawa Al’umma ta Abba Aliyu Gandu da ke jihar Kano ta bada horo sana’o’in hannu tare da raba tallafin Solar ga al’umma 500. Wannan shi ne karo ba adadi da wannan gidauniyar ta Kogunan Kasar Hausa kuma shugaban hukumar Samarda Lantarki a yankunan Karkara Alhaji Abba Aliyu ta gudanar. An raba kayan Solar guda 500 da kuma kudin fara sana’o’in hannu ga wadanda suka sami horo a karkashin wannan gidauniya. Mataimakin Shugaban wannan gidauniya Suleiman Aliyu Abubakar ya bayyana cewa sama da shekara suna rana kyayyakin sun hada da solar domin kawo karshen matsalar wutar lantarki. Suleiman Aliyu Abubakar wanda ya wakilci MD Abba Aliyu a wajen taron yace Kayayyakin sun hada da fanka da kayan caji da na...
    DSP Aliyu ya gargaɗi jama’a da su guji yaɗa labaran ƙarya, inda ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin aikata hakan za a hukunta shi. Ya kuma roƙi mutane su dogara da sahihan bayanai daga hukumomi, tare da tabbatar da cewa rundunar ‘yansandan ƙarƙashin CP Bello Shehu tana ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL November 9, 2025 Wasanni Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya November 9, 2025 Wasanni Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko November 8, 2025
    A wajen taron, tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, ya zama gargaɗi ga shugabanni su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro. Obasanjo ya ce, “Ku ne shugabannin yau, domin idan kuka bar gobe a hannun shugabannin yau, za su lalata komai, kuma ba za ku samu gobe mai kyau ba. Ku duba ƙasar Kamaru, shugabanta Paul Biya yana da shekara 92, to me za a ce game da matasan ƙasar?” Tsohon shugaban ya jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su tashi tsaye su jagoranci nahiyar Afrika domin makomarsu ta dogara da abin da suka yi a...
      ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo November 10, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Taya Ouattara Murnar Sake Lashe Zaben Shugaban Cote D’Ivoire November 10, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Halarci Bikin Bude Gasar Wasanni Ta Sin Karo Na 15 A Guangzhou November 10, 2025
    Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da yadda aikin hajjin bana zai kasance dangane da abin da ya shafi kudin kujerar aikin da lokacin da za a rufe karbar kudin maniyyata. Wannan dai ya biyo bayan kulla yarjejeniyar gudanar da aikin Hajji ta 2026 da hukumar ta yi a madadin Najeriya da hukumomin kasar Saudiyya, a lokacin wani biki da aka gudanar a birnin Jeddah na Saudiyya. Shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin ministan Hajji na Saudiyya Abdulfatah Mashat ya wakilci Saudiyyar. Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da rage kudin kujerar aikin hajji ne, bisa umarnin shugaban ƙasa. Share 0 0 votes...
    Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baghaei yayi tir da Amurka game da rashin kyakkawar nufi ko muhimmantar da tattunawa da ake Magana akai, yace sanarwar da shugaban Amurka trump ya fitar a baya bayan nan na amicewa da hannu Amurka wajen kai mata hari ya nuna cewa ta ma shiga cikin harin soji da aka kai mata. Kakakin yayi suka mai tsananin ga kamalan da shugaban Amurka  yayi dake tabbatar da hujjoji dake nuna cewa yana da hannun dumu dumu wajen kai mata harin soji,  wannan yana daya daga cinkin bayyanannun hujoji  dake tabbata da taka rawar Amurka wajen kai mata hari. Haka zalika ya nuna cewa iran ta mikawa kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya wadannan kalaman...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyyar masa’antu ta shirin nukiliya na zaman lafiya. Ministan ta fadi hakan ne a wata ziyara da ya kai hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar,  inda ya bayyana irin namijin kokarin da suke yi wajen kara inganta nukiliyar masana’antu, kuma yace kasarsa ba za ta taba yin watsi da shirin ta na nukiliya domin ayyukan zaman lafiya ba. Haka zalika ya jinjinawa iran game da irin gagarumin ci gaban da suka samu a fasahar nukiliya, inda suka shiga bangare masana’antu da ya yadu zuwa wasu bangarori daban daban. Hukumar kula da makamashin nukiliya...
    Hukumar kula da jin daɗin alhazai ta birnin tarayya (FCT) ta saka ranar 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe da za a biya kuɗin Hajji na shekarar 2026, wanda aka tsara a N7,696,769.76. Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin hukumar a yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, inda jami’in hulɗa da jama’a, Muhammad Lawal Aliyu, ya buƙaci duk masu niyyar zuwa Hajji daga Abuja su bi ƙa’idojin da aka shimfida. An bayyana cewa tabbataccen kuɗin Hajjin ya samu ne bisa ƙayyadadden tsari daga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), sannan duk biyan kuɗin za a yi ne ta hanyar Banki, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, ba tare da karɓar kuɗi a hannu...
    Pars Today – Jakadan Iran a Rasha ya sanar da cewa Tehran da Moscow sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Kazem Jalali, jakadan Iran a Rasha, ya rubuta a ranar Lahadi a dandalin sada zumunta na X cewa an cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Rasha don kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Ya kara da cewa wannan yarjejeniya ta samo asali ne daga tarurrukan da aka gudanar a ranakun 6-7 ga Nuwamba a Makhachkala tsakanin shugabannin tashoshin jiragen ruwa da na ruwa, manyan jami’an gwamnati, da daraktocin manyan kamfanonin kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen biyu. A cewar Pars Today, ya kara da cewa a lokacin wannan taron, an amince da tsarin da tsarin hadin...
    Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun yi tattaunawa ta wayar tarho game da batun halin da ake ciki a yankin, inda suka mayar da hankali kan batun  tsagaita wuta a Gaza da kuma yakin da ake yi a Sudan. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar a ranar Asabar, Abdelatty ya yi nazari kan ci gaba da kokarin da Masar ke yi na karfafa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden da yarjejeniyar ta kunsa. Ya jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da wannan yarjejeniya zuwa mataki na biyu na shirin tsagaita wuta, wanda zai  magance matsalolin siyasa da ayyukan  jin kai domin samun...
    A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, gami da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin. Kwanan nan ne CMG wato babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ya wallafa jerin wasu rahotannin talabijin guda biyar dangane da batun dawowar Taiwan kasar Sin. ’Yan jarida ma’aikatan CMG ne suka dauki rahotanni da bidiyo a yankin Taiwan, inda suka yi amfani da kwararan shaidun tarihi, don mayar da martani ga wasu kalaman karya da ke cewa wai “matsayin Taiwan ba shi da tabbas”, tare kuma da bankado markarkashiyar mahukuntan jam’iyyar DPP...
    Xi ya jaddada cewa, domin lardin Guangdong ya samar da sabbin damammaki da cimma sabbin nasarori, ya zama dole a ci gaba da himma wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa, da aiki da ruhin yankunan tattalin arziki na musamman, da kuma karfafa samun ci gaba mai inganci ta hanyar zurfafa gyare-gyare da bude kofa. Ya yi kira da a yi kokarin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Guangdong, Hong Kong da Macao, da kuma tallafa wa inganta hadewar Hong Kong da Macao da kuma hidimta wa ci gaban kasar baki daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE November 8, 2025 Daga Birnin Sin Cinikin...
      Sunana Abdulhamid Ado (Danbayaro): Inna lillahi wa inna ilaihirraju’un. Na ji ba dadi na ji komai sai da ya tsaya min har tsahon lokaci, abun ba zai musaltuba, sai dai kawai mu ce Allah ya ji kan Mal. Nata’ala. Mutum ne mai barkwanci, ga zumunci na gaske, ba a yin gulma da shi, baya boye wa mutum gaskiya, kuma baya cin hakkin mutum, kuma abun hannusa baya rufe masa ido. Kuma indai ya samu abun duniya ko baka sani ba sai ya kira ka an ci da kai, harkar sa ba bakin ciki yana da hali mai kyan gaske. Wata rigar san yi da ya kawo mana ‘location’ ya raba mana dukkan ‘crew’ sai da ya bamu, ina ganin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10 November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
    Ministan harkokin wajen kasar Ukraine ne ya bayyana cewa da akwai ‘yan asalin kasashen Afirka 1,400 da suke cikin rundunonin Rasha suna tayata yaki. Ministan harkokin wajen kasar ta Ukraine, Adriy Sabiha ya ce; Moscow tana jan hankalin ‘yan Afirka akan su rattaba hannu akan wata yarjejniyar aiki, wacce take daidai da yankewa kansu hukuncin kisa. Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar na Ukraine, ya rubuta a shafinsa na X cewa; ‘yan kasashen wajen da ake dauka a cikin sojojin Rasha, ana aike su zuwa inda za a yi saurin kashe su.” Jami’an gwamnatin kasar ta Ukraine sun sha yin kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su hana ‘yan kasarsu yi wa Rasha aikin soja da hakan yake da...
    A yau Asabar ne jirgin  kasa na dakon kaya na farko daga Rasha ya iso tashar jiragen ruwa ta “Abrin” na Iran. Zuwan jigin kasan dai yana a karkashin bunkasa alakar kasuwanci ne a tsakanin Iran da Rasha.  Jirgin kasan yana dauke ne da hajar kasuwanci saboda kasuwannin Iran da kuma Iraki, yana kuma dauke da kwantena 62 masu girman kafa 40.  Shi dai wannan jirgin kasan ya taso ne daga wani yanki mai nisan kilo mita  900 daga Arewacin birnin Moscow, ya kuma ratsa ta kasashen Kazakhstan da Turkmenistan, sannan ya shigo Iran. Kwanaki 12 jirgin ya dauka akan hanya kafin a karshe ya yada zango a cikin Iran. Gabanin tashin jirgin, sai an cimma yarjeniya da kasashen da...
    Tarayyar Afirka ta yi kira da a girmama ‘yancin kai na tarayyar  Najeriya kuma ta yi watsi da barazanar Trump Kwamitin Tarayyar Afirka ya bayyana damuwarsa game da kalaman da Amurka ta yi kwanan nan game da zargin gwamnatin Najeriya da hannu a kisan Kiristoci da kuma nuna alamun yiwuwar shiga tsakani na soja a karkashin hujjar “kare ‘yancin addini.” A cikin wata sanarwa a hukumance, wacce Al Jazeera ta samu kwafinta, Kwamitin ya jaddada jajircewarsa ga ka’idojin ‘yancin kai, rashin tsoma baki, ‘yancin addini, da kuma bin doka, kamar yadda aka tsara a cikin Dokar Tsarin Mulki ta Tarayyar Afirka da sauran kayan aikin da suka shafi hakan. Sanarwar ta tabbatar da cewa: Tarayyar Najeriya kasa ce mai muhimmanci...
    An rantsar da Paul Biya mai shekaru 93 a matsayin shugaban kasar Kamaru karo na takwas a majalisar dokokin kasar da ke Yaoundé. Ya shafe shekaru 43 yana mulki, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai. Biya wanda shine shugaban kasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na kuri’un zabe, yayin da abokin hammayarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar kasa. Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaben, yana zargin cewa an yi maguɗi,wanda hukumomi suka musanta. Lamarin dai ya janyo zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi. Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi alkawarin dawo da doka a kasar...
    Kasahen Iran, Rasha da kuma China sun gana a tsakaninsu a jajibirin taron Kwamitin Gwamnonin Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA),  Zaman ya hada jakadun kasashen uku a birini Vienna ranar Laraba don daidaita matsayinsu kan manyan batutuwan da suka shafi zaman na gwamnonin IAEA da ke tafe. Michael Ulyanov, jakadan Rasha kuma wakilin dindindin a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa kasashen uku sun yi “wani zagaye na shawarwari ” game da batun nukiliyar Iran. Ya kara da cewa wakilan sun daidaita matsayinsu don su shirya sosai don taron Kwamitin Gwamnonin da ke tafe. A cewar shirin da aka sanar, za a gudanar da zaman kwamitin na gaba daga ranar...
    Osimhen, wanda ya koma Galatasaray daga Napoli, ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarorin ƙungiyar ta ƙasar Turkiyya, ciki har da lashe kofin ƙalubale. A yanzu haka, shi ne ɗan wasan da ya fi ci wa Galatasaray ƙwallaye a dukkanin da ta ke bugawa a bana, ya bar sauran fitattun ’yan wasa irin su Leroy Sane da Mauro Icardi a baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2, 2025 Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025
    Akpabio ya mayar da martani cewa ba su da niyyar ɓata lokaci, inda ya ce, “Ba zan jira kowa ba, saboda da zarar an tantance su, ba za a sake ganinsu ba.” Daga nan sai ‘yan majalisar suka shiga zaman sirri domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86 November 5, 2025
      Sakamakon kwamitin, wanda ke dauke da kusan shafuka 40 ya bayyana shawarwari kan gyare-gyare da matakan da za a dauka na gaggawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Labarai Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista November 5, 2025 Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio November 5, 2025
    Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum,  ya mika motocin sintiri 63 ga hukumomin tsaro da kuma Rundunar Hadin Gwiwa ta Farar Hula (CJTF) da ke aiki a Maiduguri da kewaye. Daga cikin motocin 63, an ba da motocin 30 ga sassa daban-daban na Sibiliyan JTF, 16 ga Jami’an tsaron kai daukin gaggawa don dakile masu aikata laifukan cin Zarafi, 10 ga kungiyoyin tsaro, 6 ga mafarauta da kuma daya ga jami’an Hukumar Kula da Fataucin Mutane (NAPTIP). Rarraba motocin yana da nufin inganta karfin yin sintiri da mayar da martanin gaggawa musamman ga ‘yan sanda, sauran jami’an tsaro, da rundunar hadin gwiwa ta farar hula wajen magance barazanar...
    Ana ci gaba da tattara gawarwakin mutane da mayakan kungiyar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai DaukinGaggawa suka kashe a jihar Arewacin Kordofan na kasar Sudan. Kungiyar Likitoci na Kasar Sudan ya ruwaito cewa: Ana ci gaba da tattara gawawwakin mutane a Arewacin Kordofan, bayan da mayakan Rappid Support Forces suka farma yankunan a kokarin da suke yi na kwace iko da jihar baki daya. Kungiyar Likitoci ta Sudan ta bayyana cewa, tana bin diddigin manyan laifukan da Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces suke aikatawa kan fararen hula marasa makamai a birnin Bara da ke jihar Arewacin Kordofan. Kungiyar ta tabbatar da cewa: Gawawwaki da dama sun taru a cikin gidaje a cikin birnin, kuma mayakan Rapid...
      Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.   Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya a Borno. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya November 4, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025 Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi  November...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan Rasha Mikhail Mishustin yau Talata a birnin Beijing, inda suka yi kira da inganta dangantakar kasashen biyu a bangarori daban-daban da kyautata hadin gwiwarsu kan dabarun samun ci gaba. Ya ce tun daga farkon bana, Sin da Rasha ke gudanar da harkokinsu cikin nutsuwa duk da yanayi na hargitsi da suke fuskanta a waje, inda suka mayar da hankali kan ingantattun muradun ci gaba. Ya ce karfafawa da daukakawa da ci gaba da gudanar da hulda tsakanin kasashen biyu, muhimmin zabi ne da bangarorin biyu suka yi. Da yake bayyana cewa an tsara taswirar bunkasa dangantakar kasashen biyu ne yayin taron da suka yi da shugaba Vladimir Putin a bana, shugaba...
    Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karatu mai zurfi ba sun fi wadanda suka yi karatu mai zurfi samun aikin yi. NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Wadansu dalilai ne ke kara kawo rashin...
    A shekarar 2023 lokacin da Gwamna Lawal ya hau mulki, Zamfara ta kasance a ƙasan jadawalin a matsayi na 36.   Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na jihar sun ƙaru da kashi 182.34%, daga naira biliyan 87.44 a 2023 zuwa naira biliyan 246.88 a 2024. Haka kuma jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya ta ƙaru zuwa naira biliyan 315.53, ƙaruwar kusan kashi 118%. Haraji da jihar ta tara ya kai kusan kashi 10.31% na jimillar kuɗaɗen shiga a 2024.   BudgIT ta bayyana cewa wannan ci gaban yana nuna Zamfara ta fara rage dogaro ga kuɗin kason asusun tarayya, kuma idan za a yi hasashe, jihar na da ƙarfin kai da kai idan za a kalle ta a matsayin ikon...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025 Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025 Wasanni Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray October 30, 2025
    Taron kaddamar da rabar da taraktocin noman, ya gudana ne a Shalkwatar Ma’aikatar Kula da Aikin noma da kuma yin Noman Rani da ke garin Kalaba.   Kazalika, taron ya samu halartar ‘yan Majalisa da Sarakunan Gargajiya da kungiyoyin manoma mata da masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma da ke jihar da abokan hadaka.   Daukacinsu, sun jinjina wa wannan kokari na gwamna Bassey, kan wannan hangen nesa da gwamnatinsa ta yi, na kaddamar da taraktocin noman, musamman domin ciyar da fannin aikin noman jihar gaba, duba da cewa; fannin ne kinshikin tattalin arzikin jihar.   Har ila yau, gwamna Bassey, ya nanata kudurin gwamnatinsa wajen ci gaba da bai wa fannin aikin noma muhimmanci a matsayin fannin...
    A wani bidiyo daban da PUNCH Metro ta gani a Facebook, wanda Mc Pee ya wallafa, wani mutum da ake zargin dalibi ne na jami’ar ya bayyana abin da ya faru. A cewarsa, marigayin ya roki a bar shi ya rayu kafin daga bisani wanda ake zargin ya kashe shi. Ya ce: “Nanpon ya riga ya yanke Peter a kumatunsa yayin da yake rokon a bar shi. Lokacin da muka shiga tsakani muka ce ya daina, sai ya yi barazanar yanka duk wanda ya kusanto shi. “Da Peter ya ga ba ya sauraron rokonsa, sai ya rungume shi yana rokonsa da kuka. “Mun fita neman taimako amma babu wanda ya amsa mana. Da Peter ya yi kokarin tserewa sai ya...
    Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.   Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da...
    Gwamnatin kasar Iran  ta sanar da ranar 30 ga watan nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar kasa ta tsibirin Abu Musa tumbu babba da tumbu karami da ta karbo daga hannu birtaniya a shekaru da suka gabata, wanda yayi daidai da 9 ga watan Azar na kalandar iraniyawa . Tsibiran guda 3 da ake takaddama akansu Abu musa da tunbu babba da karami  suna yankin tekun fasha ne tsakanin mailand na iran da kuma hadaddiyar daular larabawa, tsibbiran wani bangare ne na kasar iran tun karnoni da suka gabata da ke cike da abubuwa da suka safi doka da tarihi  a iran da kuma kasa da kasa. Iran ta jaddada cewa dukkan wadannan tsibirai guda 3 wani bangare na kasarta...
    A cewar ta a cikin shekarar 2024 jihar Katsina kawai ta samu masu wannan cuta mutum 17 tare da guda biyu a karamar hukumar Danmusa a cikin wannan shekara Haka kuma Hajiya Zulaihat Radda ya bada tabbacin cewa kowane yaro an tabbatar da ya amshi allurar Riga-kafin shan Inna Ana jawabin wakilin asusun tallafawa yara na UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ta yabawa kokarin jihar Katsina na dawo da sabon yunkurin kawar cutar shan Inna a Nijeriya baki daya Ya kuma bayyana cewa asusun kula da kananan yara na UNICEF Yana hadin gwiwa da gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi domin ganin wajen fadakar da al’umma akan allurar Riga-kafin shan Inna a jihar...
    Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar. Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa. Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma  October 30, 2025 Daga Birnin Sin Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC October 30, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya October 30, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba October 30, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21 October 30, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai October 30, 2025
    Kwamandan Runduna Kai Daukin Gaggawa ta kasar Sudan ya yi ikirarin kafa kwamitoci don binciken kisan kiyashin da aka yi a birnin El Fasher Kwamandan Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Sudan (RSF), Muhammed Hamdan Dagalo “Hemedti,” ya amince a ranar Laraba cewa: Mayakansa sun aikata “keta haddi” a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan. Ya yi ikirarin cewa: An kafa kwamitocin bincike kuma sun riga sun isa birnin domin fara ayyukansu. A cikin wani jawabi na bidiyo, Hemedti ya ce, “Ya ga keta haddi da aka yi a El Fasher, kuma daga nan ya sanar da kafa kwamitocin bincike, ba kawai kafa kwamitoci ba, har ma kwamitocin bincike sun riga sun isa birnin na El...
    “Muna kira ga hukumar da sauran hukumomi su tabbatar da adalci da daidaito a lokacin ɗaukar ma’aikata na gwamnatin tarayya,” in ji shi. Shugaban Majalisar ya yaba wa Dala bisa kishin ƙasa da ya nuna, sannan ya umarci kwamitin majalisar da ya binciki lamarin tare da gabatar da rahoto domin ɗaukar mataki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II October 30, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa October 30, 2025 Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU October 29, 2025
    Kasar Rasha ta sanar da samun nasarar gwajin jirgi maras matuki  na nukiliya wanda yake ninkaya a cikin ruwa. Gwajin dai ya biyo bayan wasu gwaje-gwajen da Rashan ta yi ne na makamai masu linzami samfura mabanbanta masu iya daukar makaman  Nukiliya. Jirgin  maras matuki mai daukar makamin Nukiliya  yana a karkashin rundunar sojan ruwan kasar,da aka bai wa sunan; Bosidon. Bugu da kari shi kanshi jirgin yana aiki ne da nukiliya a matsayin makamanshin da yake tafiyar da shi. Shugaban kasar Rasha Vladmir ya ce; babu wata na’ura wacce za ta iya dakatar da wannan jirgin  mai ninkaya a cikin ruwa na Nukiliya. Shugaban kasar ta Rasha ya kara da cewa; Wannan sabon makamin babu kwatankwacinsa a duniya saboda...
    Shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na kasar Turkiya Rajab dayyib ardogan da ma alummar kasar na farincikin zagayowar ranar da kasar ta samu yancin kai, kuma ya jaddada muhimmancin kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Iran da Turkiya suna da alaka mai zurfa ta tarihi aladu da kuma dabarun yaki, a daidai lokacin da ake samun sauyi a yankin , akwai bukatar kasashen biyu sun kara hadin guiwa a fannonin kasuwanci tsaro da kuma diplomasiya, sakon na pezeshkiyan ya nuna aniyar iranta fifita yin hulda tsakanin kasashen biyu Akwai abubuwa da dama da suka yi kama da juna tsakanin kasashen biyu masu abokantaka da yan uwantaka, pezeshekiyan, ya kara da cewa ta...
    Mummunan cin zarafi a birnin El Fasher na kasar Sudan ya haifar da tofin Allah tsine da Allah wadai daga al’ummomin ƙasashen duniya da na cikin gida Kisan gilla da laifukan da ake aikatawa kan fararen hula a El Fasher, Arewacin Darfur, sun jawo Allah wadai daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin dan adam, yayin da gwamnati da hukumomin yankin ke musayar zarge-zarge game da musabbabin bala’in da kuma nauyin da ke kan al’ummar duniya. An ci gaba da Allah wadai da kasashen duniya da na cikin gida game da take hakkin da Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta aikata kuma har yanzu take aikatawa kan fararen hula a El Fasher Arewacin Darfur. Kwamishinan...
      Kuri’un na jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin, da jami’ar Renmin ta kasar suka gudanar, karkashin cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani, sun tattaro ra’ayoyin jama’a daga manyan kasashen duniya masu tasowa, da ma na kasashe masu samun saurin ci gaba. (Mai fassara: Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas October 28, 2025 Daga Birnin Sin Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika October 28, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 October 28, 2025
    Kasar Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji zuwa Ukraine don taimakawa Kyiv. Hukumar leken asiri ta Rasha (SVR) ta bankado cewa Faransa ta shirya aika Sojoji 2,000 zuwa Ukraine. Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta kira wannan yiwuwar “abin da ba za a yarda da shi ba,” tana mai gargadin hadarin dake tattare da shi. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta shawarci Paris da ta yi amfani da wadannan sojojin don kare gidajen tarihi na Faransa maimakon tura su a Ukraine. Dama a baya ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta bayyana cewa duk wani yanayi da ya shafi tura sojojin NATO a Ukraine ba abin yarda ba ne ga Rasha kuma yana iya fuskantar barazanar...
    Shugaba Tinubu, a cikin wasikarsa, ya ce, an yi nadin ne bisa tanadin Sashe na 18(1) na Dokar Sojojin Kasa, Cap A20, ta Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004.   Ya bukaci Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da wannan bukatar don gaggawa kan tabbatar da daidaito mai inganci a cikin tsarin tsaron kasar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025
    Wakil, ya gargaɗi masu yaɗa labaran ƙarya da su daina, yana mai cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci bisa dokar laifuka ta amfani da kafafen sadarwa. Ya tabbatar da cewa ba a ƙone gidan shugaban jam’iyyar PDP ba, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin. Ya shawarci mazauna yankin da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, yayin da hukumomi ke ci gaba da sanya ido kan lamarin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi October 28, 2025 Labarai Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025
    An ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, da wasu mutum shida a ranar Litinin bayan sun kasa miƙa takardun da ake buƙata a kotu. Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, haɗa baki wajen yin laifi, da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai miliyoyin Naira. APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa Lokacin da aka fara sauraren shari’ar, lauya mai kare gwamnati, Adeola Adedipe (SAN), ya ce sun shirya fara gabatar da shaidu, amma lauyoyin Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma suka nemi ƙarin lokaci,...
    Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara akan harkokin siyasar kasa da kasa Dr.  Ali Akbar Wilayati ya ce; Da akwai kasashe uku a cikin Asiya wadanda suke da ‘yanci da su ne Iran, China da Rasha, kuma suna taka rawa domin samar da sabon tsarin tafiyar da duniya. Dr. Wilayati ya bayyana hakan ne dai a yayin ganawarsa da jakadan China a Iran “Zong Bi Wuu” yana mai kara da cewa; Alaka a tsakanin kasashen biyu ta dade da kuma zurfi.  Har ila yau Wilayati ya ce alakar kasashen biyu ta ginu ne akan maslaha da kuma girmama juna da kuma cin gashin kai na siyasa, da hakan ya mayar da su, tare da kasar Rasha zama...
    Shugaban majalisar Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewa, wasika ta hadin gwiwa da Iran, Rasha da China suka aike wa Majalisar Dinkin Duniya a cikin ‘yan kwanakin nan, da ke adawa da yunkurin Turai na sake dawo da takunkumi kan Iran wannan ya nuna hadin gwiwa mai karfi a tsakanin manyan kasashen uku. Ya yi wannan jawabin ne a lokacin wani zaman majalisa a Tehran a ranar Lahadi, mako guda bayan da kasashen uku suka mika wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Kwamitin  Tsaro wasikarsu, inda suka tabbatar da kawo karshen aikin kuduri mai lamba 2231, wanda ya amince da yarjejeniyar nukiliya ta 2015 wadda Amurka ta yi watsi da ita. “A cikin ‘yan kwanakin nan, mun shaida...
    Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i.  Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000 daga gwamnatin tarayya wanda zai taimaka wa sana’o’insu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya  Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen ƙirƙirar ayyuka, wanda yanzu haka an samar da kuɗaɗai har naira biliyan 5.5, inda aka raba biliyan ɗaya ga mutane 701 a faɗin jihar.  Gwamna Raɗɗa...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Sakon wasikar da Iran, Rasha, da China suka aika ga Majalisar Dinkin Duniya alama ce ta hadin kai Shugaban Majalisar shawarar Musuluncin ya bayyana wasiƙar da ma’aikatun harkokin waje na Iran, Rasha, da China suka aika wa Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin tsaro a matsayin wata alama ta haɗin kai mai mahimmanci tsakanin waɗannan ƙasashe uku, yana mai cewa, “Da karewar kuduri mai lamba 2231, wa’adin Darakta Janar na IAEA na tabbatarwa da sa ido kan aiwatar da shirin makamashin nukiliya na Iran ya ƙare.” Mohammad Baqer Qalibaf ya ce a wani zaman jama’a na Majalisar Shawarar Musulunci a ranar (26 ga Oktoba) da kuma a jawabinsa ga Majalisar ya bayyana...
    A yau Asabar 25 ga wannan wata, ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar sun gudanar da liyafar murnar kebe ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan, a dakin taro na Diaoyutai dake birnin Beijing. Wakilan bangarori daban daban na yankin Taiwan da na babban yankin kasar Sin masu halartar bikin murnar cika shekaru 80 da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan da safiyar wannan rana sun halarci liyafar. Direktan ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa October 24, 2025 Daga Birnin Sin An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan October 24, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15  October 24, 2025
    Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasashen Yamma sun taka dokokin kasa da kasa a batun Iran Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov ya soki matakan ƙasashen Yamma, ciki har da harin soji da suka kai wa Iran da kuma ƙoƙarinsu na sake Sanya mata takunkumi, yana mai cewa, “A wannan yanayin, ƙasashen Yamma sun taka dokokin ƙasa da ƙasa.” Jaridar Kommersant ta ruwaito cewa: Ryabkov ya yi waɗannan kalaman ne a lokacin wani shirin yanar gizo mai taken “Tarihi da Siyasar Yanzu na Manufofin Nukiliya na Rasha da Diflomasiyyar Jama’a a Bangaren Nukiliya,” wanda Cibiyar Makamashi da Tsaro ta shirya. Yayi nuni da cewa: “Yanayin Iran, ƙasashen Yamma sun taka dokokin ƙasa da ƙasa...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya jagoranci wani taron karawa juna sani a ranar 27 ga watan Augusta, domin jin ra’ayoyin wadanda ba ‘yan jam’iyyar ba, dangane da shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar game da tsara shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 15, da ke da nufin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar. (Fa’iza Muhammad Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu October 24, 2025 Daga Birnin Sin Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da...
    Tawagar kamfanin na Rano Air a wurin ganawa da gwamnan, ta haɗa da Babban Manajan (Ayyuka), Abah O. Godwin; da Accountable Manager Alhaji Lawal Sabo Bakinzuwo; da Shugaban Sashin Ayyuka na ƙasa Bashir Abdullahi Wudilawa; da Shugaban Sashin Bunƙasa Harkokin Kasuwanci na kamfanin, Auwal Sulaiman Ubale. Jami’an kamfanin sun tabbatarwa gwamnan cewa kamfanin na Rano Air zai samar da nagartacciyar hidima abar dogaro, mai inganci kuma mai haba-haba ga kwastomomi, ta yadda za a samu sauƙin tafiye-tafiyen kasuwanci da bunƙasa harkokin tattalin arziki a faɗin jihar da Arewa Maso Gabas baki ɗaya. “Gwamna Inuwa Yahaya ya yi maraba da wannan ci gaba, inda ya bayyana hakan a matsayin wata shaida kan yadda Jihar Gombe ke da zaman lafiya da kwanciyar...
    MDD ta bayyana cewa a tsakanin kowadanne mutanen Gaza  4, daya daga cikinsu yana fama da yunwa. Mai Magana da yawun kungiyar Agaji ta tarayyar turai, May Musa Sayegh, ta yi ta’aliki akan wannan adadin na masu fama da yunwa a Gaza, inda ta ce; Wannan shi ne hakikanin abinda yake faruwa a kasa, kuma ya shafi mata manya da ‘yan mata da kuma kananan yara masu yawa.” May Musa Sayegh ta fada wa tashar talabijin din aljazira cewa; Sakamakon hare-hare na tsawon shekaru biyu da kuma rashin samun damar shigar da kayan agaji,musamman a arewacin Gaza aka fada cikin wannan halin. Sayegh ta kuma ce; ta fuskar kiwon lafiya, al’amurra suna kara tabarbarewa, domin mutane suna rayuwa cikin bakin...
    Rasha ta miƙa wa Ukraine gawarwakin sojoji 1,000 da suka mutu a fagen daga, a cewar wata hukumar gwamnatin Ukraine da ke kula da lamurran fursunonin yaƙi. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa ita ma Rashar ta karɓi gawarwakin sojoji 31 daga ɓangaren Ukraine. Messi ya tsawaita kwantiraginsa da Inter Miami Jami’an tsaro sun kama Sowore saboda shirya zanga-zanga Musayar fursunonin yaƙi da kuma gawarwakin sojoji da suka mutu na daga cikin al’amuran haɗin gwiwa da har yanzu ke gudana tsakanin Kyiv da Moscow, tun bayan mamayar da Rasha ta kai Ukraine a Fabrairun 2022. Rahotanni daga Kyiv sun ce musayar gawarwakin na daga cikin yarjejeniyar da ɓangarorin biyu suka cimma domin bai wa iyalai damar binne...
    Fadar mulkin kasar Rasha Krimlne ta sanar da cewa, shugaban kasar Valdmir Putin ne ya sa ido akan yadda rundunar dake kula da makaman Nukiliya ta gudanar da rawar daji a sansnain “Blisitiks”. Sanarwar ta kara da cewa, rundunar dake kula da muhimman makakan Nukiliyar kasar ta Rasha  ta yi amfani da makamai masu linzami samfurori mabanbanta. Haka nan kuma fadar gwamnatin Rashan ta ce, an gudanar da  dukkanin gwaje-gwajen cikin nasara, an kuma yi ne domin tabbatar da cewa rundunar tana cikin shirin ko-ta-kwana. A wani labari mai alaka da Rasha, ma’aikatar harkokin waje ta gargadi kasashen turai akan kokarin bai wa Ukiraniya kudadenta da suke a cikin bankunansu. MA’aikatar harkokin wajen Rasha ya fadawa kasashen turai din cewa...
    An tsara cewa a cikin wannan makon da aka shiga ne dai za a gana a tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Amurka da Rasha domin share fagen ganawar shugabannin kasashen biyu. Fadar mulkin Amurka “ White House” ta bayyana cewa an yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin ministocin harkokin wajen Amurka da Marco Rubio da Sergey Lavrov a shekaran jiya inda su ka cimma matsaya akan cewa, ganawar ba ta zama dole ba. A makon da ya shude ne dai shugabannin kasashen Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladmir Putin su ka yi ttataunawa ta wayar tarho, inda su ka cimma matsaya akan ganawa a birnin Budaphast na kasar Bulgaria. A cikin watan Ogusta na wannan shekarar an...
    A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka. Wannan ya kasance wani bakon abu a fili kuma abin kyama. An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar...
    Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, mako guda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa a ranar 16 ga watan Oktoba. Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin? Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja  A yayin taron, Shugaba Tinubu ya buƙaci Farfesa Amupitan da ya tabbatar am gudanar da sahihancin zaɓe a Nijeriya tare da inganta INEC domin tabbatar da gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci. An tabbatar da naɗin Amupitan bayan Majalisar Dattawa ta...
    Bisa kididdigar da hukumar kula da kudaden kasashen waje ta kasar Sin ta gabatar a yau ranar 22 ga wannan wata, a watan Satumba, yawan kudin da aka yi hada-hadarsu ta fuskar samun kudin shiga da kuma wadanda aka kashe na kamfanoni da daidaikun mutane da sauran hukumomin da ba na banki ba na kasar Sin ya kai dalar Amurka triliyan 1.37, wanda ya karu da kashi 7 cikin dari bisa na watan Agusta. Yawan kudin shiga da na kashewa da ya shafi kudaden kasashen waje na kasar Sin a farkon rabu’i na uku na bana ya kai dalar Amurka triliyan 11.6, wanda ya kai matsayin koli a tarihi, kana ya karu da kashi 10.5 cikin dari bisa na makamancin...
    Ahmed maiyaki, ya dade yana bayar da gudummawa a harkar yada labarai a a fadin kasar nan bayan kasancewarsa tsohon ma’aikaci a sashin hausa na rediyon Faransa ( FRI).   Jihar Kaduna ta kwashe shekaru takwas babu ma’aikatar yada labarai wacce tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya rufeta , sai bayan lashe zaben gwamna Uba Sani ya dawo da ma’aikatar wacce aka dorawa alhakin kula da yada manufofin gwamnatin jihar . ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince...
    “Da ba sojoji, da ba za mu iya gudanar da wannan taro cikin kwanciyar hankali ba. Don haka dole mu ci gaba da ƙarfafa musu gwiwa,” in ji shi. Sarkin Musulmi ya kuma nuna damuwa kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo ba tare da tunani ba, inda ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace don tsara amfani da su, inda ya bayyana cewa shi kansa ya taɓa fuskantar matsala bayan yaɗa labaran ƙarya a kansa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin...
    A gefe guda kuma ta roƙi jama’a su yi watsi da rahoton jaridar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Labarai Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe October 22, 2025
    Majalisar Dattawa ta amince da sabuwar doka da ta tanadi daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata da yaro ko yarinya karama. Dokar na son kare hakkokin kananan yara ne, kuma ta shafi maza da mata baki daya, ba tare da wani zabi na biyan tara ba. Sanata Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa), ya ce yara ba su da iko ko yardar wajen amincewa da yin jima’i kuma irin wannan abu na jefa su cikin tashin hankali har abada. Da farko ya ba da shawarar a daure mai laifi na tsawon shekaru 20, amma yawancin sanatoci sun nemi hukunci mafi tsauri. Sanata Muhammad Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya) ya bayar da shawarar daurin rai da...
    Babban jam’in hukumar tsaro ta kasar iran ya bayyana jin dadin kasar iran ga kasar Rasha saboda goyon bayan da ta bata a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya kan hakkin iran a gaban kasashen turai dake kokarin kakkaba mata sabon takunkumin karya tattalin Arziki, Babban sakataren tsaro na kasar Iran Dr Ali Larijani ya fadi hakan ne a jiya talata A wata ganawa da yayi da jakadan shugaban kasar Rasha Alexander Lavrentiev da ya kawo ziyara nan kasar iran , larijani a matsayinsa na mai bawa jagora shawara ya jinjinawa kasar rasha game da goyon bayan da take bawa kwamitin. LarIjani da sauran jami’an gwamnatin kasar Rasha sun yi bitar matakin hadin guiwa dake tsakanin Tehran da mosko a...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na makonni biyu da ta fara. Ƙungiyar ta kuma bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin wata ɗaya don biyan buƙatunta. Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe ASUU ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta gaza ɗaukar mataki cikin wa’adin da ta bayar, za ta iya komawa yajin aiki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas October...
    Ya ƙara da cewa shirin ya dace da shirin jihar, inda zai mayar da hankali kan bunƙasa samar da abinci a gida da karfafa matan gida wajen kula da abinci mai gina jiki. Gwamnan ya bayyana cewa majalisar kula da abinci ta jihar za ta jagoranci tsara manufofi, haɗin kai da kuma kula da aiwatar da shirin a dukkanin kananan hukumomin jihar. “Mun ƙuduri aniyar tabbatar da cewa wannan shiri ya ɗore tare da haɗin kan gwamnati da abokan hulɗa,” in ji shi. A nasa ɓangaren, kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Hon. Abdulmalik Gajam, ya ce gwamnatin Gwamna Lawal na taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkar lafiya da abinci mai gina jiki ga yara ƙanana. Haka kuma, Misis Uju Rochas...
    Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago. Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya “Tunaninmu yana tare da iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna godiya ga ma’aikatan agajin gaggawa bisa taimakon da suka bai wa waɗanda abin ya rutsa da su,”...
    Ministan harkokin wajen Habasha Gideon Timotheos ya ce ya tattauna da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov kan batutuwa daban-daban da suka Shafi dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma yadda za a kara inganta su. Timotheos ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai bayan tattaunawar da ministocin biyu suka yi a ranar jiya  Talata, inda ya ce, “A yau mun tattauna kan yadda za a gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin a fannin nukiliya, da kuma a fannonin zuba jari, binciken kimiyya, da musayar al’adu.” Ya kara da cewa, “Ciniki tsakanin kasashen biyu yana karuwa, amma idan aka kwatanta da damar da kasashen biyu suke da ita,  akwai abubuwa da dama da ya kamata a kara ingantawa da kuma habaka...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta? October 21, 2025 Daga Birnin Sin Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin October 21, 2025 Daga Birnin Sin Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia October 21, 2025
    Kwamandan ya ƙara da cewa yayin yaƙin “Operation Zero” na shekarar da ta gabata (Disamban 2024 zuwa Janairun 2025), mutane 432 ne suka mutu, yayin da 2,070 suka jikkata a haɗura 533; adadin ya ragu idan aka kwatanta da na baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi  October 21, 2025 Labarai ’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu October 21, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025
    Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya sanar a wannan  Litinin cewa, kasar Rasha a shirye take ta fadada hadin gwiwa da Iran a dukkan bangarori, yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana ci gaba da kara habaka, da kuma  amincewa da juna. Peskov ya yi nuni da cewa, Moscow na goyon bayan ci gaba da shawarwari kan yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran, yana mai jaddada cewa, “Matsayar da kasashen turai suka dauka game da batun Shirin ba ta da amfani, kuma hakan  yana kara  dagula lamurra, da kuma kawo cikas ga  duk wani ci gaba na hakika kan wannan batu.” In ji shi. Wannan matsayi na Rasha, na zuwa ne a daidai lokacin da lamurra suke kara rincabewa a...
    Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya sanar a wannan  Litinin cewa, kasar Rasha a shirye take ta fadada hadin gwiwa da Iran a dukkan fannoni, yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana ci gaba da kara habaka, da kuma  amincewa da juna. Peskov ya yi nuni da cewa, Moscow na goyon bayan ci gaba da shawarwari kan yarjejeniyar nukiliyar Iran, yana mai jaddada cewa, “Matsayar da kasashen turai suka dauka game da batun Shirin Iran na nukiliya ba ta da amfani, kuma hakan  yana kara  dagula lamurra, da kuma kawo cikas ga  duk wani ci gaba na hakika kan wannan batu.” In ji shi. Wannan matsayi na Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da lamurra suke kara...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027 October 17, 2025 Siyasa Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025
    Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Indiyan nan Asrani ra rasu. Asrani, wanda  asalin sunansa shi ne Govardhan Asrani, ya rasu yana mai shekaru 84, kuma ya shafe sama da shekara 50 yana fitowa a finafinan Indiya, inda ya fito a finafinai sama da 350. Dan wasan finafinan, ya shahara wajen taka rawar barkwanci da kuma ƙaramin jarumi wanda ake kira da mai taimaka wa jarumi wato supporting actor. Daga cikin fina-finansa da suka yi fice akwai Sholay, inda ya fito a matsayin ɗansand da Bawarchi da Chupke-Chupke da Hera Pheri da Muqabla da Dhamaal da Yamla Pagla Deewana da Dillagi da Welcome da Bhool Bhulaiya da Garam Masala da Baghban da The Burning Train da Ajnabee da Seeta aur Geeta da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a October 20, 2025 Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025 Manyan Labarai Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi October 19, 2025
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace. Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu. Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban  wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta  ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa. Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo. Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace. Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu. Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban  wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta  ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa. Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo. Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC...
    Hukumar gudanarwa ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da Mai Ba da Shawara a harkokin koyarwa na ƙungiyar, Ogenyi Evans, da Babban Koci, Ahmed Garba (Yaro Yaro), saboda rashin gamsasshen sakamako da ƙungiyar ke samu a farkon kakar wasa ta 2025/2026 Nigeria Premier Football League (NPFL).   A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon jerin sakamakon wasanni marasa kyau da suka gaza cika tsammanin masoya da masu ruwa da tsaki a ƙungiyar.   Ya yanzu dai, kungiyar ta Sai Masu Gida ta buga wasanni takwas, inda ta samu nasara a biyu kacal, ta kuma tashi kunnen doki a wasanni 2, sannan suka sha kaye a...
    Don haka, an nada “tsohon kaftin din kungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da mai horar da masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu, su maye gurbin wadanda aka sallama na dan wucin gadi. Bugu da kari, Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai taimakawa wadanda aka nada na dan wucin gadin”.   LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kungiyar mai taken ‘Sai Masu Gida’ tana fama a ‘yan makonnin nan. Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta kuma ci tarar kungiyar tarar kudi sama da Naira miliyan 9 biyo bayan rikicin da ya ɓarke a yayin da suke karawa da wata kungiya a filin wasa na Sani Abacha. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A...
    An ce wanda ake zargi da kisan, sananne ne a garin Zing saboda yawo a kan tituna, sanye da fararen kaya yana yin kamar yana wa’azi.   Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin da ya faru da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar, ya jefa al’ummar garin Zing da kewaye cikin rudani kan hakikanin yanayin lafiyar wanda ake zargin.   “Daga cikin wadanda suka jikkata akwai ’yan banga guda biyu, wadanda a baya suka yi kokarin hana wanda ake zargin shiga jama’a saboda irin halayyarsa,” in ji wani ganau. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025 Labarai Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC October...
      Yayin da yanayin duniya ke fama da fadadar matakan kashin kai da kariyar cinikayya, masu bayyana ra’ayoyin sun bayyana gamsuwa da tabbacin kasuwar kasar Sin, da damammakin da bude kofar kasar bisa matsayin koli ke samarwa duniya.   A shekarar nan ta 2025, binciken ya nuna kaso 72.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na kallon kasar Sin a matsayin mai bude kofa, wadda kuma ke amincewa da takara. Har ila yau, kaso 79.8 bisa dari na ganin babbar kasuwar Sin na samar da muhimman damammaki ga kasashensu. Kaso 79.8 bisa dari kuma, na kallon Sin a matsayin mai samar da kyakkyawar damar gudanar da kasuwanci dake janyo hankulan masu zuba jari na waje. Sai kuma kaso 78 bisa...