2025-11-14@03:24:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1275
«Wannan yana»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Hukumar Kwastam ta Kano/Jigawa ta kama jimillar kafso guda 261,750 na Polyglycine (miligiram 300) da allunan Tramadol hydrochloride 228,700 (miligiram 225) da aka boye a cikin buhunan jumbo guda biyar. Shugaban hukumar kwastam na yankin Kano, Dalhatu Abubakar, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce an boye magungunan ne a cikin fakiti 35 na Polyglycine da kuma allunan Tramadol 28. Yayin da yake mika haramtattun magungunan ga wakilin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, Konturola Dalhatu Abubakar, ya ce abubuwan na da illa ga lafiya da suka hada da lalata gabobi, jaraba, da rashin natsuwa, musamman a tsakanin matasa. Abubakar yayi gargadi game da illolin...
Masar ta jaddada goyon bayanta ga zaman lafiyar Sudan tare da yin watsi da matakan bangare guda kan kogin Nilu Kasar Masar ta jaddada cikakken goyon bayanta ga zaman lafiyar kasar Sudan da kuma yankinta a jiya Laraba, tare da tabbatar da hadin kan matsayar kasashen biyu da kuma kin amincewa da matakan bangare daya kan kogin Nilu. Wannan dai ya zo ne a wata ganawa da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty da shugaban majalisar gudanar da mulkin Sudan Abdel Fattah al-Burhan suka yi a birnin Port Sudan, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar. Abdel Aty ya ce ziyararsa ta uku zuwa Port Sudan cikin shekara guda sako ne na nuna goyon baya...
Mazauna unguwar Sabon Gero, dake bayan Millennium City a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, sun roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta kammala aikin gyaran titin unguwar, wanda suka ce an bar shi a cikin mawuyacin hali duk da cewa an bai wa wani kamfani aikin kusan shekara guda da ta gabata. Mazauna yankin sun bayyana cewa halin da hanyar take ciki ya jefa su cikin matsanancin rayuwa, musamman mata masu juna biyu da ke tilasta musu hawa babura domin neman kulawa a wajen unguwar, kasancewar babu asibiti a yankin. Ɗaya daga cikin mazauna, Rashida Shehu, wadda ke da juna biyu, ta ce ta ji rauni a lokacin da take kokarin bin hanyar zuwa gari domin kula...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Manyan garuruwan da suka shiga cikin wannan jerin sun haɗa da Mubi, Gusau da Azare. Ma’aikatar ta roƙi jami’an gwamnati a jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su sa ido sosai kan halin da ake ciki kuma su bayar da rahoto a kan lokaci. Haka kuma, ta shawarci jama’a da ke zaune kusa da koguna ko rafuka su ɗauki matakan kariya ko su bar waɗannan wurare domin guje wa ambaliyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majiyoyin tsaro sun ce waɗannan hare-haren wani ɓangare ne na yunƙurin karya ƙarfin ’yan ta’adda da kuma katse hanyoyin samun kuɗaɗensu ta hanyar safarar miyagun ƙwayoyi, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma sata man fetur. Sun kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da ba da bayanai ga hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga a faɗin ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniya ta musamman da kasar china a halin da ake ciki a yankin da kuma yadda duniya take sauyawa da sauri ya zama wajibi ga kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin da yake gabatar da sakon murna ga gwamnatin kasar China kan cika shekaru 76 da kafuwar kasar. Wanda kuma itace ranar kasa a kasar ta China. Pezeshkiyan ya kara da cewa wannan ranar ta samuwar kasar China, rana ce da hadin kai da ci gaba da kuma godewa ga irin ci gaban da kasar ta samu daga lokacin zuwa yanzu a cikin gida da kuma fagen kasa da...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha, don haka na aike da jiragen ruwa masu makaman Nukiliya da shi ne makamai mafi hatsari.” Shugaban kasar na Amurka ya riya cewa kasarsa tana gaba da kasashen Rasha da China da ci gaban shekau 25 a fagagen kimiyya dakuma kera jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa.” Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my...
Ɓangarorin biyu sun tashi baran-baran a wata tattaunawar da suka yi ƙarƙashin jagorancin Ministan ƙwadago na Nijeriya, Mohammed Dingyadi a ranar Litinin. Wannan yajin aiki na PENGASSAN ya shafi rufe ɓangarori da dama na harkar mai a Nijeriya, ciki kuwa har da babban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, tare da dakatar da ba matatar Ɗangote ɗanyen mai. Kungiyar ta PENGASSAN ta ja daga, inda ta bayyana cewa, “Muna kan bakar mu har yanzu, saboda mutanen mu da aka kora daga aiki, muna so dole a mayar da su.” Wannan na zuwa ne a yayin da wata kotun Abuja ta bayar da umarnin hana yajin aikin ƙungiyar ta PENGASSAN da ɗaukar matakin hana kai wa matatar Ɗangote ɗanyen...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda ya gudana yau Talata a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Shugaba Xi, ya jaddada cewa a gabar da yanayin harkokin duniya ke saurin sauyawa cikin sama da karni guda, dole ne a yi aiki tukuru wajen yayata akidun bai daya na dukkanin bil’adama, da aiwatar da tsarin cudanyar mabanbantan sassa, da ingiza aiwatar da shawarwarin bunkasa ci gaban...
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan aiki daya tilo na karamci da adalci ya sake farfado da fatan ma’aikatan jinya da yawa a cikin gwamnatin ku da kuma a cikin ajandar sabunta fata na Shugaban kasa,” in ji sanarwar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Iran zata iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran a yau, kamar irin abubuwan da ta faru a baya, za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali, da kuma cike da zaman lafiya, da abota, da zaman tare, da tattaunawa, kuma za ta iya sanya tausayi ya mamaye harshen bai daya ta hanyar yin amfani da arzikin al’adu. A cikin sakon da ya gabatar a wurin taron karrama mawakan Iran Shams Tabrizi da Mawlana Jalaluddin Mohammad Balkhi, shugaba Pezeshkian ya ce a ranar Talata: An ambaci ranakun 29 da 30 ga watan...
A lokacin, sun yi wa motar ‘yansanda ruwan harsasai yayin da ɗaya daga cikin jami’an ya ji rauni, amma an garzaya da shi asibiti. Ya ƙara da cewa daga baya ‘yan bindigar sun sake tare wata hanya a gaba, inda suka sace fasinjoji a motoci uku. Abiodun, ya ce an tura ƙarin jami’an ‘yansanda tare da sauran jami’an tsaro da mafarauta don bin sahun ‘yan bindigar, da nufin ceto waɗanda aka sace da kuma cafke masu laifin. A wani samame daban, Abiodun ya bayyana cewa rundunar ‘yansandan tare da mafarauta sun kai farmaki wani dajin da ake zargin maɓoyar masu garkuwa, a cikin dajin Kokolo da ke Ƙaramar Hukumar Magama. A lokacin arangamar da aka yi da ‘yan bindigar, an...
Shugaban hukumar kula da fice ta kasa iran frud askari ya bayyana cewa yawan adadin huldar kasuwancin na kasashen waje na kasar iran yana ci gaba da gudana tsakaninta da fiye da kasashen duniya 100. Kuma yawansa ya kai dala biliyan 54.311a cikin wata shidan farko na wannan shakarar. Da yake hira da manema labarai ya fadi cewa a cikin wannan lokacin an samu kudi da yawansu yakai dala biliyan 25 da miliyan 944 a kayayyakin da ba na man fetur ba. Yace yawan kayayyakin da aka fitar a tsawon wannan lokaci ya kai tan miliyan da dubu 997, yayin da nauyin kayayyakin da aka shigo da su kuma ya kai tan miliyan dubu 18 zuwa 757. Da yake kwatantan...
Buƙatun da ASUU ke nema sun haɗa da: sake duba yarjejeniyar 2009 tsakaninsu da gwamnati, samar da ƙarin kuɗaɗen bunƙasa jami’o’i, biyan bashin albashin da suke bi, da samar da ingantaccen tsarin kuɗi mai ɗorewa ga jami’o’i. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A taƙaitaccen hukuncin da ya yanke kan ƙarar, Mai shari’a Subilim ya bayyana cewa, ci gaba da yajin aikin zai lalata kasuwancin matatar da gurgunta mafi mahimmancin ayyukan ci gaban tattalin arzikin al’ummar Nijeriya. Alƙalin kotun ya ce, dokar hana ci gaba da yajin aikin za ta ci gaba da aiki har tsawon kwanaki bakwai ne kacal. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya. Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar. ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya FERMA ta ƙaddamar da aikin gyara tsohuwar hanyar Kano Rahotanni sun ce ta fara ƙorafin cewa ba ta jin daɗin jikinta da alamu na rashin lafiya, inda daga daga bisani ta yanke jiki ta faɗi. Sai dai bayan an garzaya da ita asibitin gwamnati na Lapai, likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi mata halinsa. Fatima Adamu Muhammad,...
Idan dai ba a manta ba, gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ilimi ta tarayya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar, Abel Enitan, domin duba buƙatar ƙungiyar ASUU, a wani yunƙuri na tabbatar da ci gaban jami’o’in. Sai dai har yanzu kwamitin bai fitar da wata sanarwa ko sakamakonsa ga jama’a ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an tsaron kasar Burtania sun kama George Gallaway da matar a birnin londan bayan sun shigo kasar daga kasar Rasha a ranar Asabar. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya bayyana cewa Gallawy da matarsa sun shahara da goyon bayan gwagwarmayan falasdinawa da kuma kiyayya ga HKI. Kafin haka gwamnatin kasar Burtania ta amince da samuwar kasar Falasdinu a babban taron MDD, amma amincewar samuwar kasar falasdinu bai hana ci gaba da kissan falasdinawa. Gallawy wanda ya kasashence tsohon dan majalisar dokokin kasar burtaniya, ya kuma karbi kyautar Isma’il Haniyya. Sannan a cikin watan bayun shekara da 2025 inda ya halarci bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar IRAN. Yansandan kasar Burtania sun tsare...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Rashin Amincewa Da Duk Wani Takunkumi Kan Iran
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Ba za a yarda da ƙoƙarin maido da kudurori da suka ƙare ba kan Iran Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Yunkurin da kungiyar Tarayyar Turai Troika da Amurka ke yi na maido da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran, ba abu ne da za a amince da su ba. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da sanarwar mayar da martani ga ikirarin da kasashen Turai uku da Amurka suka yi na maido da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran. Ma’aikatar ta yi la’akari da yin amfani da hanyar warware takaddama da aka tanada a cikin yarjejeniyar hadin gwiwa game da...
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi zargin cewa, cikin watanni shida, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya samu karin kaso daga gwamnatin tarayya fiye da yadda ya samu a cikin shekaru 8 da ya yi yana gwamna. Batun rabon kuɗaɗen wata-wata ga Jihohin dai ya zama abun muhawara a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa? Gwamna Yusuf Ya Aike Da Sunayen Kwamishinoni Zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano “A yau zan iya bugun ƙirjina kuma kowanne daga cikin gwamnonin nan zai iya tabbatar da cewa, rabon da ake bai wa jihohin ya ninka sau uku, kuma akwai l isassun kuɗaɗe daga ƙananan hukumomi.” in ji Ganduje Da yake...
Kamaru Kasar Kamaru tana da alaka sosai da Isra’ila. Daraktan fannin tsaro na Cibiyar Nazarin Tsaron Kasashen Afirka da tsare-tsare a Geneba, Dabid Otto ya ce Isra’ila na kallon Kamaru a matsayin daya daga cikin kawayenta na kusa a Afirka. Ya ce “Kamaru ba za ta yi gangancin lalata alakar diflomasiyya da ke tsakaninta da Isra’ila ba.” Ya ce alakarsu na da kwari sosai, kuma ya shafi batu ne na tsaro. “Isra’ila ta taimaka sosai kuma tana ci gaba da taimakawa wajen kare gwamnatin Kamaru,” in ji shi. Isra’ila ta bayar da horo, kuma ana da amannar cewa tana ci gaba da bai wa dakaru na musamman na Kamaru horo, wani abu da ke tabbatar da tsaron shugaban kasar....
Birnin Taicang dake lardin Jiangsu na kasar Sin birni ne da ake kiran shi da sunan birnin kamfanonin kasar Jamus a kasar Sin, domin kamfanonin kasar Jamus fiye da 560 suna aiwatar da harkokinsu a wurin, ciki har da kamfanoni fiye da 60 da suka fi samun ci gaba a wasu kananan fannoni. Watakila wadannan kamfanoni ba su yi girma ko yin suna sosai ba, amma sun zama matsayin gaba a duniya a matakan wasu kananan fannoni, me ya sa Sin ta jawo hankalinsu sosai? Shugaban reshen kamfanin Knorr-Bremse AG dake kasar Sin Bi Guanghong ya yi bayanin cewa, masana’antun kasar Sin sun zama matsayin farko a duniya, kana babu bukatar kashe kudi da yawa, da daidaita matsaloli cikin sauri,...
Yawan ribar da manyan kamfanoni na kasar Sin suke samu ta karu da kashi 0.9 cikin 100 a mizanin shekara-shekara a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2025, lamarin da ya farfado da raguwar da aka samu da kashi 1.7 cikin 100 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a yau Asabar. Jimillar ribar da kamfanonin da ke samun makudan kudin shiga na kasuwanci a shekara na akalla yuan miliyan 20 (kimanin dalar Amurka miliyan 2.81) ta kai kusan yuan tiriliyan 4.7 a cikin watannin takwas, a cewar hukumar kididdiga ta kasar Sin. A cikin watan Agusta, ribar da manyan kamfanonin suka samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 20.4 cikin 100 a...
Tabbas, ko a zamanin yau ma, aikin raya tattalin arziki ba ya rabuwa da wahalhalu. Misali, a cikin gidajen da ake kiwon jatan lande, dole ne mutane su jure yanayi mai zafi da ya kan kai sama da digiri 40 na ma’aunin Celcius, da kuma tarin sauro dake cizon mutum. Har ila yau, akwai wasu kifayen da ake kiwonsu, misali Mullet, wadanda mazauna yankin Xinjiang ba su saba da cinsu ba, don haka ana bukatar karin kokari a fannin tallarsu a kasuwa.Duk da haka, lokacin da ake magana kan makomar harkokinsu, masu samar da kayan noma na Alar suna cike da kwarin gwiwa. Wani mai kiwon kifi ya bayyana cewa, “Bisa fasahar noman abincin ruwa da muka bunkasa a...
“Daga baya kuma sai ta fada cikin lamarin yin Takalma, sai dai abin ban takaici, ba tada isassun kudaden da za su taimaka mata don sabuwar harkar yin Takalma sana’ar da tasa kanta. Tana fatan idan ta samu isassun kudade, za ta sake komawa harkar.” Miss Oforbiike ta kara yin bayanin ta hadu da abubuwan takaici, an maida ta wata ba kome ba, sai bakaken maganganu da ta fuskanta lokacin da take tafiyar da harkar. Mista Celab Ogodo ya ce ‘Ina samun kudade da yawa ta hanyar tuka KekeNapep fiye da ma’aikatan gwamnati’ Ya kammmala karatunsa ne daga Kwalejin ilimi ta Jihar Ebonyi, ya ce shi bai dauki aikinsa kamar wanda bai dace ba, domin kullum yana samun Naira 15,000...
Tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka bisa jagorancin Adam Smith ta kammala ziyara a kasar Sin a jiya Alhamis 25 ga wannan wata, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun maida hankali sosai kan batun. Kafin ziyarar tawagar, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun zanta ta wayar tarho, da yin musayar ra’ayoyi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da batutuwan da suke sa lura tare, kana sun tsara taswira kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kama a mataki na gaba. Bisa wannan yanayi, ziyarar tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka ta shaida muhimmiyar rawar manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara, da ci gaba da karfafa mu’amalar dake tsakanin...
A Karo Na Hudu ’Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Sun Yi Nasarar Kammala Ayyukansu A Wajen Kumbon
Rahotanni daga ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ’yan sama jannati a sararin samaniya na kasar Sin, sun ce da misalin karfe 1 da minti 35 na sanyin safiyar yau Jumma’a 26 ga wata, bisa hadin-gwiwar dan sama jannati Chen Dong dake cikin kumbo, sauran ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 guda biyu, wato Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da ayyuka har na tsawon sa’o’i 6 a wajen kumbon, inda suka kammala ayyukansu bisa shiri. Ya zuwa yanzu, Chen da Wang sun riga sun koma sashin gwaje-gwaje na Wentian lami lafiya, al’amarin da ya shaida babbar nasarar da suka samu wajen gudanar da ayyuka a wajen kumbon. Yayin da suke wajen kumbon, ’yan sama jannatin biyu sun...
A yayin da shugabanni da wakilan gwamnatocin kasashe ke ci gaba da jawabi a babban zauren MDD, firaministan Isra’ila shi ma ya gabatar da nasa jawabi da yammacin yau, saidai ya ci karo da ihu da kuma ficewa daga zauren daga wasu wakilan kasashe dake zamne a zauren. Jakadun kasashen Musulmi, Larabawa, Afrika da Latin Amurka ne suka ficewa, sannan wasu daga Turai suka bi su. Amurka ce da wasu kawayenta daga yankin Pacific, da wasu kasashen kalilan ne suka rage a zauren. An kuma rawaito yin zanga zanga a birnin New York ta goyan bayan falasdinu da kuma neman kawo karshen yakin Gaza. Netanyahu ya kwashe sama da mintina 45 yana jawabi inda ya tabo batutuwa da dama, a...
Reform ya kuma ce yana shirin hana wani wanda ba dan Biritaniya ba damar samun walwala. Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa shirin nasu zai yi tanadin fam biliyan 234 cikin shekaru da dama. Chancella Rachel Reebes ta ce tanadin da aka ba da shawarar “ba shi da tushe a zahiri” kuma tuni gwamnati ta fara duban hana walwalar bakin haure. Jagoran kawo sauyi a Burtaniya, Nigel Farage, ya ce bai kamata Birtaniya ta zama “bankin abinci na duniya ba”. Da yake kaddamar da sabbin manufofin, Farage ya ce: “Ba a gare mu ba ne mu bane a ce mutane na shigowa daga ko’ina cikin duniya.” A karkashin tsarin na yanzu, bakin haure na iya neman izinin zama na dindindin bayan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga nan sai ya jaddada aniyar Sin, ta ci gaba da goyon bayan matsayi da ikon MDD, tare da mara baya ga sassan kasa da kasa wajen cimma nasarar amfani da dandalin MDDr a matsayin fagen karfafa shawarwari da hadin gwiwa, da tsare-tsare da aiwatar da matakai yadda ya kamata. Haka kuma, a yayin zantawarsa da shugabar taron MDD karo 80 Annalena Baerbock, a gefen babban taron muhawarar majalissar dake gudana a halin yanzu, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin na goyon bayan gina MDD mai karin inganci da hangen nesa, ta hanyar gudanar da sauye-sauyen kyautata karko da nagartar ayyukanta. Ya kuma bayyana kakkarfan goyon bayan Sin ga ikon MDD, da rawar da take takawa a...
Idan aka zo batun “salon zamanantarwa irin na kasar Sin”, za ku so ku ji shin: Takamaime wace irin hanya ce wannan? Me ya bambanta ta da zamanantarwa irin ta sauran kasashe a duniya? A gaskiya dai, fahimtar salon zamanantarwa irin na Sin babu sarkakiya a ciki. Tana nan lullube a cikin harkokin yau da kullum na jama’ar kasar Sin, da ma alakar da ke tsakanin wannan kasar da sassan duniya. Salon zamanantarwa irin na kasar Sin wani tsarin zamanantarwa ne na dimbin jama’a, da zamanantar da samun wadata ta bai-daya domin daukacin al’umma, da zamanantar da tsarin dunkulewar kayayyaki da ruhin wayewar kai, da zamanantar da zaman lumana tsakanin mutum da dabi’ar halitta, da kuma zamanantar da bin hanyar...
Ya ce zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya zai tabbata ne kawai idan aka tabbatar da adalci. Shugaban ya jaddada irin gyare-gyaren tattalin arziƙin Nijeriya, ciki har da cire tallafin man fetur da sauya dokokin musayar kuɗi. Ya ce matakan suna da tsauri, amma dole ne a ɗauke su domin samar da ci gaba mai ɗorewa. A kan tsaro, Tinubu ya ce yaƙin da ta’addanci ba wai da bindiga kaɗai ake cin nasara ba, sai da ra’ayoyi da ɗabi’u waɗanda ke haɗa al’umma. Ya kuma jaddada aniyar Nijeriya ga zaman lafiya, ci gaba, da kare haƙƙin ɗan Adam, inda ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta yi canje-canjen da za a iya gani, tare da gargaɗin cewa idan...
Masu kula da jirgin ruwan agaji na keta killace Gaza ( Sumudu) sun sanar da samun gargadi daga kasashen duniya da dama akan cea Isra’ila tana shirin kai musu hari. Jiragen ruwan dake son kawo karshen killace sun kai 50, suna kuma dauke da kayan agaji HKI ta aike da jiragen sama marasa matuki wadanda suke yin shawagi na tsokana a samansu da kuma watsa musu wasu sanadarori masu guba. A jiya da dare jiragen ruwan su ka bar gabar ruwan ‘ Girka su ka shiga iyakokin ruwan kasa da kasa da zai nausa ya nufi gabar ruwan Gaza. A gefe daya, ministan tsaron kasar Italiya Guido Crosetto ya bayyana cewa kasarsa za ta aike da jirgin yaki na biyu...
Gwamnatin jihar Sokoto ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen inganta fannin kiwon lafiya a jihar. Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Idris Mohamed Gobir ya bayyana cewa yayin da ya karbi bakuncin sabuwar wakiliyar Unicef ta kasa Mrs Wafaa Sa’eed da ta kai ziyarar fahimtar da jihar. Alhaji Idris Gobir ya ce a kan haka ne bangaren ke samun mafi yawan kasafin kudi tun hawan gwamnatin mai ci. A wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai (Mataimakin Gwamnan) Garba Muhammed ya raba wa manema labarai, Mataimakin Gwamnan ya ce manufar ita ce a tabbatar da cewa mutane suna samun ayyukan kiwon lafiya cikin sauki. Ya kuma nuna jin dadinsa da tallafin daban-daban da gwamnatin...
Akalla yara miliyan 4.8 ne ake shirin yi wa allurar rigakafin cutar kyanda da cutar shan inna a jihar Katsina a wani bangare na shirin allurar riga-kafi da aka shirya yi a wata mai zuwa. Shugabar ofishin kula da kananan yara ta UNICEF, Rahama Farah, ce ta sanar da hakan a wani taron tattaunawa da wayar da kan masu ruwa da tsaki a shafukan sada zumunta da aka gudanar a Katsina a wani bangare na shirye-shiryen rigakafin da ke tafe. Ya bayyana cewa za a yi allurar rigakafin cutar kyanda ga yara ‘yan tsakanin watanni 9 zuwa 14 yayin da za a yi allurar rigakafin cutar shan inna ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar. Mista Farah...
A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci hada karfi da karfe wajen gina yankin Xinjiang ya zama mafi kyau a cikin tsarin zamanantar da kasar Sin. Ya bukaci hakan ne yayin da ya gana da wakilai daga dukkan kabilu da sauran fannonin rayuwar al’umma a yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na arewa maso yammacin kasar Sin. Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya isa birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang da safiyar yau, domin halartar bukukuwan cika shekaru 70 da kafuwar yankin. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Gavi dai ba zai dawo ba sai a farkon shekarar 2026, shekarar da ake ganin kasar Sifaniya za ta kasance cikin kasashen da suka fi damar lashe gasar cin kofin duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da kuma Canada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau talata da yamma ce aka yi jana’izar shahidan Bintijbail na kudancin kasar Lebanon, wanda HKI ta kaisu ga shahada a lokacinda ta cilla makamai masu linzami kan motar da take dauke da su a ranar Lahadin da ta gabata. Tashar talabijin ta Al-Manar ta kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa, shahidan mutane 5 biyar ne wadanda suka hada da kananan yara 3 da mahaifinsu da kuma sannan mahaifiyarsu ta ji Rauni mai tsanani, da kuma yar’uwassu wacce itama ta ji Rauni. Almanar ta nakalto cewa shahadar da kuma kissan kiyashin bai karawa mutanen garin ba sai karfin giwa na riko da kasarsu da kuma gwagwarmayansu. Ministan kiwon lafiya Rakan Nasiruddeen tare da rakiyar minister watsa labarai Paul mahaifiyar yaran...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa dandalin jawabi a MDD wata dama ce ta kasashen duniya su bayyana ra’ayinsu kuma Iran zata bayyana ra’ayinta a gobe Laraba 23 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2025. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka jim kadan fafin ya shiga jirgi zuwa birnin NewYork a safiyar yau talata. Ya ce duniya a halin yanzu tana fuskantar danniya da babakere na wasu tsirarun kasashe a duniya. Sannan gaskiya mai dacin da ke faruwa a halin yanzu shi yadda yara da jarirai da suke mutuwa a gaza, a kisan kiyashin da HKI take aiwatarwa a Gaza kimani shekaru 2 da suka gabata. Sannan yayi allawadai da...
Haka kuma sun tabbatar da cewa manoma da suka koma gonakinsu kwanan nan sun samu kariya. Babu wanda aka sace ko ɗaya, yayin da jama’ar yankin ke ci gaba da zama lafiya. A ranar 19 ga watan Satumba, Birigediya Janar Ugochukwu Unachukwu, wanda shi ne muƙaddashin kwamandan rundunar sojojin 7 Division, ya kai ziyara Banki don yaba wa sojoji kan jarumtar da suka nuna. Ya ce ‘yan ta’addan sun yi mummunan rashi kuma ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar sojojin Nijeriya za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi. Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa wani soja ya rasa ransa yayin kare mutanen, yayin da wasu suka ji rauni. Sojojin sun ce wannan shaida ce ta jajircewar rundunar...
A daidai lokacin da aka shiga cikin kwanaki na 718 da fara yakin Gaza, HKI tana ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da makamai da kuma yunwa. Majiyar Falasdinawa ta tabbatar da cewa daga safiyar yau Talata zuwa tsakiyar ranaFalasdinawa masu yawa sun yi shahada. Majiyar dai ta ce, jiragen yakin ‘yan sahayoniyar sun kai hare-hare akan wani gida da yake a gabar ruwa a yammacin Gaza. Haka nan kuma da safiyar yau Talata din sojojin HKI sun kai hari da manyan bindigogi a yankin arewacin birnin Gaza. Wasu yankunan da HKI ta kai wa hare-haren sun hada titin Umar Mukhtar a tsohon garin birin Gaza. A unguwar Tal-hawa ma sojojin mamayar sun kai wasu hare-hare akan gidajen...
An ba shi kyautar ne a daren ranar Litinin a Theatre du Chatelet da ke birnin Paris, inda ya doke matashin Barcelona, Lamine Yamal, wanda ya lashe kyautar matashin ɗan wasa mafi ƙwazo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mohammad Eslami mataimakin shugaban kasar Iran kuma shugaban hukumar makamashin nukiliya na kasar Iran ya bayyana cewa Tehran da mosko za su rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya akwanaki masu zuwa ta gina tashar nukiliya domin kara fadada alakarsu a wannan bangaren na makamashi. Wannan sanarwar tana zuwa ne adaidai lokacin da iran ke fuskantar matsin lamba kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya ,bayan da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta kasa tabuka komai akan batun. Karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakani, kasar rasha za ta samar da riaktors guda 8 a cikin iran, hudu daga cikinsu za’a yi amfani da su a tashar ta ta bushahar ne. Yace an kammala komai game da Tattaunawa da...
29. Florian Wirtz (Liverpool) 28. Virgil van Dijk (Liverpool) 27. Declan Rice (Arsenal) 26. Erling Haaland (Man City) 25. Denzel Dumfries (Inter Milan) 24. Fabian Ruiz (PSG) 23. Jude Bellingham (Real Madrid) 22. Alexis Mac Allister (Liverpool) 21. Serhou Guirassy (Borussia Dortmund) 20. Lautaro Martinez (Inter Milan) 19. Joao Neves (PSG) 18. Scott McTominay (Napoli) 17. Robert Lewandowski (Fc Barcelona) 16. Vinicius Jr (Real Madrid) 15. Viktor Gyokeres (Arsenal) 14. Desire Doue (PSG) 13. Harry Kane (Bayern Munchen) 12. Kvicha Kvaratskhelia (PSG) 11. Pedri Gonzalez (Fc Barcelona) 10. Nuno Mendes (PSG) 9. Gigio Donnarumma (Man City) 8. Cole...
Dangane da halin da ake ciki game da rikicin Falasdinu da Isra’ila, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, karfin soja ba zai iya samar da zaman lafiya ba, kuma tashin hankali ba zai iya samar da tsaro ba. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen ci gaba da jajircewa a kan tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, da kuma matukar nuna goyon baya ga tabbatar da adalci ga al’ummar Falasdinawa wajen maido da hakkinsu na kasa, da kuma kara azamar warware matsalar Falasdinu tun da wuri ta hanyar samar da cikakkiyar mafita, mai adalci...
Na hudu, an yi ta samu ci gaban sayayya sakamakon masu yawon bude ido daga ketare. Bisa ga manufar rage haraji lokacin barin kasa da kasar Sin ke gudanarwa, an shirya shirin “Sayayya a Sin” yadda ya kamata, wanda hakan ya canza fa’idar yawan baki daga ketare da suke yawon shakatawa a kasar zuwa habaka kudin da ake kashewa. (Bilkisu Xin) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya. Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa. Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin. An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin...
Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Duk wani sabon kuskuren lissafin makiya zai fuskanci mayar da martani mai muni A cikin wata sanarwa da suka fitar a farkon makon tsaro mai alfarma, na ranar tunawa da arangama da gwamnatin Saddam ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a tsakanin shekarun 1980-1988, dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun jaddada cewa: Duk wani sabon kuskuren lissafi da makiya za su yi, za su fuskanci mummunan martani da zai zame babban darasi a gare su. A cikin bayanin da suka yi na farkon makon tsaro na dakarun IRGC sun bayyana cewa: A hakikanin gaskiya makon tsaro, biki ne na nasarar gwagwarmayar jama’a, kuma abin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata cuta mai cin naman jikin dan’Adam ta yi sandin mutuwar mutum takwas yayin da wasu fiye da 60 suke kwance a asibiti a garin Malabu dake Karamar Hukumar Fufure ta Jihar Adamawa. Wannan lamari dai ya jefa fargaba a zukatan mazauna yankin. NAJERIYA A YAU: Ayyukan Da Fasahar AI Za Ta Raba Mutane Da Su Nan Ba Da Jimawa Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi bincike a kan yadda wannan cuta take yaduwa da matakan da ya kamata a dauka don kauce wa kamuwa da ita. Domin sauke shirin, latsa nan
“A wani ɓangare na wannan dubarar, jam’iyyar a ƙarƙashin kulawar ɗaya daga cikin manyan ma’aikatan gwamnati, ta yi ƙoƙarin shirya zaɓen jagoranci ƙungiyar Musulmai ƴ an asalin Jihar Filato a cibiyar Azi Nyako da ke Dadin-Kowa a garin Jos, wanda daga bayanan da aka samu lamarin ya kasa samun nasara. “PDP na ganin cewa da wannan dubarar na raba kan Musulmin Jihar Filato za ta iya samun nasara a zaɓen 2027, wanda wannan ka iya kawo rashin jituwa da haɗin kan al’umma, musamman a irin wannan lokaci da ake fama da rikice-rikice addini da ƙabilanci da kuma ayyukan ƴ an ta’adda, wanda hakan bai kamata a siyasantar da addini ba. “Yadda PDP ke amfani da addini a matsayin hanyar lashe...
A yau Lahadi 21 ga wannan wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka da Adam Smith ya jagoranta a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. A yayin ganawar, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Amurka manyan kasashe ne dake da muhimmanci sosai a duniya, kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka mai dorewa yadda ya kamata ya dace da moriyar kasashen biyu da begen kasa da kasa. Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen girmama juna, da zama tare cikin lumana, da yin hadin gwiwar samun moriyar juna. Kana kasar Sin tana son kasar Amurka ta yi hadin gwiwa tare da ita don sa...
Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Wang Yong ya bayyana cewa, kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwa da dukkan bangarori a muhimman fannoni kamar na masana’antu. Wang, wanda shi ne mataimakin shugaban babban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wacce take babbar hukumar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen bikin bude taron masana’antun duniya na shekarar 2025 da aka gudanar a lardin Anhui da ke gabashin kasar Sin. Wang ya kara da cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa, sun bi ka’idar samun moriyar juna...
Duk tawagar da ta ƙare a mataki na ɗaya daga kowane rukuni guda tara na nahiyar Afirka, ita ce za ta samu gurbi kai-tsaye. Daga baya sai a zaɓo huɗu mafiya ƙoƙari da suka ƙare a mataki na 2, inda za a fitar da ɗaya daga cikinsu sannan ta kara da takwararta ta wata nahiyar. Rabon da Nijeriya ta samu gurbin Kofin Duniya tun a 2018 da aka yi a Rasha, inda ta gaza zuwa na 2022 a Ƙatar wanda tawagar ƴ anwasan ƙasar Argentina ta lashe ƙarƙashin jagorancin Lionel Messi. Jimilla Nijeriya ta je gasar Kofin Duniya sau shida a tarihi – 1994, 1998, 2002, 2010, 2014, 2018. A wasannin neman gurbin na gasar 2026, wasanni biyu kacal Nijeriya...
“Sanarwar jan hankaki – Taron bogi ‘convocation’ a Nijeriya – Jami’ar ba ta ba Dauda Kahutu Rarara digirin girmamawa ba”. A yau (Lahadi) ne aka sanar da Jami’ar EAU labarin wani biki da kafafen yada labarai na Nijeriya suka rahoto ƙaryar cewa, Jami’ar ta gudanar da wani taro a ranar Asabar a Hotel din ‘NICON Luxury’ Abuja, Nijeriya. Jami’ar ba ta ba da izinin gudanar da wani taro a wannan wuri a ranar ba, kuma an shirya wannan taron ne ta hanyar damfara ba tare da sanin ko izinin Jami’ar ba. Waɗanda suka shirya wannan taron sun yaudari wasu da yardar cewa suna wakiltar Jami’ar EAU, amma wannan gaba ɗaya ƙarya ce kuma ba su da ikon yin...
Shugaban kasar Iran Masud pezishkiyan ya bayyana cewa Iran ba za ta mika wuya ga bukatun da suka wuce kima ba, kuma za ta iya shawo kan duk wani takunkumi da aka kakaba mata, Shugaban ya fadi haka ne a wajen bukin karrama yan kasar da suka samu lambobin yabo a gasar Olympic ta kimiyya ta duniya , bayan da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kada kuriar amincewa da kudurin dawo da takunkumi dake da alaka da shirinta na nukiliya. Haka zalika shugaban kasar yace makiya suna iya kai hari kan sakamakon binciken fasaha da aka yi, amma kwararru da masana ilimin kimiya wadanda suka samar da wadannan naurorin su ne hakikanin gaskiyar dukiya ga kasarmu, don haka...
Ya ce Morocco, ta sha alwashin zurfafa hadin gwiwa tare da Sin, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, da fadada musaya a fannoni irinsu yawon bude ido, da ilimi, da al’adu, da ci gaba da yayata kawance bisa matsayin koli tsakanin kasashen biyu. A daya bangaren kuma, Morocco na maraba, da kuma goyon bayan shawarar inganta tsarin shugabancin duniya da Sin ta gabatar. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata mata ta haifi jarirai huɗu — maza biyu da mata biyu — a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Kiwon Lafiya (FUHSTHA) da ke Azare, a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025. Sakataren yaɗa labarai na asibitin, Abdu Mohammed, ya shaida wa Aminiya cewa Malama Hauwa ta haifi yaran ne ta hanyar tiyata, kuma tana ci gaba da jinya tare da ’yan huɗun. A washegarin haihuwar, Hajiya Halima Garba, matar shugaban asibitin (CMD), ta ziyarci mai jegon tare da mijinta da manyan ma’aikatan asibitin. Ta taya iyalan murna tare da addu’ar samun lafiya cikin gaggawa. ’Yan bindiga sun kashe basarake, sun tarwatsa mutane a Sakkwato Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi Kamar yadda ta...
Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona al’aurar ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona farjin ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata, wadda ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai mummunan rauni ta hanyar ƙona mata al’aura da wuka mai zafi a garin Magama Gumau, ƙaramar hukumar Toro. Rahotanni sun ce matar ta zargi yarinyar da maita, lamarin da ya sa ta yi amfani da wuka da aka zafafata a wuta wajen ƙona jikinta. Ihun yarinyar ne ya jawo hankalin maƙwabta, inda suka yi gaggawar zuwa suka ceceta tare da sanar da ‘yansanda. Gwamnan Bauchi Ya Gargaɗi Magoya Bayan Wike A PDP An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi Wani mai fafutukar kare haƙƙin yara a yankin, Kabiru Mohammed Abdulkadir, ya...
Najeriya ta tabbatar da shirinta na karɓar Wasannin Kungiyar Kasashen Renon Ingila na 2030, inda za ta zama ƙasar Afirka ta farko da za ta kafa wannan tarihi tun 1930. Shugaba Bola Tinubu, ta bakin Shugaban Ma’aikatansa Femi Gbajabiamila, ya ce gwamnati ta ba da cikakken goyon baya, ta kuma shirya samar da dukkan abubuwan more rayuwa, tsaro da masauki kafin lokaci. A jawabansu daban daban, Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa Shehu Dikko da Shugaban Kungiyar Wasannin Renon Ingila Habu Gumel, sun bayyana cewa Najeriya ce damar Afirka mafi cancanta, yayin da kwamitin neman karɓar gasar ya gabatar da shirin gudanar da wasanni 15, ciki har da kwallon ƙafa. Najeriya da Indiya ne ke neman karɓar gasar, inda za a...
Kazalika, masu sukar na ganin cewa, gwamnatin ta yi watsi da irin halin ƙuncin rayuwa da musamman talakwan ƙasar, ke ci gaba da fuskanta, kamar dai, na ci gaba da hauhawan farashin kayan masarufi da ƙarin kuɗin Man Fetur da ƙarin kuɗin wutar lantarki da ƙarancin albashin da ake biyan ma’aikata, musamman na gwamnati, wanda a baya, ta yi alƙawarin lalubo masu da mafita. Wannan batun na ƙarin albashin, tamkar dai wani cin zarafi wanda kuma abu ne, da ke tattare da hatsari. Kusan tun lokacin da shugaba Bola Tinubu, ya ɗare Karagar shugabancin ƙasar, ya rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa, na gudanar da mulki, inda gwamtainsa, ta rage yawan ɗimbin tawagar da take kwasa, na yin tafiye-tafiye, musamman...
Kotun ta kuma samu Musa da mallakar harsashi na musamman har guda 34 mai nauyin (7.62mm) ba bisa ƙa’ida ba. Ga laifin kisan kai, sashe na 220 na kundin laifuffuka da kuma hukuncin da ke karkashin sashe na 221, Musa an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. A laifi na biyu na mallakar harsasai ba bisa ka’ida ba, sashe na 8 (1) na dokar bindigogi, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari. Bugu da ƙari, an kore shi daga aikin sojan Nijeriya acikin ƙasƙanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Bayanai na cewa, wannan munduwa mai ɗimbin tarihi, mallakin Fir’auna Amenemope ne, yayin da ta yi ɓatan-dabo a gidan tarihin da ake adana da ita. An rarraba hoton munduwar zinarin ga jami’an da ke aiki a kan iyakokin ƙasar daban-daban da suka haɗa da filayen jiragen sama da tashohin jiragen ruwa da zummar daƙile fasaƙaurinta zuwa ƙetare. ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu An kama sojan bogi da ɓarayin mota 2 a Jigawa Munduwar mai ɗauke da ado na musamman, na da matuƙar daraja tun zamanin Fir’aunan, yayin da ake danganta ta da tsofaffin gumakan da aka yi bautar su a can baya, sannan an ce tana da ƙarfin warkarwa. Munduwar na cikin jerin kayayyakin...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar alhininsa kan asarar rayuka da aka yi a gobarar da ta tashi a ranar Talata a Afriland Towers da ke Broad Street, a Legas. A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma hukumomi da ma’aikatan hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS), United Capital, United Bank for Africa (UBA) Plc, da kuma Afriland Properties Limited. Ya kuma jajanta wa wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan bala’in, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa. Shugaba Tinubu ya yaba da matakin da hukumomin gaggawa...
Ya jaddada cewa dakarun tsaron Nijeriya suna da ƙarfin da za su iya fatattakar ’yan ta’adda, amma abin da ya rage shi ne samun ingantaccen shugabanci da ƙwarin gwiwa daga fadar shugaban ƙasa. Atiku ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai domin ceto ƙasar nan, inda ya bayyana cewa dawo da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziƙi ya kamata su zama fifiko. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau ne Gwamna Siminalaye Fubara ke dawowa kujerarsa a matsayin gwamnan Jihar Ribas bayan dakatarwa da ayyana dokar ta baci na watanni shidda da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar. Manazarta dai na hasashen wannan dawowar zata bude wani sabon babi a siyasar jihar Ribas. NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Yayin da wasu ke ganin gwamna Fubara zai koma bakin aiki ne ya cigaba da gudanar da mulkin jihar kamar yadda ya barta, wasu kuwa gani sukeyi akwai babban kalubale dake gaban gwamnan. Domin sauke shirin, latsa nan
Har kullum, Sin za ta ci gaba da martaba ka’idojin kare hakkokin kamfanoninta. Duba da cewa manhajar TikTok ta shafe tsawon shekaru tana aiki a Amurka, ta kuma samar da dumbin ayyukan yi ga tarin Amurkawa, tare da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar, ya kamata gwamnatin kasar ta baiwa manhajar damar cin gajiya daidai da sauran makamantanta dake kasar. Kamar dai ko da yaushe, burin Sin shi ne wanzar da daidaito da cimma moriyar bai daya tare da Amurka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ce, fiye da Falasdinawa 35 ne su ka yi shahada daga Safiyar yau Laraba zuwa tsakiyar rana,sanadiyyar hare-haren da HKI take kai wa. Hakan tana faruwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta yi gargadi akan cewa asibitocin yankin sun kusa daina aiki baki daya. Tashar talabijin din ‘aljazira’ ta kasar Qatar ta ce,adadin wadanda su ka yi shahada har zuwa marecen yau sun kai 51,38 daga cikinsu a cikin birnin Gaza kadai. A gefe daya rahoton tashar talbijin din ta ‘aljazira’ ya bayyana cewa; HKI ta yanke hanyoyin sadarrwa na “Internet’ a fadin Gaza, haka nan kuma ta hana hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) shigar da makamashi...
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta. Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo “Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa....
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan. An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa. Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai. An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni. Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi. Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani. Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa. NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai. Domin sauke shirin, latsa nan
Yadda kasashen yammacin duniya suka ki sauke nauyin dake wuyansu, ya danne wa kasashe masu tasowa hakkinsu. Misali, a lokacin da ake samun bazuwar annobar COVID-19, dimbin kasashen yamma sun yi ajiyar alluran rigakafi a gida, inda suka hana fitar da su zuwa ketare, da musayar fasahohi masu nasaba da su. Sai dai a lokacin, hukumomi masu kula da harkokin kasa da kasa, kamar su Hukumar Lafiya ta Duniya, da Majalisar Dinkin Duniya dukkansu sun kasa tilasta musu sauya manufofinsu. Wannan tsarin kasa da kasa, idan mun bar shi haka ba tare da wani sauyi ba, to, wata rana za mu ga an koma tsarin zalunci na zamanin mulkin mallaka, wanda zai yi barazana ga hakkin rayuwa, da raya kai...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Saudiyya na iya taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Gwamnatin sahayoniyya ba za ta kuskura ta kai hari ko kai wa wata kasa ta Musulunci hari ba matukar kasashen musulmi suka hade kansu; kuma Saudiyya za ta iya taka muhimmiyar rawa a tafarkin hadin kan kasashen musulmi. A yayin ganawarsa da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman a gefen taron Doha, Pezeshkian ya bayyana jin dadinsa da yadda dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ke kara bunkasa, yana mai cewa: Zurfafa da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Iran da Saudiyya zai kare muradun kasashen biyu, da kuma muradun al’ummomin kasashen biyu,...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce: Laifin da Isra’ila ta yi na kashe ‘yan jaridun Yemen babban ta’addanci ne Kungiyar kare hakkin bil’ adama ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya suka kai a ranar 26 ga watan Satumba kan ‘yan jaridun kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan jarida sama da 30, laifi ne da ba za a iya kubutar da girman laifin kan wanda ya aikata ba. A cikin rahoton baya-bayan nan, kungiyar ta fitar ta bayyana cewa, ta tattara bayanan harin da makiya yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a ranar 10 ga watan Satumba kan hedkwatar kafafen yada labarai a kasar Yemen, kuma ta yi la’akari da wannan...
JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata . Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa wannan shi ne nasara ta wasannan kasa-da kasa har guda 6 wadanda Iran take samun lambobin zakara a cikinsu a wannan shekarar. Labarin ya kara da cewa yan damben Iran sun sami wannan nasarar kwana guda kafin a kammala gasar. An bayyana nasarar da yan damben Iran suka samu ne a jiya Litinin da yamma a birnin Zagreb inda aka gudanar da gasar. Sun sami lambobin...
Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur. Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki. Har ila yau, ya ce an biya bashin da ya haura biliyan bakwai, ciki har da miliyan 800 da ake bin jiragen saman Nijeriya. Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yanzu jihohi na iya biyan albashi da fansho a kan lokaci, sannan suna da rarar kuɗi don ayyukan raya ƙasa, abin da ba a saba gani ba a baya. “Bayan shekara biyu da watanni biyar kacal a ofis, Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama....
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar
“Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo. Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
Bikin hada-hadar ba da hidima na Sin wato CIFTIS na bana da ya kare a jiya a nan Beijing ya jawo hankalin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 85 da suka gudanar da baje koli da tarurruka, kusan kamfanoni 500, ciki hadda wasu daga cikin manyan kamfanoni 500 dake sahun gaba a duniya da manyan kamfanoni masu jagorantar bangarorinsu, sun halarci bikin, kuma an cimma nasara a fannoni sama da 900. A yayin da duniya ke fuskantar rashin tabbas, bikin CIFTIS ya karfafa mu’amala da kuma samun riba da juna. Alkaluma na nuna cewa, a shekara ta 2024, jimillar cinikin ba da hidima na Sin ya fara wuce dala tiriliyan 1 a karon farko, wanda ya zama sabon tarihi, kuma...
Shugabgan kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gana da fira ministan kasar Iraqi Muahmad Shi’a Sudani a taron Doha na kasashen musulmi ya bayyana cewa; Wajibi ne kasashen musulmi su hada kai idan har suna son kawo karshen laifukan da HKI take tafkawa. Bugu da kari, shugaban kasar ta Iran ya kuma tattaunwa wasu hanyoyin da ya kamata a yi aiki da su, matukar ana son kawo karshen ta’addancin ‘yan sahayoniya. Shugaba Fizishkiyan ya kuma ce, laifukan da HKI take tafkawa akan fararen hula a Gaza, da kashe yara da mata ta hanyar yunwa, wani lamari ne da hankali bai iya daukarsa, kuma idan musulmi su ka hada hannu da karfe wuri daya za su kawo karshensa. A nashi gefen...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya. Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11. Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu. NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku A kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari. Domin sauke shirin, latsa nan
Sunana Hafsat Sa’eed daga Jihar Naija: Ni dai a tawa fahimtar mata masu yin hakan manya ne, waɗanda sun riga sun yi aure, su ma mazan su suke zuwa da wannan ‘interest’ ɗin. Wasu kuma da yanayi na rayuwa, wasu suna da ‘ya’ya, da ‘yan’uwa, wasu ba suda abin yi. To, rashin abin yin nan wataran ya kan jaho hakan, mace ta zauna ta yi soyayyar ƙarya sabodƙ kuɗi dan ta taimaki kanta, da ‘yan’uwanta da ‘ya’yanta. Kamar yadda su mazan yanzu ba sa iya bayar da kuɗin sai a soyayyar ƙarya, ba wani abu ne yake janyo hakan ba face rashin abin yi duk wanda yake da abun yi ba zai zauna kwaɗayi da soyayyar ƙarya ba. To,...
Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila. Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da suke buga gasar Premier League ta bana. Ƙungiyoyin da suka ci riba; LIVERPOOL Ƙungiyar ce kan gaba a yawan kashe kuɗi wajen sayen ƴan ƙwallo a bana, wadda karo biyu ta ɗauki ƴan wasa a matakin mafi tsada a kakar nan. Ta fara da sayen matashin ɗan wasa Florian Wirtz kan fam miliyan 115, sannan ta ɗauki Aleɗander Isak kan fam miliyan 125 ranar da...
Misali, ya sauya lokacin da aka tsara yin wasan sada zumunta da ƴan ƙasa da shekara 20 na ƙungiyar Flamengo a lokacin da Leɓerkusen ta je atisaye a Brazil. An buga wasan kwana biyar kafin ranar da aka tsara tun farko, inda Leɓerkusen ta sha kashi da ci 5-1. Haka nan a kusan wannan lokacin ne Ten Hag ya yanke hukunci kan batun tafiyar Granit Ɗhaka, inda ya ce ya kamata ya tsaye saboda Leɓerkusen ta rasa manyan ƴan wasa da yawa. Sai dai tuni ƙungiyar ta sanar cewa Ɗhaka zai iya tafiya idan aka samu tayi mai kyau. Daga baya ya tafi Sunderland. Haka nan kuma Ten Hag ya soki ƴan wasansa tare da cewa ba su da kuzarin...
A yau Asabar aka kaddamar da tashar watsa labarai ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ta Sichuan, tare da kaddamar da wasu jerin ayyuka na CMG din a Chengdu babban birnin lardin Sichuan. Daraktan CMG Shen Haixiong ya halarci taron, inda a ciki jawabinsa ya ce kafar CMG za ta kara lalubo albarkatun dake bangarorin al’adu da yawon bude ido na Sichuan, da gabatar da kyawun al’adun Bashu da karfafa aikin sadarwa cikin ci gaba mai inganci na lardin Sichuan. Har ila yau, an kaddamar da cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasahohin bidiyo na ultra HD da na daukar murya da dakin gwaje gwajen ayyukan watsa labarai na kasa a birnin na Chengdu. (Mai fassara: Fa’iza...
Sanarwar ta ƙara da cewa, SABER wani shiri ne na shekaru biyar, wanda ya dogara da aiki, wanda Bankin Funiya ke tallafawa, wanda aka tsara shi cikin tsanaki domin wargaza shingayen faɗuwar jari, da zaburar da sana’o’i masu zaman kansu, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa ga al’ummar Zamfara. Za a raba Naira 150,000 ga mutum 2,000 a faɗin jihar domin tallafa wa ƙananan sana’o’i. Bugu da ƙari, mutane 1,000 a ƙanana da matsakaitan sana’o’i za su karbi Naira 500,000 kowanne. Haka kuma, mutane 60 daga matsakaita da manyan ‘yan kasuwa za su ci gajiyar tallafin Naira miliyan biyar kowannen su. A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, SABER ba wani abu ba ne na yau...
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
A yayin da suka yi alƙawarin yin adawa da aiwatar da harajin, ƙungiyar ta ƙara da cewa: “Yajin aiki na kan tebur idan gwamnati ta yi ƙoƙarin watsi da wannan gargaɗi ta ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofi. Don haka, TUC ta umarci dukkan kwamitocin jihohi, rassan ƙungiya, da tsarin ta a faɗin ƙasa da su kasance cikin shiri, sanya ido, kuma su jira ƙarin sanarwa wanda zai iya kai wa ga ɗaukar mataki mai ƙarfi idan gwamnati ta ƙi sauraron muradin jama’a.” Ƙungiyar ta kuma kira ga abokan hulɗarta – ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin ƙwararru, ɗalibai, ƙungiyoyin kasuwa, shugabannin addini da duk ƴan Nijeriya masu kishin ƙasa – da su tsaya tare da ita a wannan gwagwarmaya. “Tare,...
Al’amari mai rikitarwa Hakikanin gaskiya ya fi an rikitarwa. Bisa al’amari, ana kiyasta cewa mutane kimanin 15,000 zuwa 20,000 ne suka mutu a sakamakon kashe-kashen da suka shafi ‘yan bindiga da ta’addanci a Arewa maso Yamma kaai cikin shekaru 10 da suka wuce. Wannan adadi yana daidai da yawan rayukan da aka rasa a Yakin Kosobo, ko kusan kashi 40 cikin ari na asarar rayuka a Yakin Basasar Saliyo na tsawon shekaru 10, duk da cewa ba gwamnati ba bace ke yakar ‘yan bindiga, sai dai ‘yan ta’adda ne masu zaman kansu. Wannan kididdigar ba ta bayyana irin wahalar da dubban yara ke sha ba, waanda aka kashe iyayensu, gidaje marasa uwa ko masoya, mutane da suka ji rauni...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk shekara rayuka da dukiyoyi na kara salwanta sakamakon ambaliyar ruwa. Duk da jan kunne da hukumomi a matakai daban-daban keyi, rayukan mutane da dukiyoyi na kara salwanta. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan rayukan da suka salwanta a damunan wannan shekarar. Domin sauke shirin, latsa nan
Haka zalika, Ministan Ilimi, Dakta Olatunji Alausa , shi ma ya jinjinawa rawar da Gwamna Sani ya taka wajen sauƙaƙa bikin kaddamar da Cibiyar Horar da Sana’o’i da Kwarewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar, yana mai cewa yanzu haka ana sake fasalin makarantun fasaha na ƙasa baki ɗaya domin su mai da hankali kacokan kan darussa masu amfani da tasiri. Shettima ya bukaci mambobin NCS da su hada kai bayan wani tsari guda na juyin-juya halin Nijeriya, yana mai gargadin cewa “ba za mu iya gina ma’aikata da za su yi shiri a nan gaba kan tushen rarraba.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Za a kuma ƙaddamar da sabon shiri, Nigeria@65 Compendium, wanda zai zayyano ci gaban ƙasa a fannoni kamar shugabanci, tattalin arziƙi, da ci gaban ƙasa a tsawon shekarun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shaidu sun ce yawancin ‘yan kasuwar sun gudu cikin daji, domin tsira da rayukansu. Maharan sun kashe sojoji biyar da ‘yan kasuwa kusan 10. Al’ummar sun roƙi gwamnati a matakan ƙananan hukumomin, jiha da tarayya su tallafa musu wajen tsaro, ilimi, lafiya, da samar da hanyoyi. Kakakin sojojin, Kyaftin David Adewusi, ya ce bai san da labarin harin ba amma zai yi bayani daga baya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya isa kasar tunisiya domin tattaunawa da hukumomin kasar, a ci gaba da ziyarar da yake yi a yammacin Afrika, bayan da ya bar kasar masar inda ya gana da directan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya kuma suka cimma matsaya tsakaninsu, An tsara cewa babban jami’in diplomasiyar na iran zai gana da ministan harkokin wajen kasar inda za su tattauna game da dangantar dake tsakanin kasashensu, da ma na kasa da kasa, A wani sako da ya aike da shi a shafin sa na X Araqchi ya nuna jin dadinsa sosai da kuma jinjinawa ga gwamnatin kasar masar game da rawar da ta taka a bangaren diplomasiya...
“Wannan matakin ya zama dole don dakatar da saran gandun daji, kare muhalli, da tabbatar da ɗorewar albarkatun ƙasa,” in ji Dokta Hashim. Ya yi gargaɗin cewa, duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri. “Za a tsaurara doka, tare da biyan tarar ₦500,000 da kuma yiwuwar ɗauri a gidan yari saboda amfani da injin sare bishiya ba tare da izini ba, da kuma tarar ₦250,000 kan kowace bishiya da aka sare ba bisa ka’ida ba. “Haka kuma za a umurci waɗanda suka aikata laifin da su sake dasa bishiyar sannan kuma za a ƙwace injin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza A matsayin martani ga kuri’ar raba gardama kan halaccin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza da ake zalunta, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i ya ba da izini na addini na fitar da wani kaso na kudaden Khumusi don haka. A cikin cikakken labarin, a baya-bayan nan ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ba da izini na addini na ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Falastinu da ake zalunta a Gaza. Ga rubutun tambaya da amsar, kamar yadda gidan yanar gizon KHAMENEI.IR ya...