Aminiya:
2025-09-17@20:29:57 GMT

Hilda Baci ta kafa tarihin dafa shinkafa buhu 200 a tukunya guda

Published: 13th, September 2025 GMT

Chef Hilda Baci mai shekara 28 ta kama hanyar kafa sabon tarihin girka shinkafa dafa-duka (Jollof) ’yar Najeriya mafi yawa a duniya.

Hilda Baci ta kafa wannan sabon tarihi ne inda ta girka shinkafa basmati buhu 200 a wata katafariyar tukunya a bainar jama’a.

Ta yi wannan sabon abin bajinta ce shekara biyu kacal bayan ta shiga kundin tarihi na duniya na Guinness a matsayin wadda ta shafe awanni mafiya yawa tana girke-girke a duniya.

A ranar Juma’a ta fara girkin a otel ɗin Eko Hotel & Suites, da ke Legas, kuma sama da mutum 20,000 mashahurai da sauransu sun yi rajista don halarta.

An kama buhun tabar wiwi 150 bayan hatsarin mota a Kano Abba ya tarbi tagwayen da aka raba da juna bayan yi musu tiyata a Saudiyya

Girman tukunyar da aka ƙera musamman domin wannan girki mai cike da tarihi ya kai murabba’in mita 6×6 (faɗi da tsawo), kuma taba iya ɗaukar lita 22,619.

Da farko Hilda ta shirya amfani da buhu 250 (kilogiram 5,000) na shinkafa samfurin basmati. Amma saboda matsalolin awon kayan, sai aka rage zuwa bubu 100 (kilogiram 4,000).

Kafin fara girkin a ranar Juma’a, Hilda Ta rubuta a shafinta na Inatagram cewa, wannan ƙoƙarin ba a fatar baka ba ne kawai, amma “tarihi ne a keɓaɓɓe,” ta ƙara da cewa duk wanda ya halarci taron zai ci abincin da aka girka kyauta.”

A bidiyo da aka gani kafin lokacin, an ga Hilda da mahaifiyarta suna addu’a a wajen gaban katafariyar tukunyar.

An kuma gan ta ta hau tukunyar don ta wanke ta da kanta. Ta ƙara da cewa, “E, zan iya tabbatar da cewa wannan tukunya tana da tsabfta sosai. Na naɗe hannuwana na wanke ta da kaina,” kamar yadda ya rubuta a Instagram.

Ta yi alƙawarin cewa abincin zai kasance “mafi kyau, mai tsafta da za ka taɓa ci a rayuwarka.”

Shirye-shiryen girkin

Tukunyar an ƙera ta musamman a yankin Kudu maso Yamma, kuma aikin ya ɗauki kusan wata uku.

Samun kayan ya ɗauki kusan wata biyu, haɗawa da gwaji kuwa wata ɗaya.

Shinkafar za ta ƙara yawa bayan ta nuna, zuwa kimanin kilogiram 14,000–16,000, kuma za ta wadatar da wa dubban mutane.

Hilda ta ce za ta yi amfani da ilimin lissafi da lura wajen daidaita kayan miya da kayan ƙamshi da sauran kayan haɗi a girkin. 

Kayan haɗi

Kayan haɗin girkin sun haɗa da kilogiram 1,000 na tumatir, albasa kilogram 600, kilogram 750 na man girki.

Sai kuma kayan ƙamshi irin su barkono (fresh cayenne pepper), paprika, thyme, basil, tafarnuwa, citta da sauran su.

An kuma sanya naman talotalo da sauransu don ƙarin ɗanɗano.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027.

Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta.

Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo

“Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa. Wannan yana nuna cewa ba sa son a samu hamayya a lokacin zaɓe,” in ji shi.

Galadima ya kuma yi gargadi kan shirin nada wani da ya kira mai lam’a a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin rudani.

“Ina fatan ba gaskiya ba ne, domin idan wannan mutumin ya zama shugaban INEC, ka tabbata cewa wannan gwamnati na neman tayar da yaƙin basasa,” in ji shi.

Sai dai bai ambaci sunan mutumin ba.

Dangane da batun fara yaƙin neman zaɓe da wuri da wasu jam’iyyu ke yi, Buba Galadima ya zargi INEC da gazawa wajen aiwatar da tanade-tanaden dokokin zaɓe.

“Wannan batun fara yaƙin neman zaɓe kafin INEC ta ba da izini, gwamnatin da ke kan mulki ce ta fara shi. Wannan yana nuna cewa INEC ba za ta iya zama mai adalci a irin wannan yanayin siyasa da muke ciki ba,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna
  • Tarihin Ƴan Majalisar Farko Kafin Da Kuma Zamanin Mulkin Mallaka (3)
  • Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana