Pezeshkian zai halarci taron kasashen musulmi da Larabawa a Doha kan Isra’ila
Published: 13th, September 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai halarci babban taron kasashen musulmi da na Larabawa da za a yi a Doha a ranakun Lahadi da Litinin, taron da Qatar ta kira domin samar da tallafi ga Falasdinawa a Gaza da kuma mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai kan babban birnin kasar a ranar 9 ga watan nan kan kasar ta Qatar.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce zasu halarci taron yana mai cewa shi da shugaban kasar za su gabatar da jawabai.
“Lokaci ya yi da za a yi aiki, kuma kalmomi kadai ba su isa ba,” in ji shi yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na IRIB a yammacin ranar Alhamis, yana mai jaddada cewa dole ne taron ya wuce maganganu.
Taron dai na zuwa ne bayan da Isra’ila ta kai wani hari da makami mai linzami kan birnin Doha a ranar Talatar da ta gabata, kan wasu manyan shugabannin Hamas.
Harin, wanda ya kasance na farko da Isra’ila ta kai kan kasar Qatar, kasanshen duniya sun yi tir da Allah wadai da shi..
Firaministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani ya fada a wata hira da CNN cewa taron zai tabbatar da matakin da za a dauka na gaba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Turkiyya ta yi tir da harin da Isra’ila ta kai Qatar September 13, 2025 Sharhin Bayan Labarai: Qatar Zata Sauya Amurka A Matsayin Abokiyar Tsaron September 13, 2025 Gaza : Adadin shahidai A kisan kare dangi na Isra’ila ya kai 64,756 September 13, 2025 Unicef : Yara na cikin ukuba sanadin shingen Isra’ila a Gaza September 13, 2025 Araqchi: Babu Dalilin Jin Tsoron Tattaunawa September 12, 2025 Welayati: Abin Kunya Ne Yadda Duniya Ta Yi Shiru Kan Laifukan Isra’ila September 12, 2025 Ayatullah Khatami Ya Ja Hankalin Kasashen Larabawa Kan Hare-Haren Isra’ila September 12, 2025 Gaza: Falastinawa 48 Suka Yi Shahada A Hare-Haren Isra’ila September 12, 2025 Jagororin Hamas Sun Kubuta Daga Kisan Gillar Isra’ila Ne A Lokacin Da Suka Tafi Yin Sallah September 12, 2025 Qatar : shugabannin Isra’ila na kishirwar jefa duniya cikin rikici September 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da Isra ila ta kai
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan : Kasashen duniya na Allah wadai da cin zarafi a lokacin kama El-Fasher
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa garin El-Fasher da ke Darfur a ranar Alhamis, da kuma mummunan tasirin da ya yi ga fararen hula.
A cikin sanarwar da ya fitar, kwamitin ya nuna matukar damuwarsa game da karuwar tashin hankalin da ke faruwa a El-Fasher da kewaye, wanda Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta kwace iko da shi kwanan nan, kuma ya yi Allah wadai da ta’addancin da ake zargin dakarun RSF sun yi wa fararen hula, ciki har da kisan gilla da tsare mutane ba bisa ka’ida ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ta “firgita da rahotannin kisan sama da marasa lafiya 460 da abokan aikinsu a asibitin haihuwa na El-Fasher a Sudan.”
A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Laraba a shafukan sada zumunta, Janar Hemedti ya amince cewa sojojinsa sun aikata cin zarafi.
Da yake magana daga wani wuri da ba a bayyana ba, janar din, sanye da kayan soja, cewa “Na lura da keta haddi a El-Fasher,” inda ya sanar da kafa kwamitin bincike nan take.
Ya yi alƙawarin cewa za a kama duk wani soja da aka samu da laifin cin zarafi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bukaci bangarorin da su hanzarta shiga tattaunawa a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
kungiyar likitocin Sudan, ta ce “Adadin wadanda suka mutu ya wuce 2,000 a cikin kwanaki biyu na farko bayan da RSF ta shiga El-Fasher.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100 October 30, 2025 Amurka Ta Hana Marubuci Dan Nigeria Wole Soyinka Izinin Shiga Amurka October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci