2025-11-08@15:41:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 111
«yaƙin neman zaɓe»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ƙaramin Ministan Gidaje da Tsara Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana cewa ɗan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a Zaɓen 2023 Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara. Sai dai Ministan ya ce ƙaddarar hukunci daga Allah ne ya sanya a yanzu haka ba shi ke riƙe da madafan iko a Jihar Kanon ba. Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Ata ya faɗi hakan ne yayin da yake barazanar ficewa daga jam’iyyar APC muddin ake sake naɗa Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na Jihar Kano. Ministan ya ce kalaman da shugaban jam’iyyar ya riƙa furtawa su ne dalilin da Allah Ya ƙwace mulkin jihar...
Wannan bayanin da Babangida ya yi a kan zaɓen ya haifar da maganganu a kan irin rawar da Abacha ya taka wajen soke zaɓen da yadda ya hana Nijeriya komawa mulkin dimokuraɗiyya a wancan lokacin. Marigayi Sani Abacha dai ya yi mulkin soja a Nijeriya daga shekara ta 1993 zuwa 1998 da ya rasu.
Jam’iyyar PDP mai ci a Jihar Osun ta lashe zaɓen dukkan kujerun ƙananan hukumomi jihar guda 30 da na kansiloli 332 da aka gudanar yau Asabar. Shugaban hukumar zaɓen jihar OSSIEC, Hashim Abioye ne ya sanar da sakamakon a wani taron ganawa da manema labarai da ya yi a jihar. Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines Da yake jawabi a yammacin wannan Asabar ɗin a birnin Osogbo, Hashim Abioye ya ce an samu nasarar gudanar da zaɓen bisa duk wasu tsare-tsare da dokoki suka tanadar. Ya bayyana cewa jam’iyyu 18 ne suka shiga zaɓen domin cike giɓin da ake da shi a madafan iko na ƙananan hukumomin...
Sadiq S. Abacha, ɗan Tsohon Shugaban Mulkin Soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya bayyana mahaifinsa s matsayin mutum mai nagarta duk da sukar da ake yi masa har yanzu. A wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Sadiq, ya ce an jima ana cin amanar mahaifinsa, amma tarihi zai yanke masa hukunci ta hanyar yin adalci. Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa “Mutumin nan Abacha—kullum sukarsa da cin amanarsa kuke yi a asirce. Tarihi zai tuna ka a matsayin shugaba nagari, ko da kuwa sun ci gaba da ƙoƙarin rage maka ƙima. “A matsayina na ɗanka, yau na fi alfahari da kai. Lallai kai...
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo, ya zargi malaman addini da neman ƙwace lamurran siyasar Najeriya daga hannun ’yan siyasa. Sule Lamiɗo ya nuna damuwa bisa yadda malaman addini ke ƙara shiga harkokin siyasa, inda ya ce, a halin yanzu malaman suna yin tasiri sosai a yanayin tafiyar siyasa da kuma jefa ƙuri’a. Ya bayyana haka ne a yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum, bisa rasuwar babban ɗansa a Jihar Kaduna. A cikin bidiyon ta’aziyyar, an ji Sule Lamiɗo, yana cewa, malaman addini sun yi wa ’yan siyasa ƙwace, inda suke fitowa fili suna yi wa ’yan takara yaƙin neman zaɓe, tare da kiran mabiyansu su zaɓi wanda su suke goyon baya....
Kamar yadda doka ta tanada cewar duk wata ƙaramar hukumar a tabbatar da cewa zaɓaɓɓun shugabanni ne ke jagorancin ta. Wannan ya sa Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Raɗɗa ta shirya aiwatar da zaɓen ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin jahar wanda hakan zai ƙara ba su damar cin gashin kan su kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar. Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Shugaban Ƙungiyar Afenifere, Adebanjo ya rasu Kamar yadda shugaban Hukumar zaɓen mai zaman kanta ta Jihar Alhaji Lawal Alhassan Faskari ya shaidawa manema labarai a lokacin da ake rarraba kayan zaɓen zuwa ƙananan hukumomin jihar ya ce, tuni hukumar zaɓen ta kammala duk wasu shirye-shirye don...
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara. Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro. Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato. Dakarun rundunar Tsatsa Daji III, sun kuma ƙwato tarin makamai a yankin bayan ’yan ta’addann sun cika bujensu da iska. ’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai ’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a Kano Sojojin sun yi wannan nasara ne a yayin samamen da suka kai bayan samun bayanan sirri, inda daga bisani suka karasa zuwa mafakar ’yan ta’addan...
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara. Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro. Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato. Dakarun rundunar Tsatsa Daji III, sun kuma ƙwato tarin makamai a yankin bayan ’yan ta’addann sun cika bujensu da iska. ’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai ’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a Kano Sojojin sun yi wannan nasara ne a yayin samamen da suka kai bayan samun bayanan sirri, inda daga bisani suka karasa zuwa mafakar ’yan ta’addan...
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas. Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na X cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuradiyya a Najeriya. Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke kira ga haɗin kai domin fuskantar zaɓen 2027. A watan Oktoban 2024, jam’iyyar APC a Jihar Osun ya dakatar da Aregbesola bisa zargin cin amanar jam’iyya da sukar shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamnan...
Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa Farfesa Ignatius Uduk hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari kan laifin sauya sakamakon zaɓe. An gurfanar da Farfesan kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da gazawa wajen aiwatar da aikinsa, sauya sakamakon zaɓe, da kuma yin rantsuwar ƙarya a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe. Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Lamarin ya shafi zaɓen ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a Essien Udim a shekarar 2019. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Bassey Nkanang ya same shi da laifin sauya sakamakon zaɓe da yin rantsuwa bisa ƙarya. Hakan ya sa alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara uku...
Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun ce sun ƙwato tarin makamai a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda na Jihar Zamfara. Dakarun tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (DSS), sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan masu safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya. Tankar mai ta sake fashewa a Neja Jadawalin Gasar AFCON 2025 da za a fafata a Morocco Wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce sun ƙaddamar da farmaki ranar 27 ga watan Janairun 2025, abin da ya kai ga ƙwato makaman kan hanyar Namoda zuwa Zurmi. Ya ce waɗanda ake zargin sun tsere zuwa cikin daji tare da barin motarsu bayan artabu da sojoji. Kanal Abubakar ya...
