2025-09-17@23:12:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1113
«sojojin Rasha»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ya ƙara da cewa jama’a na shiga ADC saboda suna ganin ita ce mafita. “Gazawar gwamnatin APC ta tilasta mutane su nemi mafita, kuma ADC za ta bayar da wannan damar,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya. A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina. An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa, shekaru arau-aru. Mahaya dawaki da sauran mahalarta bikin daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje da mazauna garin Daura sun fara tururuwa zuwa filin bikin, wanda zai samu. An kuma shirya gudanar da gagarumin hawan daba a Fadar Sarkin Daura, albarkacin zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na 10. A wannan ranar ake cika shekara 10 da fara wannan gagarumin biki,...
A duk ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ake bukukuwan zagayowar Ranar Hausa ta Duniya. An fara wannan biki ne tun a shekarar 2015, inda wani tsohon ma’aikacin sashen Hausa na BBC kuma ma’aikacin TRT Hausa a yanzu, Abdulbaƙi Jari Aliyu ya ƙirƙiro tare da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta. An ɓullo da ranar ce domin haɗa kan masu magana da harshen Hausa a faɗin duniya da nufin magance matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya. Da farko dai, an fara bikin wannan rana ce kamar wasa a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta amfani da kalmar #RanarHausa. Zuwa shekara ta 2018 kuma aka fara yin bikin a zahiri tare da gudanar da tarurruka...
Na yi imani babu rayuwa ba tare da harshe ba, domin duk wata al’umma tana da buƙatar harshe domin gudanar da rubuce-rubuce, kimiyya da fasaha. Amma an yi sakaci da nazarin harshen Hausa, duk da cewa yana cikin manyan harsunan duniya masu ƙarfi da adabi. Don haka zan fara bayyana matsalolin, sannan in kawo shawarwari. Matsala ta farko: Sai Bango Ya Tsage… Idan gwamnati da manyan al’umma ba su ɗauki Hausa da muhimmanci ba, ba zai samu ci gaba ba. An taɓa samun shugaban ƙasa da ya ce nazarin wasu darusa ɓata lokaci ne, amma shi kansa a lokacin yaƙin neman zaɓe da Hausa yake magana. Gwamnati ta nuna rashin kulawa da harshen Hausa, tana ganin ba shi da amfani....
Bikin ranar ba iya Nijeriya kawai ya tsaya ba. Ana gudanar da bikin a ƙasashe da dama irin su Ghana, Amurka, Turkiyya da kuma Dubai, inda al’ummar Hausawa ke yin rayuwa. A waɗannan wurare, ana shirya wasanni irin gargajiya kamar wasan Dambe, nuna abinci da kayayyakin al’adu, da kuma gudanar da taruka, tattaunawa kan harshen Hausa da tarihinsa. A Nijeriya, cibiyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu sukan shirya taruka da laccoci. A jami’o’i irin su Jami’ar Bayero ta Kano da sauransu, masana da ɗalibai su kan tattauna kan ci gaban Hausa a fannin kimiyya da fasaha, da kuma ƙirƙiro sababbin kalmomi da ke dacewa da zamani. Haka kuma, jama’a na amfani da wannan rana a kafafen sada zumunta domin wallafa...
“Mun yi tattaunawar gaskiya, amma gwamnati tana yi mana wasa,” in ji shi. Ya ce an yi watsi da rahotanni masu muhimmanci, an kafa manufofin da ke cutar da ilimi, sannan an jefa malaman da suka yi ritaya mummunan hali. “Wannan gwamnati ta raina ilimi da malamai. Mun gaji,” in ji shi. Shugaban ASUU ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki, za ta ɗauki alhakin duk wata matsala da za ta biyo baya. Ya kuma kira mambobin ASUU da su fito ƙwansu da kwarkwata wajen tarukan da za a gudanar a manyan jami’o’i a ranar Talata, 26 ga Agusta, 2025, yana mai cewa wannan shi ne mataki na farko da ƙungiyar za ta ɗauka don nuna rashin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Har ila yau, rahoton ya ce, matakin na Amurka muradu da dabarunta na siyasar duniya kadai yake karewa, yayin da take dogaro da karfin soja wajen haifar da tsaiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankuna da ma tsarin harkokin tekun na duniya. Bugu da kari, ya soki ayyukan Amurka yana cewa, sun saba doka, ba su kamata ba, kuma suna nuna fuskoki biyu. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya godewa kasar Rasha saboda goyon bayanta ga kasar kan hakkinta na tace makamashin uranium, musamman a taron kwamitin tsaron MDD wanda za’a gudanar nan gaba dangane da kudurin kwamatin mai lamba 2231 dangane shirin nukiyar kasar Iran ta JCPOA, Inda kasashen turai 3 wato triko wadanda suke bukatar sake dawoda takunkuman MDD kan kasar ta Iran. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakato Pezeshkiyan yana fadar haka a lokacinda yake magana ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putun a yau litinin. A nashi bangaren shugaba Putin ya bayyana cewa Rasha za ta tabbatar da cewa sakamakon taron kwamitin tsaro dangane da shirin “snapback” zai fito mai kyau ga kasar Iran....
Ya kuma yi gargadin cewa, “Wannan ba lokaci ba ne da Arewa za ta naɗe hannunta tana kallo yayin da al’amura ke ci gaba da taɓarɓarewa, lamarin tsaro yana kara ta’azzara yayin da ake ci gaba da kwashe albarkatun yankin, ambaliyar ruwa na ci gaba da barazana, dole ne mu tashi tsaye mu hada kai domin kare yankin.” Osuman ya koka da kashe-kashen da ake yi a Arewacin Nijeriya a kullum, yana mai jaddada cewa, babu yadda za a yi, a zura ido ana kallo. “Mun yi asarar yara, matasa maza da mata, da tsoffi saboda ambaliyar ruwa, bala’o’i, ‘yan bindiga da masu kwacen wayoyi, halin da ake ciki, akwai matukar damuwa, don haka nake kira da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an tsaron Najeriya sun yi awon gaba da Shugaban al’ummar Falasdinawa mazauna Najeriya, Abu Ramzi Ibrahim, a birnin Abuja Rahotanni sun suna jami’an tsaro sun kama Abu Ramzi Ibrahim me a gidansa da ke Abuja tun ranar Juma’a. Majiyoyi daga cikin al’ummar Falasɗinu sun ce Ibrahim, wanda dasn Bafalasɗine ne kuma ya yi karatu a jami’ar Najeriya, yana tsare har zuwa yanzu. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin Jakadan Falasɗinu da ke Najeriya amma hakarsa ta cin ma ruwa ba. Rushe Kasuwar Alaba Rabo: Mun yi asarar fiye da N20bn — ’Yan Arewa Yau Shugabannin Tsaron Afrika 54 ke taro a Abuja Ibrahim ya shahara wajen kare muradun Falasɗinawa ta kafafen yaɗa labarai, musamman a ’yan watannin nan da...
’Yan Arewa a Kasuwar Alaba Rago, shahararriyar kasuwar ’yan Arewa a Jihar Legas sun roki gwamnatin jihar ta biya su diyya kan asarar da suka yi sakamakon rushe kasuwar da gwamnati nta yi. Sun bayyana cewa asarar da suka tafka ta haura Naira biliyan 20 bayan Gwamnatin Legas ta rusa masallatai sama da 40 da shaguna kimanin 3,000 a Kasuwar wadda suka kafa shekara 45 da suka gabata a jihar. A karo na biyu a ’yan kwanakin nan mahukunta a Jihar Legas suka rushe sassa da dama na kasuwar, wadda ta yi fice da kasuwancin kayan abinci da dabbobi da karafa da sauran kayan masarufi, wacce Hausawa suka kafa a shekarar 1979. A cikin watan Mayun 2024, jami’an hukumar ’yan...
Dakarun Kai Daukin Gaggawa sun kai hari kan ƙungiyar ba da agaji ta Red Crescent a Kordofan da jirgin sama maras matuki ciki Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) sun kai hari kan tawagar kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Sudan (SRCS) a yankin Andaraba na jihar Kordofan ta Arewa, inda suka raunata masu aikin sa kai 10 tare da lalata motoci biyu na tawagar. Kwamishinan agajin jin kai na jihar, Mohamed Ismail, ya shaidawa Al Jazeera cewa, Dakarun kai daukin gaggawar sun kai harin bam kan tawagar kungiyar Red Crescent a Kordofan mai tazarar kilomita 70 yammacin jihar Khartoum da wani jirgin yaki maras matuki ciki. Ya kara da cewa, an kai harin ne...
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya tabbatar da cewa gobe Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025, ita ce za ta zama 1 ga watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugaban kwamitin kula da harkokin addini a majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda ya bayyana cewa ba a samu labarin ganin sabon wata na Rabi’ul Awwal a ranar Asabar, 29 ga Safar ba. Dangote ya ci gaba da zama attajiri mafi arziƙi a Afirka — Forbes An haramta bukukuwan aure a Taraba Farfesa Sambo wanda kuma shi ne Wazirin Sakkwato, ya ce saboda haka, Lahadi, 24 ga watan Agustan 2025, za ta zama 30 ga watan Safar, sannan kuma bisa...
Yakasai ya kawo misalin tattaunawa da aka yi da kamfanoni a kasar China lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje, inda aka kawo tawaga Kano don duba yiyuwar saka hannun jari amma rashin wutar lantarki ya kawo cikas, ganin cewa dokar gwamnatin tarayya a wancan lokaci ta hana jihohi samar da wutar lantarki ta kansu. Ya bayyana roƙo ga gwamnatin Kano ta yanzu da ta mayar da hankali wajen tabbatar da isasshiyar wutar lantarki, musamman ta hanyar wutar solar ko haɗin gwuiwa da manyan kamfanoni kamar Dangote da BlackRhino, don farfado da masana’antun jihar. A cewar Yakasai, damuwa mafi girma ita ce yadda albarkatun Arewa ake dauka zuwa wasu jihohin kudu don a sarrafa, daga bisani kuma a dawo da su a sayar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ‘Yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya faru a garin Kojiyo dake karamar hukumar Goronyo a jihar sakkwato sun samu kansu cikin damuwa. Yayin da kalilan daga cikin wadanda abun ya rutsa dasu suka tsira da ransu, wasu da dama sun mutu, a gefe guda kuma an kasa gano inda sauran da abun ya rutsa dasu suke. Wannan lamari ya tayar da hankulan jama’a, musamman ‘yan uwan waɗanda abin ya shafa, waɗanda yanzu ke cikin damuwa, jimami da rashin sanin makoma. NAJERIYA A YAU: Dalilan Karyewar Farashin Hatsi A Kasuwanni DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan...
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kebbi da al’ummar jihar bisa rasuwar Sarkin Zuru, Mai Martaba, Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (Gomo II). A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana rasuwar Sarkin a matsayin “babban rashi ga ƙasa,” inda ya tuno irin hidimar da marigayin ya yi a matsayinsa na tsohon gwamnan soja na Jihar Bauchi da kuma hidimarsa a matsayin basarake. Shugaba Tinubu ya lura cewa Najeriya za ta daɗe tana tuna gudummawar tsohon janar ɗin, wanda kuma ya yi yaƙi a matsayin ƙaramin hafsan soja lokacin Yaƙin Basasa. Shugaban ƙasa ya kuma yabawa jagorancin...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da rabon sabbin baburan hawa ga shugabannin jam’iyyar APC na mazabun kananan hukumomi 12 na shiyyar Jigawa ta Arewa maso yamma wadda Sanata Babangida Hussaini Kazaure ya bayar da kyauta. A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi ya yaba da kokarin Sanatan tare da shawartar shugabannin da suka sami ababan hawan da su yi amfani da su yadda ya kamata. A jawabin sa, Sanata Babangida Hussaini Kazaure ya ce ya bada baburan ne domin saukakawa shugabannin jam’iyya gudanar da ayyukan su cikin sauki. Ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa nasarorin da ya samu a shekaru biyu da ya yi akan karagar mulki. Usman Mohammed Zaria

Gwamnatin DR Kongo Ta Nuna Rashin Amincewarta Da Zabin Kenya Kan Wajen Da Zata Bude Karamin Ofishin Jakadancinta A Kasarta
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta ki amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta sanar da kin amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma da ke gabashin kasar, duba da matakin da ya saba wa ka’idojin diflomasiyya, duba da yadda Kongo ke ganin ci gaba da kasancewa a birnin na Goma ya saba ka’ida. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar din da ta gabata, mahukuntan kasar Kongo sun bayyana mamakinsu kan sanarwar da fadar shugaban kasar Kenya ta bayar na nadin Judi Kiara Nkumiri a matsayin karamin jakadanta a birnin Goma ba tare da amincewar ma’aikatar harkokin wajen Kongo ba. Sun dauki wannan a matsayin...
Dubban mutane a birnin London sun yi cincirindo a kofar shiga sansanin sojojin sama da ke arewa maso yammcin birnin London inda suke zargin gwamnatin kasar da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jiragen yakin F-35 na kasar Burtania suna shawagi a tekun medeteranin inda suke taimakawa HKI yakin da take fafatawa da Falasdinawa a Gaza. Don haka gwamnatin kasar tana da hannui a kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza. Tun cikin watan octoban shekara da 2023 mutane daga bangarori daban-daban a kasar Burtaniya suke zanga-zanga don neman a kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa a Gaza, sannan a bawa kasar falasdinu cikekken yanci bayan...
Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke kan hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan dogon lokacin da suka shafe ba tare da samun wutar lantarki ba. Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni da su kawo musu ɗauki cikin gaggawa. Tun a watan Ramadan Al’ummar sun bayyana cewa tun watan azumin Ramadan da ya gabata suke cikin duhu, sakamakon ƙonewar transforma da ke yankin, lamarin da ya bar su cikin ƙunci har tsawon watanni, da ke shafar rayuwar su ta yau da kullum. Wani daga cikin mazauna yankin, Muhammad Idris Gargajiga, ya bayyana cewa duk lokacin da suka kai ƙorafi ana gaya musu cewa yankin ba shi da rumfar zaɓe, abin da ya...
Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da yake amsa tambaya kan tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Iran da E3 (Faransa, Birtaniya da Jamus) a nan gaba, yayin da kuma an riga an gudanar da zama zagaye na biyu na masana da kwararru a matsayin sharar fage a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a karshen watan Yuli. “Yanzu, wadannan shawarwari za su ci gaba, mun yanke shawarar ci gaba, kuma za mu...
A yau Juma’a ne kasar Japan ta gudanar da gangamin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin duniya na biyu, sai dai yayin da yake jawabi albarkacin taron, firaministan kasar Shigeru Ishiba, bai tabo batu kan alhakin dake rataye a wuyan kasarsa ba, a matsayinta na wadda ta mamayi wasu kasashen nahiyar Asiya. A hannu guda kuma ya gabatar da addu’a ga wurin ibadar nan na Yasukuni, a matsayin girmmawa ga wurin ibadar da ake kallo a matsayin wurin da aka karrama mutanen da suka tafka danyen aiki yayin yakin duniya na biyu. Kazalika, wasu ministocin kasar sun kaiwa wurin ibadar na Yasukuni ziyarar girmamawa. Jerin wadannan matakai dai na shan suka, da adawa daga sassan kasa da kasa....
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu saurarozasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai dubi “ranar 40 na Imam Hussain(a) wanda ya fado a ranakun Alhamis ko jumman da suka gabata, a nan Iran da kuma Iraki, kowa da yadda suke yi lissan watan Safar a wajensu. Ranar 40 na Imam Hussain (a) ita ce ranar 20...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu saurarozasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai dubi “ranar 40 na Imam Hussain(a) wanda ya fado a ranakun Alhamis ko jumman da suka gabata, a nan Iran da kuma Iraki, kowa da yadda suke yi lissan watan Safar a wajensu. Ranar 40 na Imam Hussain (a) ita ce ranar 20...
Daga cikin wadannan alkaluman na yara miliyan 1.65 sun kasance suna a jihohin Zamfara, Bauchi, Sokoto, Borno, Kebbi, Kano, da kuma wadanda kuma suke a jihohin da Kungiyar ta MSF ke gudanar da ayyukanta kuma jihohin da ke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro. Bugu da kari, akasarin kungiyoyi, sun yi ittifakin cewa, batun kula da lafiya, abu ne, da ya kamata matan Gwamatin uku na kasar, su bayyana dokar ta baci a kai. Wannan rashin ayyana dokar ta bacin a fannin, mussaman a Arewacun Nijeriya, za a iya cewa, babbar gazawar rashin iya gudanar da shugabanci na gari ne, inda a Katsina irin wannan sakacin, mussaman na gazar samar wa yaran abinci mai gina jiki, ya bayyana karar...
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da miƙa wa mataimakinsa, Malam Faruk Jobe, ragamar mulkin jihar, inda shi kuma zai tafi hutun mako uku domin duba lafiyarsa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai fara ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025. An zabi sabuwar firaminista a Luthuania Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC A cewar Gwamna Radda, hutun zai ba shi damar samun kulawar likitoci da kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin koshin lafiya. “Cikin matakan da nake ɗauka don kula da lafiyata da kuma ganin na yi...
Shugaban ƙasar Lithuania, Gitanas Nauseda, ya zabi ’yar majalisa Inga Ruginiene ta jam’iyyar Social Democrat, a matsayin firaminista, bayan Gintautas Paluckas ya yi murabus sakamakon binciken rashawa da ake gudanarwa a kansa. Sai dai Ruginiene ta taba fuskantar suka kasancewar tana da alaka da ’yan uwa a Rasha, wadanda ta ziyarta a shekarun 2015 da 2018. Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC Tinubu ya cancanci yabo kan daidaita tattalin arzikin Nijeriya —Ngozi Sai dai ta ce yanzu daina kai musu ziyara, kuma ta jaddada cewa tun farko Ukraine take mara wa baya a yakin da take yi da Rasha, wadda ta kaiwa mamaya a 2022. Majalisar dokokin ƙasar za ta amince da nadinta tare da ministocinta kafin...
“Kowa ya sani wadatar abinci yana ɗaya daga cikin alamun da ke nuna kyautatawar tattalin arziki na ƙasa baki ɗaya, don haka ne muka himmatu wajen ba da namu gudunmawar ta wannan fannin.” Ya kara da cewa, an kafa gidauniyar ne domin taimakawa a ɓangaren kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki wanda rabon takin na daga cikin shirin gidauniyar na bunƙasa tattalin arziki, da kuma kyautata ci gaban al’umma. “Wannan shi ne karo na huɗu da wannan gidauniyar ta ke rabon taki duk shekara ga manoma masu ƙaramin ƙarfi da ba za su iya sayen takin a irin wannan lokacin da gona ke buƙata ba.” “An ware buhun taki guda 6,000 da za a rabar wa manoma masu...
Gwamnatin kasar Afirka ta kudu zata fara tattaunawar kasa dangane da talauci da kuma rashin adalci a rabon arziki a kasar. Gwamnatin kasar ta ware kimani dalar Amurka miliyon 40$ don gudanar da tattaunawar. Inda ake saran dukkan mutanen Afrika ta kudu suna da damar bayyana ra’ayinsu dangane da wadannan matsaloli. Na talauci da rashin adalci a rabon arzikin kasar. Ana fatan masana daga ciki da wajen kasar zasu gabatar da ra’ayinsu ta shafukan sadarwan da za’a samar a cikin taron. A halin yanzu fiye da shekaru 30 kenan da fita karkashin mulkin wariya na launin fata tsiraru a kasar, amma har yanzun kasar tana fama da matsalolin talauci, rashin aikin yi aikata laifuka da sauransu. Mutane da dama suna...
Al’ummar garin Talasse da ke Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe, sun ce sun gaji da rayuwa cikin duhu har na tsawon shekaru 19. Sun kuma bayyana takaicinsu bayan tsayawar aikin wutar lantarki da ya tsaya. Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe Aikin, wanda ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Billiri da Balanga, Ali Isa JC, ya fara tun farkon wannan shekara, ya sanya al’ummar yankin farin ciki bayan an kafa turakun wuta da na’urorin taransifoma. Sai dai cikin watanni biyu da suka gabata, aikin ya tsaya ba tare da wani bayani ba. “Yan siyasa su kan zo da alƙawura a lokacin zaɓe, sannan...

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Manufar Shugaba Trump Ta Korar Marasa Galihu
Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ya kuma nuna cewa, kaso 92 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na bayyana matukar damuwa game da tsaron rayukan al’ummun Amurka, yayin da kaso 81.7 bisa dari suka ce muggan laifuka, da karuwar masu kwana a kan tituna sun zamewa manyan biranen Amurka alakakai, lamarin da ya zamo cutar Amurka mai matukar wahalar magani. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tinubu ya yi kira da a sake duba kudaden gudanar da aikin NNPC da ake cire kashi 30 cikin 100 wanda doka ta tanadar a karkashin dokar masana’antar mai. Shugaban ya bayyana godiya ga mambobin majalisar bisa jajircewarsu da aiki tukuru wajen aiwatar da gyare-gyare masu tsauri da wahala wadanda suka dabaibaye ci gaban tattalin arzikin kasa a baya, amma a yanzu, za su karfafa kwarin gwiwar masu zuba jari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Gombe, mai wakiltar Nafada ta Kudu, Adamu A. Musa, ya zargi gwamnati da ‘yan majalisun jihar da kasa aiwatar da dokokin da suke zartarwa. Ya ce akwai dokar da aka zartar shekaru takwas da suka gabata domin yaƙi da fyaɗe da cin zarafin mata da yara, amma har yanzu ba a aiwatar da ita ba. Sojoji sun kashe babban Kwamandan ISWAP, Amirul Fiya a Borno Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki A cewarsa, majalisa tana yin doka sannan ta tura wa gwamna ya sanya hannu, amma daga baya a bar ta kamar ba ta da amfani. Ya yi gargaɗin cewa irin wannan sakaci yana ƙara wa masu aikata laifi ƙwarin guiwa...
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya saboda ɗaukar matasan da aka horar ƙarƙashin shirin GOSTEC aiki a matsayin cikakkun ma’aikata. Ya ce wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnati wajen taimaka wa matasa domin rage zaman banza da kuma ba su damar dogaro da kai. Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan Gwamnatin Gombe za ta ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13 Ya ƙara da cewa, yanzu wasu daga cikin matasan sun za su hidimata wa al’umma, saɓanin halin da suke ciki a baya. Ya roƙi matasan su zama masu gaskiya, riƙon amana da kishin ƙasa, inda ya bayyana cewa su ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. Ɗaya daga cikin...
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Rano, Alhaji Muhammad Naziru Ya’u, na tsawon watanni uku sakamakon zarge-zargen aikata ba daidai ba. An yanke wannan hukunci ne a zauren majalisa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan kwamitin majalisar kan ƙorafe-ƙorafe ya gabatar da rahoton bincikensa. Yayin gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin wanda shi ne shugaban masu rinjaye, Alhaji Lawan Hussaini Dala, ya ce binciken ya samo asali ne daga ƙorafin da kansiloli tara daga cikin goma na Rano suka sanya wa hannu. A cewarsa, ƙorafin ya zargi shugaban da yin sakacin kuɗi, sayar da shaguna, da karkatar da takin zamani da aka ware wa ƙaramar hukumar, tare da wasu zarge-zarge daban. Lawan ya bayyana...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a ɗakin taro na Majalisar da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja. Kafin a fara taron, Shugaban Ƙasa ya rantsar da Farfesa Dakas James Dakas da Dakta Uchenna Eugene a matsayin Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki ta Ƙasa da Kwamishina. Majalisar ta kuma dakatar da taron na minti ɗaya domin girmama marigayi Cif Audu Ogbe, wanda ya kasance memba a majalisar a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari, haka kuma a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Cif Ogbe ya rasu a ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, yana da shekaru 78. Daga Bello Wakili
Gwamnatin jihar Katsina ta ce shirye-shirye sun kankama domin bin sahun sauran sassan duniya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya a za ake gudanarwa ranar 26 ga watan Agustan kowacce shekara. Shugaban Hukumar Kula d Tarihi da Al’adu ta jihar, Dr Kabir Ali-Masanawa ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai a Katsina ranar Talata. Ya ce za a yi taron ne a Fadar Sarkin Daura da ke jihar, kuma ana sa ran manyan baki daga kasashe akalla 24 za su halarta. Masanawa ya ce wannan shi ne karo na farko da gwamnati ta shiga cikin shirya bikin, inda ya ce hatta Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ya tsaya tsayin daka wajen ganin bikin ya yi nasara....
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce, “Idan ba a zarge ni wajen binciken gwamnoni da ministocin jam’iyyar da ke mulki ba, bai kamata a zarge ni idan na binciki ’yan hamayya ba.” Duk da haka, mutane da dama a kafafen sada zumunta sun nuna shakku, tare da tambayar dalilin da ya sa EFCC ba ta ɗauki mataki kan manyan ’yan siyasa na jam’iyyar APC kamar tsohon Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa, tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ba. Wasu sun zargi EFCC da yin aiki ƙarƙashin ikon gwamnatin da ke mulki, yayin da wasu suka yi tsokaci ta hanyar buƙtar shugaban EFCC ya bayyana bayanan asusun bankinsa na yanzu. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke shirin tafiya wurin bauta a ranar Lahadi. “CLO ya je don ya tayar da shi daga barci amma sai ya gano cewa, ba ya numfashi, nan take ya kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yansanda ta Dambam,” in ji Wakil. Biyo bayan umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani Omolori-Aliyu, jami’in ‘yansanda na sashen ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin. An garzaya da Chukwuebuka...
Sai dai wasu daga cikin hadiman shugaban kamar Abdulaziz Abdulaziz, mai taimaka masa a kafafen watsa labaru, ya ce labarin ba gaskiya ba ne. Batun rashin lafiyar Tinubu ba sabon abu ne, domin tun yana yaƙin neman zaɓen takara a 2023 ake kai ruwa rana kan batun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce yaki da talauci muhimmin mataki ne na hanzarta ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Ya bayyana haka ne a lokacin shirin gwamnatin jihar mai taken “Gwamnati da Jama’a” wanda aka gudanar a karamar hukumar Ringim. Malam Umar Namadi ya jaddada muhimmancin horas da matasa sana’o’in hannu da samar da yanayin kasuwanci mai kyau domin cimma wadannan manufofi. Saboda haka, ya yi kira ga zababbun wakilai, masu rike da mukaman siyasa, shugabannin kasuwanci da sauran attajirai da su taimaka wa al’ummarsu domin kara bunkasa ci gaba da habaka tattalin arziki. A yayin taron, Kwamishinan jin kai da harkokin musamman na jihar, Auwal Danladi Sankara, ya raba naira miliyan 50...
Lee ya kara da cewa, fifikon musammam da Hong Kong ke da shi karkashin manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu’, ya ba yankin damar jan hankalin masu zuba jari na ketare domin su lalubo damarmakin kasuwanci a yankin da ma kasuwar babban yankin kasar Sin tare da taimakwa kamfanonin babban yankin shiga kasuwannin ketare. Bugu da kari, ya ce kamfanonin waje da dama sun samu damarmakin kasuwanci a Hong Kong, kuma suna ci gaba da fadada harkokinsu. Su ma kamfanonin babban yankin kasar Sin sun aminta da karfin Hong Kong kuma suna hada gwiwa da tawagar dake Hong Kong wajen lalubo damarmakin dake akwai a kasuwanni masu tasowa na ketare. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana...
Rikicin filin gona ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu biyu a ƙaramar hukumar Gulani da ke Jihar Yobe. Lamarin ya faru ne a daren Asabar bayan ce-ce-ku-ce tsakanin mazauna ƙauyukan Zango da Azere, waɗanda ke tsakanin iyakokin Gujba da Gulani. Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa shalƙwatar ƴansanda ta Bara ta samu kiran gaggawa daga shugaban ƙauyen Zango a ranar 9 ga Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na dare, inda ya sanar da cewa wasu ƴan daba daga ƙauyen Azere sun kai mummunan farmaki kan manoma. Gwamnatin Yobe Za Ta Yi Taron Girmama Ɗalibar Turanci Ta Duniya, Nafisa Abdullah Afam Osigwe Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar Lauyoyi Ta Kasa Wanda aka...
Ma’aikatar kula da albarkatun kasa ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, kasar ta kammala yin rajistar hakkin mallakar yankuna 5 na kare muhalli da halittu na kasar, a matsayin wani muhimmin mataki na daukaka aikin kare muhalli da halittu. Yankunan 5 na kasa sun hada da na Sanjiangyuan da na Giant Panda da yankin kare dabbar Tiger na arewa maso gabashin kasar wato the Northeast China Tiger da na kare Damisa da ake kira Leopard National Park da daji mai dumi da damshi na Hainan wato Hainan Tropical Rainforest da kuma yankin Wuyishan. Rajistar na bayyana ikon da matakai daban-daban na gwamnati ke da shi da bayyana hakkokin mallaka da aikin kula da yankunan da nauyin kula...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da haɗin gwiwar Gavi da ke taimakawa wajen samar da rigakafi, sun mika na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana g Gwamnatin Jihar Kano domin amfani da su a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) guda 28 da nufin ƙarfafa rigakafin yara da kuma kula da lafiyar jama’a. A yayin bikin mika kayayyakin ga gwamnatin jihar da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Kwamishinan Lafiya na Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce wannan shiri na nufin taimaka wa yaran da ba a musu rigakafi, da mata masu juna biyu da ba su da damar samun rigakafin yau da kullum da kuma wasu ayyukan...
’Yan ta’adda sun kashe mutum 24 tare da sace wasu akalla 144 a cikin mako guda a sassan Jihar Zamfara. Kungiyar Al’ummar Zamfara mai suna Zamfara Zamfara Circle Community Initiative ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai hare-haren da suka kai kan kauyuka 15 inda suka jikkata mutane 16 a kananan hukumomi daban-daban. Ta bayyana cewa daga ranar 4 zuwa 10 ga watan nan na Agusta, 2025 ’yan ta’adda suka kai hare haren; kauyukan da aka kai wa farmakin sun hada da Sabe, Tungar Yamma, Sauru, Lambasu, Dogon Madacci, Dankalgo, da Kwanar Kalgo a ƙaramar hukumar Bakura. A Karamar Hukumar Tsafe, hare-haren sun shafi Chediya, Kucheri, Yankuzo, da Katangar Gabas Bilbils. A Karamar hukumar Mafara, an samu rahoton hare-hare a...
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae shawara, wato Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewa Iran zata hana America samar da hanya a yankin Caucasus, ko da kasar rasha ta taimaka ko bata taimaka ba. A wata hira na musamman da kamfanin dillancin labaran Tasnim, Ali Akbara wailayati ya yi watsi da wani shiri wai shi zangezur wanda an tsara zai hana kasar Armenia da Nakhchivan. Da aka tambaye shi da maganar cewa Armenia zata bawa Amurka yankin haya na tsawon shekaru 99 masu zuwa, Wilayati ya bayyana cewa warin zai zama makabartan sojojin Donal trump, wannan ba hanya ce wanda Amurka ta mallaka ba. Ya ce gwamnatin kasar Iran ta sha bayyana cewa bata...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar. Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, dukkan ɗaliban aji na ƙarshe na makarantun sakandaren Larabci na gwamnati da suka amfana da wannan tallafi sun kammala rubuta jarabawar NBAIS makon da ya gabata, kuma suna jiran sakamakon. Ya ce wannan tallafi na daga cikin ɗawainiyar da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ke yi wajen taimaka wa ɗaliban aji na ƙarshe na sakandaren Larabci domin...
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin Rann, da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge, a Jihar Borno. A makon da ya gabata, dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun daƙile harin da Boko Haram suka kai garin Rann. Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi Sun kashe ’yan ta’adda da dama, duk da cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu sakamakon harba roka da ‘yan ta’addan suka yi. Rann na da iyaka da ƙasar Kamaru, kuma daga Maiduguri yana da nisa kusan kilomita 196. Bayanan jami’an tsaro sun tabbatar cewa Abu Nasr, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa...
Falasdinwa 11 suka rasa rayukansu a yau Asabar a Gaza saboda yunwa, wanda ya kawo adadin wadanda yunwa ta kasashe a Gaza tun lokacinda HKI ta hana shigowar abinci yankin zuwa 212. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar ma’aikatar kiwon lafiya na Gaza na fadar haka, sannan masana sun bayyana cewa mai yuwa wannan adadin ya wuce haka, saboda ita yunwa tana hana garkuwan jiki aiki, don haka karamin cuta tana iya kashe mutun saboda yunwa. Sun kara da cewa akwai wasu Falasdinawa da dama a wasu wurare a cikin gaza wadanda basa da lafiya amma yunwa ta karasa su a gida ba tare da sun zo asbiti ba. Larabarin ya kara da cewa a cikin...
Bayan da aka ɗaura auren, masoyanta da abokan aikinta suka tura mata saƙonni taya murna daga sassa daban-daban na Nijeriya. Wannan aure ya zo watanni kaɗan bayan rasuwar mahaifinta, wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta yi aure da masoyinta, Ibrahim Garba. An ɗaura auren a ranar Asabar a Masallacin da ke Unguwan Rimi, a Jihar Kaduna, bayan Ibrahim ya biya sadaki Naira 300,000. Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara Rahama, ta sanar da ɗaurin auren a shafinta na Facebook, inda ta gode wa Allah tare da neman addu’a daga masoyanta. Ta bayyana farin ciki da godiyarta, tare da fatan wannan sabon babi na rayuwarta zai kasance mai albarka. Auren mata na zuwa ne watanni biyu bayan rasuwar mahaifinta, Ibrahim Sadau. ’Yan uwanta sun yaɗa hotuna da bidiyon bikin a kafafen sada zumunta, inda...
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan noma daga 2015 zuwa 2019, Audu Ogbeh, ya rasu a ranar Asabar, 9 ga Agusta, yana da shekaru 78 a duniya, kamar yadda iyalinsa suka tabbatar. A cikin wata sanarwa, iyalan sun ce: “Ya rasu cikin kwanciyar hankali, ya bar mana gado na gaskiya, hidima da jajircewa ga kasa da al’umma. Mun sami kwanciyar hankali daga yadda ya shafi rayuka da kuma yadda ya kafa misali.” Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala Jihar Gombe Za Ta Rungumi Shirin Farfado Da Noman Auduga Na Gwamnatin Tarayya – Inuwa Iyalan sun bayyana cewa za a sanar da yadda za a...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, ta wayar tarho a yau Jumma’a 8 ga wata. A tattaunawarsu, Putin ya bayyana ra’ayin kasar Rasha dangane da rikicin Ukraine a halin yanzu, da yadda Rasha ta tuntubi Amurka kwanan nan, inda ya ce, Rasha ta yaba sosai da muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a fannin shawo kan rikici ta hanyar siyasa. A nasa bangaren kuma, Xi ya jaddada matsayin kasar Sin, tare da bayyana cewa babu wata dabara mai sauki da ke iya magance matsaloli masu sarkakiya. Ba tare da la’akari da duk wani sauyi da za a fuskanta ba, kasar Sin za ta tsaya ga neman sulhu da gudanar da shawarwari....
An shawarci sabbin mataimaka na musamman da su kasance masu adalci da gaskiya wajen aiwatar da ayyukansu a ƙaramar hukumar Auyo ta jihar Jigawa. Shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Alhaji Binyaminu Ahmad Adamu Kafur ne ya bayar da wannan shawara yayin bikin rantsar da sabbin mataimaka na musamman 69 da aka gudanar a Auyo. Alhaji Binyaminu Kafur ya sake tabbatar da kudirin majalisar wajen yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin samar da kayayyaki more rayuwa, don tabbatar da ganin kowa ya amfana da mulkin dimokuraɗiyya. Ya yi kira ga jama’a da kada su gaji wajen yin addu’a domin samun nasarar shugabanni wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwarsu. Shi ma a...
A cewarsa, daga cikin waɗanda Allah ya yi wa rasuwa akwai mahaifiyar yaran wato Mariya Sani, ‘yar shekara 45 da kuma Mujahid Sani, ɗan shekaru 20, sai Zahariya Sani, ‘yar shekara 18. Sauran sun haɗa da Hauwa Sani, ‘yar shekara 15 da Amira Sani, ‘yar shekara 3 da kuma Nura Sani, ɗan shekara 5. Muhammad ya bayyana cewa yanzu haka akwai waɗanda suka samu raunuka, inda suke asibitin Katsina domin karɓar magunguna. Mahaifin yaran ya bayyana irin kaɗuwar da ya yi lokacin da ya samu labarin faruwar wannan al’amari, wanda ya ce ya yi wa Allah godiya, su kuma da suka rasu Allah ya jikansu. Yanzu haka dai ‘yan’uwa da abokan arziki na ci gaba da zuwa yi wa Malam...
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna batutuwa da dama a wata zantawa ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin. Ofishin shugaban kasar Afirka ta Kudu ya ce, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, shugaban kasar ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan rikicin Ukraine da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Ofishin shugaban kasar Afirka ta kudu ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, “Tattaunawar ta biyo bayan bukatar shugaba Putin na yiwa shugaba Ramaphosa bayanin shirin zaman lafiya da Ukraine da kuma magance batutuwan da suka shafi moriyar juna.” Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {}...
“Shin an taɓa yin sulhu a na cin zarafin jama’a, an taɓa yin sulhu a na sa manoma noman dole, an taɓa yin sulhu a na karbar harajin dole, an taɓa yin sulhu ba a ajiye makamai ba?” Ya ce Turji da sauran ‘yan bindigansa irin su Kachalla Choma da Kachalla Haru ba za su ajiye makami ba, ya ce suna da kwamandoji da makaman da sun fi a kirga. Guyawa ya bayyana cewa Malamin bai san Turji ba, bai kuma san yankinsu ba, ya ce su da suke a yankin sun tabbatar Turji bai ajiye makami ba, kuma bai yi sulhu da kowa ba. Ya ce a kwanan baya Turji ya kashe jami’an tsaro tare da ƙone motarsu, don...
Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba. Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Waɗannan bayanai duk suna ƙunshe ne a cikin jawaban da aka gudanar a gangamin wayar da kai game da wannan cuta, wanda ya gudana a Kaduna. Lokacin da ta ke zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan wannan gangami, Dr. Maimuna Lawal Garba, ƙwararriyar Likita a fannin hanci, kunni da maƙogwaro, ta fara bayanin ta ne da bayyana abubuwan da suke haddasa wannan cuta ta Kansar Maƙogwaro. Ta ce, “Muna bai wa mutane shawara su kiyayi shan tabar sigari, barasa (giya). Haka kuma akwai yanayin aikin mutane, misali, masu aiki a wurin yankan katako, wannan ƙurar ta katako tana daga cikin abubuwan da za su iya sabbaba ma mutum kamuwa da wannan cuta. “Haka kuma akwai (radiation),...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC). Haka kuma, ya naɗa Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Abokan Hulɗa, da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa. A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, shugaban ƙasar ya bukaci waɗanda aka naɗa su yi amfani da ƙwarewarsu wajen tabbatar da burin gwamnatinsa a fannin wutar lantarki. Onanuga ya bayyana cewa waɗannan nade-naden suna jiran tantancewar Majalisar Dattawa. Sai dai, domin kauce wa gibin shugabanci a hukumar, Shugaba...
Da yake la’antar kisan a matsayin “mummuna, dabbanci, kuma lamarin da ba za a lamunta ba,” gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da adalci. Ya umurci hukumomin tsaro da su dau mataki tare da kama wadanda ke da hannu a kisan nasa nan take. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bada motocin aiki ga shugabannin hukumomi, jami’an tsaro da wasu manyan jami’an gwamnati a jihar. An gudanar da bikin mika motocin ne a Fadar Gwamnati da ke Minna. Gwamna Bago ya bayyana cewa wannan mataki na bayar da motocin aiki na da nufin tallafa wa harkokin sufuri da kara inganta gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Ya yabawa kwazon wadanda suka amfana da motocin a aikin gwamnati tare da bukatar su yi amfani da su bisa gaskiya da amanar da aka dora musu domin cimma nasarorin da ake bukata. Cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin akwai Shugabannin Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi, Hukumar Majalisar Dokoki, Hukumar Ma’aikata da Hukumar Kula da Binciken...
Matasan Kauru Sun zargin Dan Majalisar Dokoki Barnabas Danmaigona da Rashin tabuka komai Wata kungiyar matasa, Kauru Youth Ambassadors (KYA) a karamar hukumar Kauru sun nuna matukar damuwa kan yadda Barnabas Danmaigona, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kauru a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gaza samar da ingantaccen wakilci tun bayan zaben sa. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai taken daga ‘Daga Fata zuwa Yaudara’ wanda kuma Junaidu Ishaq Maisalati, ya sanyawa hannu, kungiyar ta caccaki dan majalisar kan abin da ta bayyana a matsayin mai dimama kujera kuma ɗan siyasar da ya gaza wajen gudanar da ayukka a mazabar da kuma aikin da zai amfani al’umma. Sanarwar ta koka da yadda al’ummar Kauru suka sanya kyakkyawan...
Shugaban Amurka, Donald Trump, yana shirin ƙara tsaurara wa Rasha takunkumi idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba kafin ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta. Ko da yake Rasha ita ce ƙasar da aka fi ƙaƙaba wa takunkumi a duniya, har yanzu tana amfani da arziƙin man fetur da iskar gas da ta ke da su domin ɗaukar nauyin yaƙin da ta ke yi da Ukraine. Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma Trump ya bayyana cewa zai sanya sabbin takunkuman da za su hana Rasha cin gajiyar kasuwanci da wasu ƙasashe. Daga cikin matakan, akwai sanya haraji har kashi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara. Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa a kan rayuwar ‘’yan Najeriya wanda aka wallafa bara a mujallar Springer ya nuna gudunmawar da jahilci yake taimakawa wajen yaduwar cutar a kasar. A sassan Najeriya da dama dai, ba kasafai mutane ke iya bambance Zazzabin Lassa da sauran nau’ukan zazzabi ba. Shin yaya za a iya gane Zazzabin Lassa a kuma bambance da sauran nau’ukan zazzabi? NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu...
Ta sake kafa tarihi bayan da jaridar National Concord mallakar MKO Abiola ta naɗa ta a matsayin editan jaridar ta farko, inda A shekarar 1986, aka ɗaga darajarta zuwa matsayin Manajan Darakta kuma Babban Edita mace ta farko da ta riƙe wannan matsayi a tarihin jaridun Nijeriya. Ta auri MKO Abiola a shekarar 1981, kuma ta tsaya tsayin daka tare da shi wajen gwagwarmayar siyasarsa da rikicin da ya biyo bayan zaɓen 12 ga watan Yuni, inda ta bayar da gagarumar gudunmawa a fagen jarida, tare da shafe kusan shekaru 30 tana jan ragamar kafafen yaɗa labarai a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Ya kuma kara da cewa, a Benuwe, sama da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a gwamnatin baya. Nuhu ya bayyana cewa, ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankin Arewa-maso-Yamma sun kai ga ceto mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su a watan Mayun 2025. An kuma kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan bindiga da tawagarsu a jihohin Zamfara, Kaduna, da Katsina. A wajen taron, akwai manyan shugabannin Arewa da suka hada da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe, Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume, tare da gwamnoni na yanzu da tsofaffi, Ministoci, Hakimai, da masu rike da mukaman siyasa. Ribadu ya kammala da jaddada kudirin gwamnati na tabbatar...
Sashen cinikayyar samar da hidimomi na Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni shida na farkon shekarar nan ta 2025, inda ya karu da kaso takwas bisa dari kan mizanin shekara. A cewar ma’aikatar cinikayya ta Sin, darajar hidimomin shige da fice a wannan wa’adi ta kai kudin Sin tiriliyan 3.89, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 544.9. Cikin wannan adadi, alkaluman hidimomin da aka fitar daga kasar Sin ya karu da kaso 15 bisa dari, wato darajar da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 1.69, yayin da na wadanda aka shigo da su kasar ya karu da kaso 3.2 bisa dari, daidai da kudin Sin tiriliyan 2.2. Sai kuma gibin cinikayya a fannin na bayar da hidimomi...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa kasar Rasha tana shirin kara dankon zumunci da kungiyar Brics saboda fuskantar takunkuman tattalin arziki wadanda kasar Amurka ta daura mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Maria Zakharova kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha tana fadar haka, ta kuma kara da cewa, kungiyar BRICS kungiya ce wace kasar Rasha ta dogara da ita don magance irin wadannan matsaloli. Sannan kasashen iya magance takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka suke dorawa kasar Rasha. Zakharova, ta kara da cewa kasashen Global south da BRICS sune kawayen Rasha a kan abinda ya mshafi matsalolin takunkuman tattalin arziki da kuma kawayenta a cikin harkokin siyasar duniya. Zakharova ta kara...
Hukumar Kula da Dokokin Hanya ta Jihar Legas (LASTMA) ta rufe wani gidan casu mai suna Vaniti Club House da ke kan titin Adeola Odeku a Victoria Island bisa laifin karya dokar harkokin sufuri ta shekarar 2018. A cewar LASTMA, an rufe gidan casun ne saboda ajiye motoci ba bisa ƙa’ida ba a gefen titi da kuma toshe hanyoyi, lamarin da ke haddasa cunkoso da barazana ga lafiyar jama’a. Wannan matakin ya samu jagorancin babban daraktan hukumar, Olalekan Bakare-Oki, tare da sashen ceto da tabbatar da doka. Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos Kwalara Ta Kashe Mutane 5 A Lagos, An Kai 60 Asibiti Ranga-Ranga Hukumar ta ce wannan mataki na ɗaya daga cikin tsarin...
Tsohon jami’in harkokin wajen Tarayyar Turai Joesp Borrell, ya yi gargadi game da ci gaba da rashin taka rawar gani daga bangaren kasashen Turai dangane da ayyukan cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi, yana mai cewa irin wannan rashin hankali ya sa kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta zama abokiyar tarayya a cikin laifukan da Isra’ila ke aikatawa. Joesp Borrell ya bayyana hakan ne a cikin wani fashin baki wanda aka buga a cikin jaridar The Guardian ta kasar Burtaniya. “Wadanda ba su yi aiki ba don dakatar da wannan kisan kiyashi da kuma keta dokokin kasa da kasa, duk da cewa suna da ikon yin wani abu kan hakan, to tabbas suna da hannu a cikin wadannan...
Gwamnatin tarayya ta ce tace a shirin ta sauya wuraren dake bushe a sassan arewacin Nijeriyaza a raba naira miliyan miliyan 3.4 kuma akasarin wadanda zasu amfana da wannan za su kasance mata ta hanyar Shirin ACReSAL. Da yake jawabi a wajen bude taron kwanaki 10 na masu ruwa da tsaki kan tsarin kula da tsare-tsare (SCMP) na sabbin magudanan ruwa guda 11 a fadin Jihohi bakwai na tarayya a Ilorin, kodinetan ayyukan ACRESAL na kasa, Mista Abdulhamid Umar, ya ce za a gudanar da aikin ne ta hanyar shirin kawo sauyi na dogon lokaci. Jami’in kula da ayyukan na kasa na ACRESAL Adamu Shettima wanda ya samu wakilcin kwararre a bangaren kula da ayyukan ruwa na gwamnatin...
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba wa sabbin ma’aikatan aikin gona 1,038 da aka dauka aiki takardun su na kama aiki. Bikin, ya gudana ne a gidan gwamnatin Kano. Da yake jawabi yayin bikin gwamnan ya gargade su da su guji cin hanci da rashawa, ya kuma bukace su da su yi wa jihar hidima cikin himma da gaskiya. Ya ce matakin ya nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da jihar ke yi na inganta samar da abinci da kuma habaka arzikin iyali. Gwamna Yusuf ya bayyana daukar ma’aikata a matsayin cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe da kuma wani muhimmin mataki na cimma wadannan manufofin. ...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da karin kudin da gwamnatoci a matakin jiha suke samu daga asusun tarayya, ’yan Najeriya da dama suna korafin ba sa gani a kas. Manazarta dai sun ce ko kafin karin ma ya kamata ya yi a ce ayyukan da gwamnatcin jihohi suke yi sun fi da ake gani Ko mene ne ya sa jihohi “ba sa kashe karin kudaden da suke samu yadda ya kamata”? NAJERIYA A YAU: Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin,...
Jaridar Le Monde ta bayyana cewa: Tallafin kayan da jiragen sama suke saukarwa a Gaza tamkar digon ruwa ne idan aka kwatanta girman bukatun al’ummar yankin Jaridar Le Monde ta ruwaito cewa, ko da yake hukumomin mamayar Isra’ila, a karkashin matsin lamba na kasa da kasa, sun ba da izinin saukar da kayan agajin abinci ta hanyar jiragen sama, amma adadin tallafin takaitacce ne da ba zai magance wata matsala ba. Le Monde ta kara da cewa: Sakamakon ya bayyana takaitacce ne a daidai lokacin da dubban manyan motoci makare da kayan agaji ke makale a wajen zirin Gaza. Jaridar ta yi bayanin cewa kasashe da dama da suka hada da Jordan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Faransa, da Birtaniya, sun fara...
Bayanin da Hukumar Haraji ta Kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, a rabin farko na wannan shekara, kudaden cinikin da kamfanoni a duk fadin kasar suke samu ya ci gaba da karuwa cikin kwanciyar hankali. Masana’antu sun sami ingantaccen ci gaba yayin da manufofin “sabunta manyan kayan aiki na kasa” da “Maye gurbin kayan amfani da suka tsufa da sababbi” suka yi tasiri sosai. Kudin da aka samu a bangaren sana’ar kere-kere ya karu da sauri fiye da matsakaicin karuwar dukkan kamfanoni da kashi 1.5%. Wannan ya tabbatar da cewa masana’antu su ne tushen karfafa tattalin arzikin kasar. Kazalika, masana’antun kirkire-kirkire sun kara habaka, inda kudaden da aka samu a bangaren sayar da kayayyaki na masana’antun kimiyya mai inganci ya...

Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15
Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kana shugaban kasar, Xi Jinping ya bayar da muhimmin umarni game da binciken ra’ayoyin jama’a masu amfani da shafukan Intanet kan aikin tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 a kwanan nan, inda ya ce, ya kamata aikin tattara ra’ayoyin jama’a ta yanar gizo wajen tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15 ya samu shigar jama’a sosai, kuma ya kasance wani aiki na dimokuradiyya dake shafar dukkan bangarori. Jama’a sun yi ta ba da shawarwari tare da gabatar da ra’ayoyi masu muhimmanci, wadanda ya kamata sassan da abin ya shafa su yi nazari a hankali tare da shigar da su cikin tsarin. Kuma dole ne...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Binciken Kwamishinan Sufuri Kan Belin Wanda Ake Zargi Da Safarar Kwayoyi
Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri, Ibrahim Namadi, kan hannu da yake da shi a ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Shugaban kwamitin kuma mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Tsarin Mulki, Barrister Aminu Hussain, ne ya mika rahoton ga Sakataren Gwamnati na Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim. Barrister Hussain ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da bincike bisa gaskiya da adalci, da kuma bin hujjoji, ba tare da son rai ba. Ya bayyana cewa an gayyato Kwamishinan Sufuri domin karin bayani, inda ya kuma gabatar da rubutaccen jawabi ga kwamitin. Sauran da aka tattauna da su...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati. Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin. Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko. Ta kara...
Rahotanni daga Gaza na cewa sojojin Isra’ila sun sake buɗe wuta kan Falasɗinawa da ke cikin tsananin buƙatar agaji a kusa da inda ake rabon kayan tallafi a cibiyoyi biyu, a jiya Lahadi. Asibitoci a Gaza sun ce aƙalla Falasdinawa 27 aka kashe. Rahotanni na cewa sojojin sun buɗe wa mutane wuta bayan isa gab da ɗaya daga cikin cibiyoyin rabon agajin na gidauniyar da Amurka da Isra’ila ke mara wa baya a Rafah. Sanan sauran kuma an kashe su ne a sansanin da ke tsakiyar Gaza. Har yanzu sojojin Isra’ila ba su yi martani ba kan wannan rahoton. Hamas ta ce ƙungiyar agaji ta Red Cross kaɗai za ta iya miƙa wa ‘yan Isra’ilar da take riƙe dasu a...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya bukaci sabbin mambobin hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) da aka rantsar da su kasance masu kishin kasa da kuma ci gaba da zama ’yan kasa nagari. Gwamna AbdulRazaq ya bayyana haka ne a yayin bikin rantsar da rukunin ‘B’, a sansanin NYSC dake Yikpata a karamar hukumar Edu. Ya kuma shawarce su da su yi taka tsantsan wajen gudanar da ayyuka daban-daban na kwas din. Gwamna AbdulRazaq ya tabbatar wa ‘yan yiwa kasa hidimar cewa gwamnatin jihar za ta samar da yanayin da zai taimaka musu su ci gaba. A nasa jawabin, kodinetan NYSC na jihar, Mista Onifade Joshua, ya yabawa gwamna AbdulRazaq bisa goyon bayan da yake baiwa...
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana jin dadinsa kan aikin titin Eiyenkorin zuwa Afon Ojoku zuwa Offa zuwa Odo zuwa Otin mai tsawon kilomita 49 da ake ginawa. Titin siminti na daya daga cikin manyan tituna hudu da ake ba da tallafi a jihar Kwara a karkashin shirin gwamnatin tarayya na karbar haraji a misalin hadakar kamfanin BUA. Gwamna AbdulRazaq ya godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da aiwatar da ayyukan karbar haraji da kuma sauran dimbin tallafin da yake baiwa jihar. “Muna duba ayyukan titunan gwamnatin tarayya da na Jihohi, wannan sabon titin Ilorin/Offa ne, kuma za ku ga yadda yake da inganci, dole ne mu gode wa Shugaba Bola Tinubu kan...
ADC ta ce, duk da cewa an tsara filin jirgin ne don karbar fasinjoji miliyan 14 a cikin shekara guda, amma rahotannin da ake da su sun nuna cewa, filin jirgin ya karbi fasinjoji miliyan 6.5 ne kawai a shekarar 2024, kasa da rabin karfinsa. Don haka, ADC ta yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su yi watsi da wannan aiki na “rashin hankali”, inda ta bukaci a dakatar da shi nan take, sannan a karkatar da kudaden zuwa ayyukan da al’umma suka fi bukata, wadanda su ya kamata kowacce gwamnati ta fi ba su muhimmanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a jiya Lahadi cewa, Sin da Rasha sun fara atisayen soja na hadin gwiwa mai taken “Tekun hadin gwiwa na shekarar 2025” a tekun Japan, a wani bangare na kokarin zurfafa hadin gwiwarsu ta fuskar “mutumin Amurka.” Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta bayyana cewa, sojojin biyu za su gudanar da ayyukan ceto a cikin ruwa, da yaki na hadin gwiwa na yaki da jiragen ruwa, da na yaki da jiragen ruwa, da na jiragen ruwa a kusa da tashar jiragen ruwa na Vladivostok na Rasha. Sanarwar ta ce, jiragen ruwa na kasar Sin 4 ne ke halartar atisayen tare da na Rasha, ciki har da makami mai linzami Shaoxing da Urumqi. Rasha da...
Wannan mataki yana daga cikin manyan matakan da za su tallafa wa inganta tsaron abinci, rage fatara, da ƙarfafa zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a Bauchi ta Kudu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A kokarin da Gwamnatin Jihar Jigawa ke yi na kara habbaka harkokin noma, shirin ACRESAL yace sami amincewar gwamnatin na siyo injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana guda 3,000 domin tallafawa manoma. Shugaban Shirin na Jihar, Malam Yahaya Kafin Gana ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. Yana mai cewar, samar da injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana ga manoman na da nasaba da bunkasa aikin gona a jihar Jigawa. A cewar sa, shirin ACRESAL na jihar ya sami sahalewar gyaran karin wasu cibiyoyin renon itatuwa guda 3 a sassan jihar. Malam Yahaya Uba Kafin Gana ya kara da cewar, cibiyoyin renon itatuwan da za’a gyara sune na garuruwan Birnin Kudu da Kafin Hausa da...
Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr Hameem Nuhu Muhammadu Sunusi ya kaddamar da rabon zakkar kudi ta shekarar musulunci ta 1446 a gundumar Yayari dake Karamar Hukumar Buji. A jawabin sa, Mai Martaba Sarkin ya ja hankalin al’umma da su ci gaba da fitar da hakkin Allah domin samun makoma a nan duniya da kuma gobe kiyama. Ya nuna gamsuwa da nasarorin da Gundumar ta samu wajen tattara zakka a masarautar sa. Daga bisani ya karrama Hakimin Yayari, Alhaji Garba Muhammad da Dagaci da kuma Mai Unguwar cikin garin Yayari. A jawabin sa, Sa’in Dutse, Mallam Mahmud Yunusa yace gundumar Yayari ce ta zo na 1 a tattara zakkar kudi yayin da Gundumomin Gantsa da Fagam suka zo na...
A cewar shugaban kwamitin, Katsina na kuma goyon bayan batun sauke wasu ikon gwamnati daga matakin tarayya zuwa jihohi, saka sarakunan gargajiya a cikin kundin tsarin mulki da kuma sake fasalin harkokin kuɗi. Sanata Ibrahim ya shaida wa kwamitin cewa an tattara dukkan ra’ayoyi da buƙatun jama’ar Katsina, tare da gabatar da su a cikin takardar matsayar. Tun da farko, yayin da yake ƙaddamar da taron jin ra’ayoyin jama’a, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan gyaran kudin tsarin mulki ya buƙaci a riƙa yin irin wannan taron lokaci zuwa lokaci domin ya dace da halin da ake ciki. Sanata Barau Jibrin, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya tabbatar da cewa dukkan abubuwan da aka tattara daga gwamnati, ƙungiyoyi da...
Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI da kuma kasar Japan suna iya jagorantar kasashen duniya zuwa ga rabata daga makaman kare dangi. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Ministan yana fadar haka a wani rubutu da yayi, wanda kuma aka buga a jaridar Asahi Shimbun ta kasar Japan. Ya kuma kara da cewa, kasashen biyu an yi amfani da makaman kare dangi a kansu. Y ace kamar yadda Amurka ta yi amfani da makaman nukliya kan kasar Japan a shekara ta 1945 a karshen yakin duniya na biyu, haka nan Sadam ya yi amfanin da makaman guba a kan iraniyawa a kallafeffen yakin da suka fafata na shekaru 8 a tsakaninsu. Arachi...
An ƙara hakimai shida a Masarautar Katsina kamar yadda mahukunta suka tabbatar. Wata sanarwa da Sakataren Masarautar Katsina, Alhaji Bello M. Ifo ya fitar ta ce tuni an fitar da sunayen sabbin hakimai shida da iyakokin da za su jiɓinci jagorancinsu. Jamus ta soma jefa kayan agaji a Zirin Gaza Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMA Sabbin hakiman sun haɗa da Karshin Katsina, Alhaji Sanusi Kabir a matsayin Hakimin Shinkafi da Tsohon Ministan Harkokin Sufurin jiragen sama Sanata Hadi Sirika a matsayin Marusan Katsina — Hakimin Shargalle. Sauran sun haɗa da Alhaji Ahmad Abdulmuminu Kabir Usman — Danmajen Katsina a matsayin Hakimin Dankama da Alhaji Abubakar Dardisu Sarkin Muduru a matsayin Hakimin Muduru. Sanarwar ta...
Magana ta gaskiya matsala daya ce zuwa biyu ko uku, na farko akwai laifin iyaye, na biyu akwai laifin samari da suke zuwa su yi auren, na uku kuma akwai laifin amaryar wacce ita ce take zaman auren. Bari na fara da maganar farko, dalilin da ya sa na ce laifin iyaye ne shi ne; duk mutumin da ya zo zai auri ƴarka, idan kana da ƴa ta isa aure, ya kamata ka zaunar da shi ka tambaye shi; mene ne ma auren, kuma me yasa yake son ya auri ƴar taka? da yawan samarin da suke yin aure, ba su san ma mene ne auren ba. An Nemi A Kafa Dokar Ta-ɓaci Kan Masu Ƙwacen Waya anyoyin Da Za...
A’isha ƴar shekara uku da suke zaune a ƙarƙashin inuwar bishiyar ɗogoyaro a wani ƙauye mai nisa a yankin Arewa maso Gabas (sansanin gudun hijira). Babu takalmi a ƙafarta, ta yi shiru, saboda radaɗi da take ji. ƙafafuwanta sirara sun yi rauni, cikinta ya dan kumbura saboda yunwa, idanunta sun fito tana cikin halin da bai kamata a ce mai shekaru irinta na ciki ba. Aisha Abdullahi ba ta iya yin kuka ba, domin babu ƙarfin halin yin hakan Mahaifiyarta, Maryam Abdullahi, tana girgiza ta a hankali a cinyarta, ta hada man gero mai ruwa da dakakken ganye a cikin wani ƙaramar roba. Abincin da suke ci a cikin kwana biyu. Ta shaida wa LEAɗERSHIP Weekend cewa, “wani lokaci ta...