Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata
Published: 2nd, September 2025 GMT
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar da auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi.
Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin.
Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin ZazzauSheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.
Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa.
Tun bayan hawansa mulki ne, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa zai yi wa matan da ba su da galihu auren gata, ta hanyar samar musu da dukkan kayayyakin da mace ke bukata a gidan aure da kuma yi musu walicci.
A wancan lokacin, ɗaura aurarrakin ne a wasu masallatan Juma’a a dukkan ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.
A babban Masallacin Juma’a na gidan Sarkin Kano kawai an daura auren kusan mutum 300 wanda shi ne Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaban Hisbah Sheikh Daurawa, wanda shi ne jagoran hidimar suka halarta.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya yi walicin angwaye yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zama waliyyin amare a kan sadaki Naira 50,000 ga kowace amarya.
Gwamnan Jigawa Umar Namadi na daga cikin waɗanda suka harlaci daurin auren.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: auren zawarawa Jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
এছাড়াও পড়ুন:
An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA