Kotu ta daure dan Shugaban Equatorial Guinea kan sayar da jirgin saman kasar
Published: 28th, August 2025 GMT
Wata kotu a kasar Equatorial Guinea ta daure dan Shugaban Kasar a kurkuku kan sayar da jirgin sama mallakin kasar ba bisa ka’ida ba, sannan ya zuba kudaden a aljihunsa.
Alkalin kotun dai a ranar Laraba ya yanke hukuncin cewa dan Shugaban Kasar Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, mai suna Ruslan Obiang Nsue, zai shafe shekaru shida a gidan yari.
Sai dai kotun ta ce idan zai biya kudin jirgin da ya bace ba za a daure shi ba, kamar yadda Daraktan yada labarai na Kotun Kolin Kasar, Hilario Mitogo ya shaida wa ’yan jarida.
Kotun dai ta yanke wa Ruslan mai shekaru 50 a duniya, wanda tsohon shugaban kamfanin jiragen samar kasar mai suna Ceiba Intercontinental hukuncin ne bisa laifin sayar da jirgin kasar mai suna ATR 72-500 ga wani kamfanin kasar Spain, sannan ya zuba kudin a aljihunsa.
A shekara ta 2023 an yi masa daurin talala bisa umarnin Mataimakin Shugaban Kasar, wanda shi ma dan uwansa ne na jini kuma dan shugaban kasar.
Kotun dai ta ce wanda aka yanke wa hukuncin zai iya kauce wa daurin idan ya biya tarar Dalar Amurka 255,000, kwatankwacin sama da Naira miliyan 382 ga kamfanin jiragen sannan ya biya tara ga gwamnati.
Sai dai kotun ta wanke shi daga wasu zarge-zargen na almundahana da halatta kudaden haram.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Shugaban Kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA