Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista
Published: 8th, April 2025 GMT
Tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce Ma’aikatun Harkokin Jin-ƙai na tarayya da jihohi sun zamo matattarar cin hanci da rashawa a Nijeriya.
Essien, ya kuma zargi ministocin ma’aikatun da karkatar da biliyoyin naira da aka ware domin ‘yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali.
Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58“Wani zai yi tunanin ƙirƙirar ma’aikatun nan zai inganta rayuwa da walwalar al’umma, amma abun takaici sun zamo mazurarar sace kuɗin al’umma ba tare da wata shakka ba.
“Dukkanin ministocin ma’aikatun jin-ƙan Najeriya, babu wanda ba a zarga ba da karkatar da kuɗin al’umma.” In ji shi.
Kazalika ya soki shirin ‘yan siyasa na raba jari ga talakawa, yana mai cewa suna yi ne don boye gazawar gwamnati na samar da abubuwan more rayuwa da damarmaki ga al’ummarsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ma aikatar Jin Kai
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik.
Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA