Sabbin Haraji: Yadda ‘Yan Bindiga Ke Tilasta Wa Jama’a Biyan Miliyoyin Kuɗi A Zamfara
Published: 23rd, April 2025 GMT
Garuruwan da aka fi tsananta wa harajin sun haɗa da Gijinzama da aka tilasta musu biyan Naira miliyan 8.5, Dakolo da aka karɓi Naira miliyan 5 da buhun wake 20, sai Kibari da Kunchin Kalgo da suka biya Naira miliyan 20, Sungawa da Naira miliyan 15, da kuma Yalwa da aka tilasta su biyan Naira miliyan 2.
Bayan rasuwar Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga mai suna Dogo Gide ya sa harajin Naira miliyan 100 a kan ƙauyuka 23 da ke ƙaramar hukumar Tsafe.
A ƙarshen makon da ya gabata kuma, mazauna ƙauyen Dankurmi a ƙaramar hukumar Maru sun fuskanci sabon harajin Naira miliyan 60.
Wani mazaunin ƙauyen Dan Jibga, Muhammad Dogo, ya bayyana cewa bayan kashe mutane biyu a Gama Lafiya, an ƙaƙaba wa yankin harajin Naira miliyan 10.
Haka kuma, haraji ya ci gaba da yaɗuwa a Unguwar Tofa (Naira miliyan 26.6), Makera (Naira miliyan 15), Sungawa (Naira miliyan 20), Rakyabu (Naira miliyan 7), Yalwa (Naira miliyan 8), Mai Saje (Naira miliyan 11), da Langa-Langa (Naira miliyan 20 zuwa 30).
Sauran yankunan da ‘yan bindigar suka ƙaƙaba wa haraji sun haɗa da Gidan Dawa, Rijiyar Tsakar Dawa, Dan Jibga da kuma Bilbis. Malam Ibrahim Maru, wani mazaunin karamar hukumar Maru, ya ce matsalar ta’addanci a yankin na ƙara ta’azzara fiye da da.
Lamarin na nuna irin ƙalubalen da jama’a ke fuskanta a hannun masu aikata laifuka, wanda ke buƙatar kulawar gaggawa daga gwamnati da hukumomin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Haraji Matsalar Tsaro Yan bindiga Zamfara Naira miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar.
Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasaAn ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.
Shedun gani da ido sun ce ɗaya daga cikin motocin bas ɗin mai lamba KG: KPA 622LG na kan hanyarta zuwa Abuja, tare da fasinjoji daga wata tashar mota a unguwar Ankpa da ke yankin Kogi ta Gabas.
Har yanzu ba a iya gano adadin fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba zuwa yanzu, sai dai mun iya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da fasinjoji ne daga yankin Ankpa, kamar yadda aka gano wasu takardu da wasu kayayyaki a wurin da lamarin ya faru suka bayyana.
“Motocin bas ɗin guda biyu suna kan hanyar Abuja ne a lokacin da suka ci karo da shingayen ’yan bindiga a safiyar ranar Alhamis. Dukkanin fasinjojin, ciki har da direban motocin bas ɗin biyu an yi awon gaba da su cikin daji,” in ji Unubi Ademu, wani mazaunin Achigili, a ƙauyen da ke maƙwabta.
Al’ummar yankin sun ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da mafarauta da kuma ’yan banga suna ƙoƙarin magance lamarin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kogi (PPRO), CSP William Aya bai amsa kira da saƙo ba lokacin da aka tuntuɓe shi har zuwa lokacin tattatara wannan rahoto.