Burkina Faso ta sanar da dakile wani yunkurin juyin mulkin a kasar
Published: 23rd, April 2025 GMT
Hukumomin Burkina Faso sun sanar da cewa sun dakile wani sabon yunkurin juyin mulki, da aka shirya daga Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast.
Ministan tsaron Burkina Faso Mahamadou Sana ne ya fitar da cikakken bayani kan juyin mulkin da bai yi nasara ba, ya kuma kara da cewa ana fargabar sake yunkurin tayar da zaune tsaye.
Ministan tsaron Burkina Faso, Mahamadou Sana, ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa hukumomin kasar sun dakile yunkurin juyin mulkin da aka yi wa hukumomin gwamnati.
An dai shirya juyin mulkin ne a ranar 16 ga watan Afrilu tare da kai farmakin hadin gwiwa a fadar shugaban kasa.
Sanarwar da aka fitar a hukumance ta ce jami’an leken asiri sun kame mutane da dama musamman sojoji dake da alaka da yunkurin juyin mulkin.
Ma’aikatar ta kuma yi nuni da cewa, masu yunkurin juyin mulkin sun bullo da dabarun da za su bijire wa jami’an leken asiri tare da ingiza su wajen aiwatar da kame-kame a cikin jami’an tsaro da na cikin gida.
Idan dai ba a manta ba, an dakile wani yunkurin juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Satumban shekarar 2023 inda aka kama sojoji hudu tare da korar mutane biyu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta
A jiya Litinin ne dai gwamnatin kasar Holland ta sanar da hana wa minstocin tsaron kasa Itmir Bin Gafir, da na kudi, Bitsirael Smotrich shiga cikinta.
Kasar ta Holland ta zargi wadannan mutanen biyu da cewa suna ingiza sojojin HKI da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da kuma fadada yawan matsugunan ‘yan sahayoniya a yankunan da aka ce nan ne za a kafa Daular Falasdinawa.
Haka nan kuma gwamnatin kasar ta Holland ta kira yi jakadan HKI a birnin Hauge domin gargadinsa akan yanayin da ake ciki a Gaza, da cewa babu yadda za a iya ci gaba da jurewa akansa, ko kare dalilin jefa yankin cikin wannan halin.”
Wannan matakin na kasar Holland ya zo ne gabanin wani taro da tarayyar turai za ta yi a yau Talata domin jingine aikin tare da HKI a fagen nazari da bincike na ilimi, saboda ta ki tsagaita wutar yaki a Gaza.
Tun da fari, Fira ministan kasar Holland Dick Schoof ya wallafa a sharin X cewa; A yayin taron da kasashen turai za su yi, Kasarsa za ta yi matsin lamba akan ganin an dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da HKI, haka nan kuma kakaba takunkumai akan shigar da kayanta na kasuwanci zuwa kasuwannin turai.
Fira ministan na kasar Holland ya ce, ya fada wa shugaban HKI Ishaq Herzog wannan matakin da suke son dauka ta hanyar tarayya turai.