Munanan abubuwan da suka faru na zubar da jini bayan wasa tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli a Libya

A kusa da filin wasa na birnin Tripoli an ga abubuwan na zubar da jini bayan wasan da aka yi tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli, lokacin da wasu motocin ma’aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin hadin kan kasa suka bindige magoya bayanta da gangan.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa bayan an kammala wasan ne wata mota dauke da makamai ta kutsa cikin wurin da jama’a ke cunkoso, inda suka bi ta kan wasu matasa, lamarin da ya haifar da firgici da hargitsi. An kuma ji karar harbe-harbe a wurin, lamarin da ya ta’azzara lamarin tare da jikkata wasu da ke wajen.

Majiyoyin lafiya sun tabbatar da cewa an mayar da wani matashi dan shekara ashirin zuwa wani asibitin da ke kusa da birnin wasanni, inda aka bayyana halin da yake ciki da mawuyaci. Har yanzu ba a fitar da kididdigar adadin wadanda suka jikkata a hukumance ba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura

Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin.

Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar.

A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen.

Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa  na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa.

Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama.

Dr Shuaibu ya bayyana cewa, sauran mutane 9 da ke cikin jirgin har yanzu ba a same su ba a lokacin da ake bayar da wannan rahoto.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, ba a fitar da sunayen waɗanda abin ya shafa ba, amma lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da baƙin ciki.

Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa, za a raba rigunan kariya (life jacket) ga fasinjoji a nan gaba kadan domin kiyaye sake afkuwar lamarin nan gaba.

Ya kuma gargadi matuka kwale-kwale da su kiyaye ƙa’idojin tsaro da kaucewa cunkoson fasinjoji, musamman da yamma a lokacin damina, inda ruwa ke  ƙaruwa a kowane lokaci.

Dr Hambali, wanda ya isa wurin da abin ya faru, ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Wasu daga cikin mazauna yankin da Rediyon Najeriya ta tattauna da su, sun nemi gwamnatin ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace, tare da inganta hanyoyin sufuri ta ruwa.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya
  • Muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba za mu amince da kafa ƙasar Falasɗinu — Birtaniya
  • Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 
  • Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa
  • Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan
  • Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane Da Dama A Yola
  • An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja
  • An gano gwawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja
  • Kungiyar Kwallon Kafa Ta Matan Najeriya Ta Samu Nasara Akan Takwararta Ta Moroko Da Kwallaye 3-2