Najeriya : Mutum 56 suka mutu a harin Benue
Published: 20th, April 2025 GMT
Hukumomi a jihar Benue dake Najeriya sun ce adadin wadanda suka mutu a harin da ‘yan bindiga suka kai a hukumomin Ukum da Kogo ya kai 56.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, a wata ziyara a yankin ya shaidawa manema labarai cewa adadin wadanda suka mutu a harin ya kai 56.
”A yanzu, mutum 56 ne suka mutu wadanda ba su ji ba su gani ba, da suka hada da iyaye da maza da mata da kananan yara”, in ji shi.
Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakai domin kawo karshen hare-hare a jihar.
Gwamnan ya ce tuni gwamnatin jihar ta kara tura jami’an tsaro zuwa yankunan domin kwantar da hankula.
Harin na zuwa ne kimanin mako biyu bayan wasu yan bindiga sun kashe fiye da mutum 100 a wasu hare-hare a jihar Plateau mai makwabtaka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Bom Da Ya Tashi A Arewa Maso Gabashin Najeriya Ya Kashe Mutane 6
Wani bon kirar hannu da aka dasa akan hanyar dake hada Rann da Gamboru a jihar Borno ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6.
Daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom din sun hada mata da kananan yara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta sanar.
Kungiyar nan mai suna; gwamnatin musulunci a yammacin Afirka ce ta sanar da daukar alhakin kai hari na ranar Litinin din da ta gabata.
Bugu da kari sauran wadanda su ka rasa rayukan nasu manoma ne da suke cikin motar a-kori-kura da ta taka nakiya.
Baya ga wadanda su ka rasa rayukansu, wasu mutanen su 3 sun jikkata,kuma tuni an dauke su zuwa asibiti domin yi musu magani.
Wani dan sintiri da yake aiki da rundunar fararen hula masu taimakawa jami’an tsaro, Abba Madu, ya shaida wa manema labaru cewa; Da alamu an dasa bom din domin ya tashi da jami’an tsaro da suke yin sintiri akan wannan hanyar.
Kungiyoyin ‘yan ta’adda sun saba dasa irin wadannan nakiyoyin da bama-baman akan hanyar da jami’an tsaro suke bi.
Kungiyar nan da take kiran kanta; Gwamnatin Musulunci a yammacin Afirka wacce a takaice ake kira; “ISWAP” ce ta dauki nauyin kai harin.
Tun a 2009 ne yankin Arewa maso gabashin kasar ta Najeriya yake fama da matsalar kungiyoyi masu dauke da makamai da su ka hada Bokoharam, sannan kuma daga baya waje 2016, kungiyar gwamnatin musulunci a yammacin Afirka.