Leadership News Hausa:
2025-07-31@12:22:00 GMT

Muna Ganin Kashe-kashe Ta Ko’ina – ‘Yan Gudun Hijirar Sudan

Published: 20th, April 2025 GMT

Muna Ganin Kashe-kashe Ta Ko’ina – ‘Yan Gudun Hijirar Sudan

Labarin harin na zuwa ne kwana daya kafin cika shekara biyu da fara yakin basasar na Sudan tsakanin RSF da rundunar sojin kasar.

Da yake magana da BBC a safiyar Lahadi, wani mazaunin Zamzam da ke aiki da wata cibiyar da ke tallafa wa mutane da abinci ya ce an kashe “matasa da yawa”.

“An kashe masu aiki a cibiyar, haka ma an kashe likitocin da ke aikin kula da lafiya a cibiyar,” a cewar Mustafa mai shekara 34 cikin wani sakon murya ta WhatsApp.

“An kashe kawuna da dan dan’uwana. An raunata mutane kuma babu magani ko asibitin da zai kula da su – suna mutuwa saboda zubar jini.

“Har yanzu ana ci gaba kawo hari, kuma muna tunanin za a ci gaba da yin hakan har zuwa safiya.”

Ya kara da cewa an rufe dukkan hanyoyin fita daga sansanin “kuma dakaru sun zagaye duka bangarori hudu”.

Wani mutum mai suna Wasir ya ce “babu komai da ya rage a Zamzam”.

“Fararen hula masu yawa sun gudu, mu ma muna kokarin tafiya amma ba mu yi nasara ba, an rufe duka titunan, ga kuma yara a tare da mu.

Mutuwa ta ko’ina. Yanzu da nake magana da ku daga cikin wani rami, ana ta luguden wuta.”

Wasu daga cikin mazauna sansanin sun samu tserewa kuma suka yi tafiyar kilomita kamar 15 zuwa el-Fasher, a cewar Ministan Lafiya na Arewacin Darfur Ibrahim Khater.

“Na ga mutane da yawa suna barin Zamzam da kafa – akasarinsu yara, da mata, da tsofaffi,” in ji shi.

“An raunata wasu, wasu agajiye bayan an kashe ‘yan’uwansu. Lamarin ya ta’azzara.”

Jagorar tattara kayan agaji na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, Clementine Nkweta-Salami, ta ce “ta kadu sosai” da jin rahotonnin da ke fitowa daga Darfur.

“Wannan na nuna irin yadda ake tsananta hare-haren rashin imani kan mutanen da aka kora daga muhallansu da masu aikin agaji,” a cewarta cikin wata sanarwa.

Ita ma ma’aikatar harkokin Amurka ta yi “tir da rahotonnin hare-haren da RSF ta kai a Zamzam da kuma Abu Shouk”, tana cewa: “Muna yin Allah wadai da hare-haren RSF kan fararen hula marasa karfi.”

Kungiyar bayar da agaji ta Relief Organization ta ce ma’aikatanta tara “aka yi wa kisan rashin imani cikinsu har da likitoci, da direbobi, da wani jagoran tawaga” a harin da aka kai a Zamzam.

Kungiyar, wadda ta ce ita kadai ta rage da ke aikin kula da lafiya a sansanin, ta zargi RSF da aikata laifukan.

“Mun fahimci cewa wadannan hare-hare ne da gangan kan cibiyoyin lafiya a yankin domin hana ‘yan gudun hijira samun magani.

“Muna cikin zulumi ganin yadda aka hari daya daga cikin cibiyarmu da sauran cibiyoyin lafiya a el-Fasher.”

Kashif Shafikue, shugaban kungiyar, ya fada wa BBC cewa abin da ya faru da gangan aka aikata shi.

Kamar yadda wata ma’aikaciyar lafiya da ta tsira ta bayyana masa, ya ce mayakan RSF sun shiga wata maboyar mutane suka harbe mutum tara a ka da kuma kirjinsu.

CIkin wata sanarwa a ranar Asabar, RSF ta ce ba ita ce ta kai hare-hare kan fararen hular ba, kuma wai an shirya hare-haren ne domin a shafa mata kashin kaji.

Kwana daya bayan haka ne kuma ta ce “ta yi nasarar ‘yanta” sansanin daga hannun dakarun Sudan.

RSF ta zargi sojojin kasar da yin amfani da Zamzam “a matsayin sansanonin soji da kuma fararen hula a matsayin garkuwa”.

Wata tawagar kwararru a jami’ar Yale da ke Amurka ta ce hotunan tauraron dan’Adam da ta nazarta sun nuna “harin ya zama mafi muni da aka kai ta kasa a kan Zamzam…tun bayan fara yakin a el-Fasher cikin shekarar 2024”.

Ta ce ta lura da yadda “hare-haren amfani da wuta suka kona gine-gine da wurare da yawa a tsakiya, da kudanci, da kudu maso gabashin sansanin”.

Yakin da ake yi domin kwatar iko tsakanin RSF da sojin gwamnatin Sudan, ya jawo bala’i mafi girma a duniya a kan al’umma, inda ya tilasta wa sama da mutum miliyan 12 barin gudajensu da kuma jefa su cikin yunwa.

An fara gwabzawa a ranar 15 ga watan Afrilun 2023 bayan shugaban RSF da shugaban Sudan sun samu sabani game da makomar kasar.

El-Fasher ne gari mafi girma a yankin Darfur da ke karkashin ikon sojoji, wanda RSF suka kewaye tsawon shekara daya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gudun hijira

এছাড়াও পড়ুন:

Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar

Ma’aikatar leken asiri na JMI ta bada sanarwan cewa ta gano shirin makiya na kashe manya-manyan Jami’an gwamnati har 35 a kasar kafin yakin da suka dorawa kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar na fadar haka, ta kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 sun yi kokarin kashe many-manyan Jami’an gwamnati har 35 a cikin yakin. Da kuma wasu 13 watanni kafin yakin, amma saboda matakan da ma’aikatar ta dauka hakan bai faru ba.

Labarin ya kara da cewa, hukumar a tsaye take kan makirce-makircen makiya, sannan kuma tana daukar matakan da suka dace don hana  kutsawar su a cikin kasar da kuma cutar da shuwagabanni da kuma mtanen gari.

A wani bangare kuma hukumar ta bayyana cewa tana ayyukan leken asiri kan HKI da kuma shirye-shiyenta nag aba. Tana samun ma’aikata a cikin sojoji da jami’an tsaro na HKI. Sannan ta kara da cewa ma’aikatansu kadanne yahudawan suka kama.

Majiyar ta kara da cewa ta sami bayanan sirri kan shirye-shrye masu muhimmanci na HKI daga ciki har da bayani dangane da shirinta na makaman Nukliya.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya: Likitoci a Lagas Sun Shiga Yajin Aiki July 29, 2025  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai July 29, 2025 Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu July 29, 2025  Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta July 29, 2025 Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba July 29, 2025 Araqchi: Iran Zata Mayar Da Martanin Da Ba Zai Yiwu A Boye Ba  Kan Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kanta July 29, 2025 Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza July 29, 2025 Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine July 29, 2025 Kasar Faransa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Birnin Zahedan Na Kasar Iran July 29, 2025 Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza July 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku  
  • Tallafin matar Tinubu na N1bn ga ’yan gudun hijirar Binuwai ya bar baya da kura
  • Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa
  • Ku Daina Kashe Mutane Ko Ku Miƙa Wuya – Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Bindiga
  • Matashi Ya Kashe Surukarsa Saboda Shigarta Cikin Sha’anin Aurensu
  • Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar
  • Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu
  • Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati
  • SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa