Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ranar Hausa ta duniya: Za a yi gagarumin biki a fadar Sarkin Daura

Gwamnatin jihar Katsina ta ce shirye-shirye sun kankama domin bin sahun sauran sassan duniya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya a za ake gudanarwa ranar 26 ga watan Agustan kowacce shekara.

Shugaban Hukumar Kula d Tarihi da Al’adu ta jihar, Dr Kabir Ali-Masanawa ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai a Katsina ranar Talata.

Ya ce za a yi taron ne a Fadar Sarkin Daura da ke jihar, kuma ana sa ran manyan baki daga kasashe akalla 24 za su halarta.

Masanawa ya ce wannan shi ne karo na farko da gwamnati ta shiga cikin shirya bikin, inda ya ce hatta Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ya tsaya tsayin daka wajen ganin bikin ya yi nasara.

DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi

Shugaban ya ce ranar na fito da tarihi da al’adun Hausawa a fadin duniya, wadanda suka warwatsu a kasashen duniya daban-daban.

Ya kare da cewa, “Kwanan nan mun ziyarci Fadar Sarkin Daura inda muka jaddada masa alfaharin da muke yi da harshen Hausa.

“Ana sa ran a bana, akwai akalla kasashe 24 da za su halarci bikin na Daura,” in ji shi.

Shugaban hukumar ya kuma ce bikin zain una al’adun Hausawa ta hanyar kade-kade da raye-raye da tufafi da abincin Hausawa.

Daga nan sai ya baki masu shirin shiga jihar tabbacin cewa akwai zaman lafiya kuma suna kokari wajen bunkasa tsaro, ta yadda jihar za ta ci gaba da zama wajen yawon bude ido ga baki.

Daga cikin kasashen da ake has ashen zuwan bakin har da Burtaniya da Amurka da Saudiyya da Ghana da kuma kasar Netherlands, a karon farko.

Kiyasi dai ya nuna Hausa shi ne yare na 11 da aka fi amfani da shi a duniya inda yake da masu amfani da shi sama da miliyan 150.

An dai fara bikin ranar ne a shekara ta 2015 kuma duk shekara akan gudanar da babban taro a sassa daban-daban na duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Dauki Matakan Mayar Da Martani Kan Bankuna Biyu Na EU
  • Ranar Hausa ta duniya: Za a yi gagarumin biki a fadar Sarkin Daura
  • An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe
  • Fasahohin AI Sun Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
  • PDP Ta Soki Gwamnatin Tinubu Kan Tsare Tambuwal Da EFCC Ta Yi
  • Giyar mulki Na Jan Trump – Ƴan Democrats
  • ’Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 6 A Taraba
  • Sin Ta Kammala Yi Wa Yankuna 5 Na Kare Muhalli Da Halittu Na Kasar Rajista
  • Jiragen Saman NAF Sun Kai Hari Kan Taron ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara
  • Za a samu ambaliya da ruwa mai karfi a jihohi 15 a Arewa —NEMA