Gwamnatin Kasar Aljeriya Ta Dakatar Da Zirga-Zirgan Jiragen Saman Kasar Zuwa Kasar Mali
Published: 8th, April 2025 GMT
Gwamnatin kasar Aljeriya ta dakatar da duk zirga-zirgin jiragen sama daga kasar Mali da kuma zuwa kasar saboda abinda ta kira keta hurumin sararin samaniyar kasar.
Shafin yanar giza na watsa labarai “Africa News” ya nakalto tashar talabijin ta kasar Aljeriya na fadar haka a daren Lahadi.
Kafin haka dai matsalolin sun tashi tsakanin kasashe yanken Sahel 3 Niger, Mali da Burkiya faso kan kakkabo jirgin saman yaki wanda bai da matuki wanda ya keta sararin samar kasar ta Aljeriya a makon da ya gabata, wanda ya sa kasashen uku suka janye jakadunsu daga kasar.
Gwamnatin kasar Mali dai bata yi magana a kan wannan matakin da gwamnatin kasar ta Aljeriya ta dauka ba.
Sai dai dakatar da zirga-zirgan jiragen sama tsakanin kasashen biyu zai shafi al’amuran kasuwanci soai a kasashen yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sakkwato Ta Sayo Manyan Tan-tan 250 Na Sama Da Naira Biliyan 22
An shawarci gwamnatocin jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da su kirkiro hanyoyi na wayar da kan al’umma dangane da shirye-shiryen tallafi da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da tsaro a yankunansu.
Shugaban sashen kimiyyar zamantakewa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Chika Umar Aliyu, ne ya bayar da wannan shawara yayin gabatar da takarda a wajen taron shekara-shekara na kungiyar Nigerian Institute of Management reshen jihar Sokoto na shekarar 2025, wanda aka hada da gabatar da lambar yabo ga wadanda suka cancanta.
Farfesa Chika ya bayyana cewa, gwamnati tarayya na da shirye-shiryen tallafi da dama da suka hada da na noma, kasuwanci da kuma koyar da sana’o’in hannu domin kara habaka tattalin arzikin ‘yan Najeriya da rage zaman kashe wando, da tayar da hankali musamman matasa a yankin.
Ya jaddada cewa dole ne gwamnatocin jihohi su tallafa wa kokarin gwamnatin tarayya ta hanyar amfani da hukumominsu na jin dadin al’umma domin cimma burin shirye-shiryen.
A jawabinsa wajen taron, kwamishinan noma na jihar Sakkwato, Muhammad Tukur Alkali, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayo manyan Tan-tan na noma guda 250 da kayan aikin gona da darajarsu ta kai naira biliyan ashirin da biyu da miliyan dari daya (₦22.1bn), domin tabbatar da wadatar abinci.
A cewar Tukur Alkali, gwamnatin jihar ta hanyar shirye-shiryen inganta rayuwar al’umma, ta samar da sama da ayyukan yi 2,700 a bangaren noma, abin da ke da tasiri mai girma wajen bunkasa noma mai dorewa da ci gaban ababen more rayuwa a karkara.
Daga Nasir Malali