Aminiya:
2025-08-01@12:20:35 GMT

Gwarzon gasar Alƙur’ani ya Kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina

Published: 30th, March 2025 GMT

Iyayen Abdulsalam Rabi’u Faskari, wanda aka sace tare da mahaifinsa a Jihar Katsina, sun bayyana cewa sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Abdulsalam, wanda ya lashe gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa da aka gudanar a Jihar Kebbi, an sace shi tare da mahaifinsa da wasu makonni biyu da suka gabata, bayan Gwamnan Katsina ya karrama shi.

Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi. Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi

Mahaifinsa, Malam Rabiu Zakariya Faskari, ya shaida cewa suna tsare a hannun ’yan bindiga a Katsina har sai da wani babban ɗan bindiga mai suna Yellow daga Zamfara ya zo ya karɓe su da ƙarfi.

“Ya yi wa masu garkuwa duka kafin ya tafi da mu,” in ji shi.

Ya ce an yi ciniki kan fansa amma Yellow ya ƙi yarda.

“Muna ta addu’a har ranar Juma’a da aka zo aka ce mu fito mu tafi. Yaransa suka ɗauke mu suka kai mu wani gari, daga nan muka yi tafiyar awa huɗu kafin muka samu mota.”

Malam Rabiu, ya ce da suka hau babur sai direban ya shaida musu cewa an kashe Yellow.

“Ashe mutuwarsa ce ta sa yaransa suka sake mu muka koma gida.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Gasar Alƙur ani Gwarzo

এছাড়াও পড়ুন:

Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati

Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati.

Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar.

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri  Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno

Bakori, wanda shi ne Kwamishinan Harkokin Noma na jihar, ya ce binciken kwamitin ya gano cewa makarantu biyu masu zaman kansu ne kacal a faɗin jihar ke da cikakkiyar rajista da hukumomin da suka dace.

“Jihar Katsina na da makaruntun gaba da sakanadare na gwamnati huɗu da ke bayar da takardar shaidar difloma da koyarwa, sai kuma ƙarin 39 masu zaman kansu.

“Sai dai bincikenmu ya bankaɗo biyu ne kacal a cikin 39 suke da cikakkiyar rajista da hukumomi.”

Kwamishinan, ya kuma ce shida daga cikinsu na buƙatar gyare-gyare domin kammala rajistar, yayin da 22 ke aiki ba tare da rajistar ba.

“Ƙarƙashin sabon tsarin da muka ɗauka yanzu, ya zamo dole makarantun da ke bayar da takardar shaidar digiri su yi rajista da Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC).

“Masu difloma kuma da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha (NBTE), sai masu koyarwa da Hukumar Kula da Kwalejin Ilimi ta Ƙasa (NCCE).

Bakori, ya jaddada cewa, duk makarantar da ta saɓa wa wannan tsarin, a shirye gwamnatin take ta rufe ta.

Sai dai ya yi wa ɗaliban da ke makarantun albishir ɗin cewa gwamnatin za ta tabbatar ta sauya musu makaranta zuwa masu rajista daga waɗanda ba su da su, idan buƙatar rufe su ta taso.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana
  • Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah
  • ‘Yan Sandan Niger Sun Hada ‘Yan’uwa Mutanen 35 Da Aka Ceto Da Iyalansu 
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Kwamitin Kolin JKS Ya Shirya Taron Bita Tare Da Wadanda Ba ’Yan Jam’iyyar Ba 
  • Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Ku Daina Kashe Mutane Ko Ku Miƙa Wuya – Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Bindiga