Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon Ya Yi Gargadi Akan Masu Tunanin Kulla Alakar Kasar Da HKI
Published: 24th, March 2025 GMT
Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barri ya jaddada cewa; HKI tana kokarin jefa Lebanon cikin tarkon kulla alaka da ita, yana mai jaddada cewa; Ko kadan Lebanon ba ta kama wannan hanyar ba.
Nabih Barri ya bayyana yadda wasu rahotanni daban-daban suke Magana akan cewa Amurka tana kai gwauro da mari, domin ganin an bude alaka kai tsaye a tsakanin Lebanon da HKI.
Shugaban majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya ce, ko kadan kasar Lebanon ba ta tunanin kulla alaka da HKI.
Haka nan kuma ya yi ishara da tsagaita wutar yaki wacce a kodayaushe HKI take ketawa, yana mai tabbatar da cewa Hizbullah tana riko da ita, don haka ya yi kira ga Amurka da sauran bangarorin da suke a cikin tsagaita wutar da su yi matsin lamba ga HKI domin ta yi aiki da ita.
Bugu da kari Nabih Barri ya ce; Sojojin kasar ta Lebanon sun gama shiryawa domin shiga cikin kudancin tafkin Laitani, amma matsalar da ake fuskanta ita ce yadda Isra’ila take kin janyewa daga wasu yankuna a cikin Lebanon.
Nabih Barri ya kuma jaddada cewa; Kungiyar Hizbullah tana aiki da tsagaita wutar yakin, kuma ba ta keta ta ba ko kadan.
Shugaban Majalisar Dokokin kasar ta Lebanon ya kara da cewa; Duk da cewa HKI tana keta tsagaita wutar yaki, amma ko sau daya Hizbullah ba ta harba ko harsashi daya ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tsagaita wutar
এছাড়াও পড়ুন:
Jaridar The Guardian Mafi Yawan ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Ne A Gidan Yarin Kasar Girka
Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan
Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma dokar ta kunshi hukunta masu laifin daurin shekaru 25 a gidan yari.
Jaridar ta The Guardian ta ruwaito cewa: Masu fasakwaurin mutane da aka yanke wa hukunci sun zama rukuni na biyu mafi girma a gidajen yarin Girka, bayan masu safarar miyagun kwayoyi.
Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Sudan su ne rukuni na hudu mafi girma na masu neman mafaka a kasar Girka, inda suka zarce ‘yan ciranin gargajiya na wasu kasashe kamar ‘yan Siriya da Falasdinawa.