Aminiya:
2025-08-01@05:04:06 GMT

’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara

Published: 23rd, March 2025 GMT

Aƙalla jami’an rundunar tsaron al’umma ta Zamfara (CPG) 10 ne, suka rasu, yayin da wasu 14 suka jikkata a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a yankin Anka da ke Jihar Zamfara.

Sun kai harin ne a ranar Asabar bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki wani sansanin ’yan bindiga da ke dajin Bagega a ranar Juma’a da Asabar.

An shiga ruɗani yayin da Sanusi II da Bayero ke shirin hawan salla a Kano Ɗan sa-kai ya kashe matasa biyu a Borno

A yayin farmakin, sun kashe ’yan bindiga da dama kuma sun kuɓutar da wasu mutanen da aka sace a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ’yan bindiga, Alhaji Beti.

Wata majiya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kuma ƙone gidan wani shugaban ’yan bindigar mai suna Bellon Kaura, wanda lamarin da ya fusata su.

“Kurakuran da suka yi shi ne komawa ta hanyar da suka bi a lokacin farmakin farko,” in ji wani shugaba a yankin Anka.

“’Yan bindigar sun tsere daga sansaninsu amma sun shirya tarko, sun yi kwanton-ɓauna, kuma suka buɗe wuta bayan jin ƙarar baburan jami’an tsaron.”

Harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro bakwai daga Anka da kuma uku daga Talata Mafara.

Sunayen waɗanda suka rasu sun haɗa da Shehu Lawali, Murtala Mesin, Ubandawaki Moda, Muhammad Want, Haruna Kwanar Maje, Ibrahim Ware Ware, Yusuf Ware Ware, Rabi’u Barbara, Lawali Dan Hassi Jangebe, da Badamasi Gima.

An yi jana’izarsu a Anka a ranar Lahadi, inda Gwamna Dauda Lawal ya halarta, tare da ɗaukar alƙawarin ci gaba da goyon baya wajen yaƙi da ’yan bindiga a jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari Jami an Tsaro kwanton bauna Zamfara jami an tsaro yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja

Rundunar sojin ba ta fitar da sanarwa ba game da wannan hari na baya-bayan nan, amma hukumar DSS ta tabbatar da faruwar lamarin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ZAMFARA: APC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Dauki Don Matsalar Tsaro Na Kara Tsananta
  • Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja
  • Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF
  • Ku Daina Kashe Mutane Ko Ku Miƙa Wuya – Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Bindiga
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 
  • Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati
  • ’Yan sa-kai aƙalla 100 da jami’an tsaro 30 sun mutu a bakin aiki a Katsina —Gwamnati