Isra’ila ta kashe wani mamba na ofishin siyasa na Hamas
Published: 23rd, March 2025 GMT
Wani sabon kazamin harin sojojin Isra’ila ya yi sanadin shahadar mutum 40 cikin sa’o’I 24 da suka gabata ciki har da Salah al-Bardawil, dan majalisar Falasdinu kuma mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas.
A cikin wata sanarwa da ta fitar yau, Hamas ta ce an kai wa Bardawil hari ne a wani hari na ” yahudawan sahyoniya na ha’inci”, a lokacin da yake gudanar da sallar dare a daren 23 ga watan Ramadan.
An kashe shi ne tare da matarsa a wani hari da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa da ke yankin al-Mawasi, yammacin birnin Khan Yunis na kudancin Gaza.
Kungiyar ta bayyana Bardawil a matsayin “alama ta siyasa, yada labarai,” da ayyukan bunkasa al’umma da yankin Falastinu.
Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, amma ta kasa cimma manufofinta duk da kashe Falasdinawa 49,747, galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu fiye da 113,213 a yankin da aka yi wa kawanya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kutsa Cikin Quneitra Na Kasar Siriya Tare Da Kafa Shingen Bincike
Rahotonni sun tabbatar da cewa: Da tsakar daren jiya Litinin wayewar garin yau Talata, sojojin mamayar Isra’ila dauke da motocin soji guda hudu da wasu sojoji masu tafiyar kafa sun kutsa cikin yankunan kasar Siriya daga titin Al-Hurriya, inda suka wuce titin Al-Kassarat, zuwa Talat Jabata Al-Khashab.
Majiyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya ta bayyana cewa: Sojojin mayar sun kafa shingen binciken ababen hawa inda suka tsaya suna binciken ababan hawa da ke wucewa, sannan suka haska wuta don gano hanyar kafin su fita ta hanyar da suka shiga. Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma suna shawagi a sararin samaniyar birnin Damascus fadar mulkin kasar ta Siriya.
A jiya Litinin ma, sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wasu sansanoni na rundunar sojin ta 36 ta musamman da aka fi sani da Ain al-Burj a gabashin kauyen Qala’at Jandal da ke cikin karkarar birnin Damascus, tare da kafa wani sansanin soji a saman dutsen Barbar domin sa ido kan motsin da ake yi a yankin.