Sudan Ta Haramta Shigar Da Kayayyakin Daga Kenya
Published: 14th, March 2025 GMT
Gwamnatin mulkin sojin Sudan ta ayyana haramta duka kayayyakin da aka shigar da su ƙasar daga Kenya, a wani mataki na martani karɓar baƙuncin RSF da ƙawayenta da Nairobin ta yi.
Ministan kasuwancin Sudan, ya ce an ɗauki matakin ne bisa shawarar, majalisar ikon ƙasar, wadda ta zargi Kenya da rura tashin hankali a Sudan.
A ganawar da aka yi a Nairobi ce, RSF ta yanke shawar kafa gwamnatin ƴan adawa a wuraren da take iko da su tare da sanya hannu kan abin da ta kira ‘rubuta kundin tafiyar gwamnatin’.
Sudan ce ƙasa ta 10 a duniya, sannan ta biyu a Afirka, cikin jerin ƙasashen da suka fi sayen ganyen shayin Kenya.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kenya
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
A ƙoƙarinta na ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa.
Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace gunduma ta yankin
A cewarsa, manufar horon ita ce koyar da mahalarta yadda za su samar da kariya yayin al’ada da kansu domin rage kashe kuɗi da kuma kare kansu daga kamuwa da cututtukan mahaifa.
Shi ma shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Shehu Sani Gwadayi, ya bayyana cewa tsafta na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan adam domin inganta rayuwa da ƙarfafa garkuwar jiki.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Muhammad Abdullahi, ya yi wa mahalarta horon bayani kan muhimmancin tsafta yayin al’ada domin gujewa kamuwa da cututtuka.
Shugaban ƙaramar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun Gabas, ya shawarci mahalarta da su mai da hankali ga sashen aikace-aikace na yadda ake sarrafa audugar mata a gida yayin horon.
Usman Muhammad Zaria