Kasar Sin Ce Ke Kan Gaba A Matsayin Kasar Da Ta Fi Samun Jari Daga Ketare
Published: 14th, March 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta ce alkaluma sun nuna cewa, har yanzu kasar Sin ce ke kan gaba a duniya a matsayin wacce ta fi samun jari daga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen wajen su zo su kara zuba jari.
Mao Ning ta kara da cewa, ba tare da la’akari da sauyin da za a gani a duniya ba, kasar Sin za ta cika alkawarinta na fadada bude kofarta.
Da take amsa tambaya game da manufar kasar ta daukewa wasu kasashe neman visa, Mao Ning ta ce kasar ta soke neman visa ga kasashe 38 da kuma tsawaita lokacin yada zango a kasar ba tare da visa ba zuwa sa’o’i 240 ga kasashe 54. Ta ce a bara, sama da baki miliyan 20 ne suka shigo kasar ba tare da visa ba, adadin da ya karu da kaso 112 kan na shekarar da ta gabace ta. Ta kara da cewa, kasar Sin za ta kaddamar da karin matakai domin saukaka shigowa kasar. Haka kuma, tana maraba da baki abokai daga fadin duniya, domin su zo su ganewa idanunsu kasar Sin ta ainihi mai kyau da bude kofa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu
Mujallar Qiushi ta kasar Sin za ta wallafi jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping gobe Jumma’a 1 ga watan Agusta, wanda Xi ya taba gabatarwa a gun babban taron kiyaye muhallin halittu na kasar Sin a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2023.
Jawabin ya bayyana cewa, bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin ta riga ta shiga sabon mataki na neman samun ci gaba mai inganci, wanda ke bukatar gaggauta kiyaye muhallin halittu da rage yawan iskar Carbon da ake fitarwa. Aikin kiyaye muhallin halittu na fuskantar matsin lamba. Ya kamata a yi kokarin zamanantar da kasar Sin bisa tushen samun daidaito a tsakanin bil Adama da muhallin halittu. (Kande Gao)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp