Jami’an NDLEA Sun Kashe Budurwa A Kano, An Damƙe Su
Published: 6th, March 2025 GMT
Jami’an hukumar yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Kano sun shiga hannu bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 19, Patience Samuel, a unguwar Jaba.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:55 na dare a ranar Laraba, inda rahotanni suka nuna cewa jami’an ‘yansanda sun kai ɗauki, suka kwashe ta zuwa Asibitin koyarwa na Abdullahi Wase, inda aka tabbatar da rasuwarta.
An kama jami’an biyu, Nass Ridwan Usman mai shekaru 23 da Ismaila Yakubu mai shekaru 26, waɗanda ke aiki a shalƙwatar NDLEA a Kano.
Har yanzu NDLEA ko ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa dangane da lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.