Mahara sun yi basaja da kayan EFCC wajen sace mutum 10 a otal
Published: 2nd, March 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga sun yi basaja a matsayin jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), tare da sace mutum 10 a Otal ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a Ƙaramar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja.
Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 4:58 na asubar ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun isa otal ɗin ne, inda suka yi basaja a matsayin jami’an EFCC da ke bakin aiki.
Sun fara da kashe na’urorin CCTV na otal ɗin kafin su kutsa cikin ɗakunan baƙi, inda suka kwashe mutum 10 suka tafi da su ba tare da sanin inda suka nufa ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ya ce suna gudanar da bincike don gano waɗanda suka aikata laifin da kuma ceto waɗanda aka sace.
Hukumomi sun buƙaci jama’a da su kasance masu sanya ido tare da sanar da hukumomin tsaro idan sun ga wani abin da ke da ɗaukar hankali.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Garkuwa hari Jami an Tsaro kaya mahara
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.
A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp