Ukraine ta cimma yarjejeniya da Amurka kan haƙar ma’adinai
Published: 27th, February 2025 GMT
Ukraine ta amince da wata yarjejeniya da Amurka kan haƙar ma’adinai da cinikayyar albarkatun ƙasa.
Ana sa ran sanar da yarjejeniyar a hukumance a yau Laraba, inda za a ba wa kamfanonin Amurka dama su shiga harkar haƙar ma’adinai a Ukraine, ciki har da man fetur da iskar gas.
Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N860 a Legas Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a BornoBisa ga bayanai, Amurka za ta samu wani kaso mai yawa daga ribar da za a samu, wanda zai iya kai wa Dala biliyan 500.
Duk da cewa ba a bayyana batun tallafin tsaro a cikin yarjejeniyar ba, ministar shari’ar Ukraine, Olha Stefanishyna, ta ce akwai wasu muhimman batutuwa da Ukraine za ta amfana da su.
A ranar Juma’a mai zuwa ne shugaba Volodymyr Zelenskyy, zai tafi Amurka don ganawa da shugaba Donald Trump domin kammala yarjejeniyar.
Ukraine za ta riƙa saka kaso 50 na ribar da ta ke samu daga ma’adinanta a wata gidauniya ta haɗin gwiwa da Amurka, kuma wani ɓangare na kuɗin za a yi amfani da shi wajen sake gina ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ukraine yarjejeniya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp