Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba
Published: 26th, February 2025 GMT
Jam’iyyar APC mai mulki, ta gudanar da babban taronta na ƙasa a Abuja, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar daban-daban.
Duk da kasancewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a waje taron, wasu manyan shugabannin jam’iyyar ba su halarci taron ba.
Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a Kano Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasaDaga cikin waɗanda ba su halarci taron ba akwai tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, da tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi.
Dangane da dalilin da ya sa Buhari bai samu halartar taron ba, tsohon mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa tsohon shugaban bai samu katin gayyata a kan lokaci ba.
“Taron masu ruwa da tsaki ne, wanda ya kamata Buhari ya halarta. Amma an aike masa da gayyatar taron ne a ranar Litinin, sai dai bai samu wasiƙar ba sai ranar Talata da rana.
“A wannan lokacin, ba zai iya barin Daura ya tafi Abuja don halarta ba, ko da kuwa yana da jirginsa na musamman.”
Duk da hakan, Garba Shehu ya jaddada cewa Buhari har yanzu cikakken ɗan jam’iyyar APC ne kuma zuciyarsa tana tare da ita.
Dalilin Rashin Halartar El-Rufai da AmaechiBabu cikakken bayani game da dalilin da ya sa Malam Nasir El-Rufai bai halarci taron ba.
Sai dai a baya, tsohon gwamnan na Kaduna ya sha bayyana rashin jin daɗinsa game da jagorancin jam’iyyar, inda zargi cewa ta sauka daga aƙidar da aka kafa ta.
Duk da haka, ya nanata cewar har yanzu shi cikakken ɗan jam’iyyar.
Shi ma Rotimi Amaechi bai bayyana dalilin rashin halartarsa ba.
A kwanakin baya dai, tsohon gwamnan na Ribas ya daina yawan magana a fili.
A wata hira da ya yi da BBC, ya ce: “Idan akwai abu guda ɗaya da na koya daga Shugaba Buhari, shi ne rage yawan surutu.
“Domin ya taba fada min cewa ‘Amaechi, ba don abinci kawai aka yi ciki ba.’“
Manyan Jiga-Jigan da Suka Halarci TaronDaga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai na jihohin Edo, Benuwe, Ondo, Ekiti, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Yobe, Nejs, Legas, Kogi, Ogun, da Imo.
Mataimakin gwamnan Ebonyi da wasu tsofaffin gwamnoni daga Kogi, Kebbi, Neja, Zamfara, da Filato su ma sun halarci taron.
Duk da rashin halartar wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar, babban taron ya gudana kamar yadda aka tsara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Buhari jam iyya taro tsohon gwamnan halarci taron babban taron
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Taya Sabon Firaiministan Kanada Mark Carney Murna
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama.
Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013 zuwa 2020.
Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa ƙwarewar sabon shugaban Kanada a fannin kuɗi da shugabanci za ta taka muhimmiyar rawa wajen gina makomar ƙasar. Haka kuma, ya sake jaddada kudirin Najeriya na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da Kanada, musamman a fannonin ilimi, sauyin yanayi da hijira.
Shugaban Najeriya ya ƙara da cewa yana fatan kafa kyakkyawan hadin gwiwa da gwamnatin Carney, yayin da ya nuna godiyarsa ga kyakkyawar alakar da aka kula a tsakaninsu a zamanin tsohon Firayim Minista, Justin Trudeau.
Bello Wakili