Iran Ta Kaddamar Da Kayakin Aiki Na Samar Da Maganin Wata Nau’in Cutar Cancer Ko Daji
Published: 26th, February 2025 GMT
Hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ta kaddamar da kayakin aikin da ake bukata don samar da garin sinadarin (Tellurium Dioxide) wanda ake hada maganin cutar daji wanda ake kira (Iodine-131) da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar hukumar makamashin nukliyar ta Iran, na cewa ana samar da wannan sinadarin ne tare da amfani da makamashin nukliya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: samar da maganin
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
A wani gagarumin ci gaba na inganta walwala da ci gaban yara da matasa wadanda suka isa makaranta, Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Farko ta Jihar Nasarawa NSUBEB, Dokta Kasim Mohammed Kasim ya karbi tawagar Kids & Teens Resource Center K&TRC a wani taron bayar da shawarwari da aka mayar da hankali kan shirin Ilimi don Lafiya da walwala, wanda UNESCO ke tallafawa.
An gudanar da babban taron ne a hedkwatar Hukumar NSUBEB, inda ya samu halartar kwamishinonin hukumar su uku, da Daraktoci da dama, da kuma tawagar K&TRC karkashin jagorancin wanda ya kafa kuma Shugaba, Mista Martin-Mary Falana.
Tattaunawar a yayin zaman ta tabo batutuwan da suka shafi rayuwar yara da matasa a jihar, wadanda suka hada da yawaitar cin zarafin mata kamar lalata da fyade, cin zarafi a makarantu, kananan yara da auren dole, kaciyar mata, da kuma yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Mahalarta taron sun amince da bukatar gaggawar samar da cikakken martani ta bangaren ilimi domin tunkarar wadannan kalubale.
Shugaban hukumar ya yi alkawarin ba da cikakken kudurin siyasa na hukumar tare da ba da tabbacin baiwa kungiyar K&TRC na NSUBEB goyon baya wajen samar da yanayi mai dacewa don samun nasarar aiwatar da aikin.
COV/Aliyu Muraki/Lafia.