Gwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Sama Da Naira Biliyan 5 Ga Wadanda Aikin Tituna Ya Shafa
Published: 26th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan Biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa.
Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.
A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na yanki suka gabatar.
Ya ce, majalisar ta kuma amince da kashe sama da naira biliyan takwas da miliyan dari biyu a matsayin kashi 30 bisa na kudaden shirin noman rani na shinkafa na shekarar 2025.
Ya kuma yi bayanin cewa, an amince da hakan ne da nufin samar da wadataccen abinci da inganta rayuwar miliyoyin al’ummar Jigawa ta hanyar bai wa Manoma 58,500 rance, don noma hekta 50,000 na shinkafa a fadin yankunan da ake noman shinkafa, kamar yadda ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta gabatar.
Kwamishinan ya ce, majalisar zartaswa ta jihar ta kuma amince da sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita wa’adin shekaru 2 tsakanin ma’aikatar lafiya ta gwamnatin jihar Jigawa da kungiya mai zaman kanta ta Medicins San Frontiers (MSF) da ke kasar Faransa.
A cewarsa, rattaba hannu kan yarjejeniyar na da nufin karfafa kokarin jihar na rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, ta hanyar samar da ingantacciyar kula ga masu juna biyu a babban asibitin Jahun da kuma cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na Miga da Ajura.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Manufar Sauyin Yanayi
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da taron wanda aka gudanar a dakin taro na Armani Event Centre dake Kano, Gwamna Abba Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Farouk ya wakilta, ya bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba a kokarin gwamnatinsa na mayar da jihar Kano a matsayin mai ci gaba a harkokin tafiyar da yanayi da muhalli.
Gwamna Yusuf ya jadadda cewa, manufar tana cike da shirin aiwatar da sauyin yanayi, wanda ke fassara kudirin siyasar gwamnati zuwa tsarin aiwatarwa a aikace.
Ya kuma yi tsokaci kan shirye-shiryen da gwamnati ke yi na samar da makamashi ta hasken rana da ababen more rayuwa.
Gwamnan ya nanata shirin gwamnatin sa na dasa itatuwa miliyan 5 a shekarar 2025 domin rage zaizaiyar kasa, da inganta iskan shaka, da inganta kyawawan birane.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO