Mai magana da yawun kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da ketare ya amsa tambaya da manema labarai suka gabatar masa kan takardar bayani a kan manufar “Zuba jari a Amurka ta zamanto farko” a gun taron manema labarai da aka gudanar a jiya Lahadi. Inda ya ce, bangaren masana’antu da kasuwancin Sin na matukar kin yarda da matakin da Amurka ta dauka, wanda ya yi gamin-gambiza da batun tsaron kasa wuri guda, sannan ya yi hannu riga kwata-kwata da tsarin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Kakakin ya kara da cewa, Amurka ta tsaurara matakan tsaro da nufin fakewa da guzuma ta harbi karsana a kan shigo da jari daga bangaren Sin a fannin kimiyya da manyan ababen rayuwa da kiwon lafiya da aikin gona da makamashi da kayayyakin da ake sarrafawa da sauransu, a hannu guda kuwa, ta yi yunkurin habaka takaita zuba jarinta a kasar Sin ta hanyar daukar matakan sanya takunkumi da tantance harkar kudade da sauransu. Kuma da zarar an aiwatar da matakan da ake dauka, za su kara tagayyara manufofin da kamfanoni za su aiwatar, zai yi matukar illa ga zaman oda da dokar cinikayyar duniya da haifar da rashin tabbaci ga tsarin samar da kayayyaki a duniya.

Kakakin ya ce, “Sin na kalubalantar Amurka da ta mutunta ka’idar kasuwanci da yin takara daidai wa daida, da kuma fahimtar ainihin iyakar batun tsaron kasar da soke kayyade zuba jari tsakanin kasashen biyu ta yadda za a shimfida yanayi mai yakini ga masana’antu da kasuwancin kasahen biyu kan hadin gwiwarsu ta moriyar juna.” (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

NEJERIYA A YAU: Sai Yaushe ’Yan Najeriya Za Su Ci Gajiyar Manufofin Shugaba Tinubu?

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A yau shekara biyu ke nan cif  tun bayan da  shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na 16 tun bayan samun ‘yancin kai.

 

Daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar ya fara yi yayin jawabin karbar mulkin shi ne sanar da kawar da tallafin man fetur.
Yayin da yake cika shekaru biyu, ana ci gaba da muhawara mai zafi game da irin nasarorin da aka samu da kalubalen da ake fuskanta da kuma yadda al’ummar ƙasa ke amfana da tsare-tsaren gwamnati.

NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada”

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu daga cikin muhimman manufofin Shugaban Kasa Bola Tinubu a cikin shekara biyu, da yadda suka shafi rayuwar ’yan Najeriya.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Rasu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Neja
  • Ɗalibai sun maƙale lokacin da gini ya rufta suna jarrabawa
  • NEJERIYA A YAU: Sai Yaushe ’Yan Najeriya Za Su Ci Gajiyar Manufofin Shugaba Tinubu?
  •  Kasar Chile Na Shirin Yanke Alakar Diplomasiyya Da “Isra’ila”
  • Shugaban  Iran na ziyarar aiki a kasar Oman
  • Araghchi: “Ba ma wasa game da batun inganta uranium, wanda hakkin al’ummar Iran ne”
  • Masu Bincike Na Sin Sun Cimma Sabon Sakamako A Fannin Saurin Sadarwa Tsakanin Tauraron Dan Adam Da Doron Duniya
  • Kasar Ireland Ta Yi Dokar Hana Shigar Da Kayan Da Aka Kera A ” Isra’ila” Cikinta
  • Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Nuna Misali Na Bude Kofa Da Raya Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da ASEAN Da GCC
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Dole Ne A  Dauki Kwararan Matakan Don Dakatar Da Laifukan Gaza