Jakadan Sin Dake Najeriya Ya Gana Da Karamar Ministar Harkokin Wajen Kasar
Published: 20th, February 2025 GMT
Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu.
Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, wanda ya zama babban ci gaba ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A nata bangare, madam Bianca Odumegu-Ojukwu ta bayyana cewa, shugaba Tinubu ya kai ziyara kasar Sin a shekarar bara, lamarin da ya shaida cewa, Najeriya tana maida hankali ga raya dangantakar dake tsakaninta da Sin. Ta ce kasar Najeriya ta tsaya tsayin daka kan manufar Sin daya tak, kuma tana son hada hannu da kasar Sin wajen aiwatar da ayyukan da aka cimma a ganawar shugabannin kasashen biyu da taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na Beijing, ta yadda za a inganta hadin gwiwar kasashen biyu har ya amfanawa jama’arsu baki daya. (Zainab Zhang)
কীওয়ার্ড: dangantakar dake tsakanin
এছাড়াও পড়ুন:
Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba
Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba.
Basil Khairudden wakilin gidan talabijin na Al-Alam a Gaza, ya ce: “A ranar Juma’a, shi da iyalinsa da daukacin al’ummar Gaza ba su iya samun ko da biredi guda da za su ci ba, sakamakon yunwa da ake fama da ita a Gaza.”
Ya tabbatar da cewa a Gaza akwai mutanen da ba su ci abinci ko da sau daya a tsawon kwanaki uku. A ranar Juma’a mutanen Gaza sun yi ta yawo a kasuwanni, tituna, da unguwanni ba tare da samun kilo guda na gari ba.