Kungiyoyin Falasdinawa A Gaza Sun Bukaci Yin Taron Musamman Domin Dakile Batun Tilasa Wa Mutanen Gaza Yin Hijira
Published: 20th, February 2025 GMT
Kungiyoyin Falasdina mabanbanta sun yi kira da a gudanar da taron musamman na al’ummar Falasdinu domin a tattauna hanyoyin da za a dakile batun tilastawa mutanen Gaza yin hijira.
Kungiyoyin na falasdinawa sun bayyana hakan ne dai a wani taro da su ka yi a Gaza domin karfafa gwiwar mutanen wannan zirin su ci gaba da jajurcewa da tsayin dakar da suke yi, tare da kara da cewa; Babu yadda za a yi al’ummar Falasdinu su fita daga kasarsu.
Mahalarta taron na Gaza sun bayyana furucin da shugaban kasar Amurka ya yi akan fitar da Falasdinawa daga Gaza da cewa yana nuni akan yadda Amurka da ‘yan sahayoniya su ka yi tarayya a laifukan da aka tafka akan Falasdinawa, haka nan ita kanta wannan maganar tana nufin shelanta wani sabon yakin akan al’ummar Falasdinu da hakan yake da bukatar fitar da wani matsayin na kasashen larabawa da kuma kungiyoyin kasa da kasa.
A karshe sun bukaci ganin cewa taron kasashen larabawa da za a yi nan gaba kadan, ya fito da wani tsari na ci gaban al’umma, saboda kawo karshe duk wani batu na yin hijira. Haka nan kuma sun bukaci ganin masu alaka da ‘yan mamaya daga cikin larabawa sun yanke ta.
Jami’in da yake kula da tuntubar juna a tsakanin kungiyoyi mabanbanta Khalid al-Badhash ya bayyana cewa; Duk da baranazar da hakkokin falasdinawa suke fuskanta, da kuma makirece-makircen Amurka, sai dai kuma batun kare hakkokin Falasdinawa ya sake dawowa da karfi a duniya, kuma duniyar ta gane hakikanin ‘yan mamaya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA