Mujallar “Qiushi” Ta Gabatar Da Muhimmin Sharhin Xi Jinping Game Da Inganta Tsarin Daukar Kwararan Matakai Wajen Kula Da Harkokin Jam’iyya
Published: 16th, February 2025 GMT
Mujallar “Qiushi” da aka buga a yau Lahadi, ta gabatar da muhimmin sharhi na sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping mai taken “Inganta tsarin daukar kwararan matakai wajen tafiyar da jam’iyya a dukkan fannoni”.
A cikin sharhin an nuna cewa, har yanzu ana fuskantar matsanancin yanayi da sarkakiya wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta dade tana fuskantar wannan jarrabawar.
কীওয়ার্ড: ta kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
A wani yunkuri na inganta kula da mata masu juna biyu da sauran ayyukan kiwon lafiya a jihar Jigawa, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF tare da hadin gwiwar Karamar Hukumar Kirikasamma sun mika kayayyakin aiki da wasu muhimman kayayyaki ga cibiyar kiwon lafiya ta farko a Kirikasamma.
Mai kula da cibiyar kiwon lafiya ta farko, Kabiru Musa, ya bayyana cewa kayayyakin sun haɗa da gadajen haihuwa, zannuwan gado, kayan aikin jinya, matashin kai da sauransu, kuma za a rarraba su zuwa wuraren kiwon lafiya a fadin karamar hukumar.
A cewarsa, kayan da UNICEF da karamar hukumar suka samar za su inganta yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya a yankin.
Yayin mika kayayyakin ga mai kula da cibiyar kiwon lafiya, shugaban karamar hukumar Kirikasamma, Alhaji Muhammad Maji Wakili Marma, ya bukaci ma’aikatan lafiya da su tabbatar da gaskiya da adalci a lokacin rabon kayan.
Haka kuma, ya yaba da kokarin Gwamna Umar Namadi da sauran abokan hulda wajen gyara cibiyoyin kiwon lafiya da gina gidajen Ungozoma a Kirikasamma da kuma fadin jihar domin inganta ayyukan kiwon lafiya.
Usman Muhammad Zaria