Amurka Ta Bai Wa HKI Bama-Baman MK-84 Guda 1800
Published: 16th, February 2025 GMT
A yau Lahadi ne HKI ta sanar da cewa, bama-bamai samfurin MK-84 har guda 1800 da kowane dayansu yake da nauyin ton daya da Amurka ta bata, sun isa tashar jirgin ruwa ta Oshdud.
Majiyar ta kuma ce tuni aka dauki bama-baman daga tashar jirgin ruwan zuwa filayen jiragen sama.
Jaridar “Maariv” ta ce makaman da Amurka ta bai wa Amruka ta kai yawan ton 76,000 da ana shigar da su ne ta sama da kuma ruwa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Ayyukan Sadarwa
Kasar Sin ta cimma nasarar harba sabon tauraron dan’adam na ayyukan sadarwa mai suna Tianlian II-05, daga tashar harba kumbuna ta Xichang dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar.
An harba tauraron ne da karfe 12 saura mintuna 6 na tsakar daren jiya Lahadi agogon Beijing, ta amfani da rokar Long March-3B, kuma tuni ya shiga da’irarsa kamar yadda aka tsara.
Tauraron zai rika samar da hidimomin musayar bayanan sadarwa ga kumbunan sama jannati, irin su kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati, da tashar binciken sararin samaniya, domin nasarar ayyukan taurarin dan’adam marasa nisa da doron duniya, da taurarin dan’adam masu taimakawa aikin harba kumbuna.
Wannan ne karo na 572 da aka yi amfani da roka samfurin Long March wajen harba tauraron dan’adam na Sin zuwa samaniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp