Aminiya:
2025-08-01@16:08:12 GMT

Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙura

Published: 13th, February 2025 GMT

A karo na biyu a kasa da wata daya wasu ’yan bindiga sun mika makamansu ga sojoji, a wani kokari na samar da zaman lafiya.

Aminiya ta ruwaito yadda a a ranar 19 ga watan Janairun 2025, ’yan bindiga suka sallama makamansu da mutanen da suka yi garkuwa da su, a wani zaman sulhu da aka yi da su a yankin Ƙaramar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.

Sojoji da jami’an hukumar tsaro ta DSS da sarakunan gargajiya da mazauna sun halarci zaman na ranar Lahadi a ƙauyen Kofa da ke kid da garin Batsari. A wannann karoj manyan ’yan bindiga irin su Umar Black, Abdullahi Lankai da Jijjige da Musa Dan Gandu da Abu Radda, da sauransu, waɗanda d suka adsabi yankunan Batsari da Jibia da Safana, ne suka ajiye makamainsu. Fitaccen ɗan siyasa Ahmadu Haruna Zago ya rasu Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Sani samu rabuwar kai Ajiye makaman da ’yan ta’addan suka yi ya haifar da rabuwar kai a tsakanin mutane inda wasu ke yabawa tare alaƙanta shi da tsananta ragargazar da sojoji ke wa ’yan ta’adda.

A gefe guda kuma wasu kuma na zargin Gwamnatin Tarayya Nana hannu wajen yin sulhu da ’yan ta’addan ta bayan fage domin a sami zaman lafiya a Jihar.

Al’ummar Batsari sun halarci taron mika malaman inda sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta. Wasu na ganin abin yabo da da ta kamata a ba wa goyon, wasu kuma na ganin sa a matsayin tarin shayi, saboda an mayar da al’ummar da hare-haren suka shafa saniyar ware.

Wani mazaunin yankin ya ce, “Ba a gayyace mu ba amma na je na ga abin da aka yi. Kimanin motoci takwas na APC da hiluxs ɗauke da sojoji da ’yan sanda da jami’an tsaron CWC da ’yan banga.

“Na ga ’yan bindigar sun miƙa wa sojoji bindigogi biyu ƙirar Machine Gun sun neman a basu damar shiga garuruwanmu da kasuwanninu ba tare da wani ƙaido ba.

“Duk da cewa ba duk makamansu suka miƙa ba, amma na yi imani abu mai kyau ne kuma ya kamata a dama da duk hukumomin tsaro,” in ji shi. Wani ɗan yankin kuma ya ce babu yadda za a yi sulhun ya yi nasara ba tare an sanya mutanen ya yankunan da abin ya shafa ba. Ya ce, “a na farkon da ka yi, kawai jerin gwanon motocin jami’an tsaro muka gani suna zuwa wurin. Shi ne wasunsu suka je, inda suka ga ’yan bindiga sun mika musu bindigogi biyu. Haka kuma aka yi a na biyun da ka yi jiya. “Amma ban je na jiyan ba, saboda ina tunanin babu abin da zai tsinana,” in ji shi. Gwamna Radda ya jaddada matsayinsa Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, wanda ya ziyarci Batsari ya jaddada matsayinsa cewa gane da sulhu da ’yan bindigar cewa gwamnatinsa ba za ta roƙe su ko ta lallashe su su miƙa makamansu ba.

Ya ce “mun sha faɗa cewa babu ɗan bindigar da za mu je mu roƙe shi don a samu zaman lafiya. Amma idan su da kansu suka zo suka miƙa wuya za mu karɓe su,” in ji a yayin wani gangamin yaƙin nemba Batsari gabanin zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a gudanar ranar Asabar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Batsari yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Zaɓen 2027: Arewa Za Ta Sake Mara Wa Tinubu Baya — Gwamna Inuwa

Sauran sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci da hafsoshin tsaro.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Cika Alƙawurran Da Ya Ɗauka – Ƙungiyar Gwamnonin Arewa
  • Shekara 2 Ta Gwamnatin Tinubu: Gwamnonin Arewa Sun ƙaryata Zargin ACF Na Watsi ɗa Yankin
  • ‘Yan Sandan Niger Sun Hada ‘Yan’uwa Mutanen 35 Da Aka Ceto Da Iyalansu 
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Zaɓen 2027: Arewa Za Ta Sake Mara Wa Tinubu Baya — Gwamna Inuwa
  • Ku Daina Kashe Mutane Ko Ku Miƙa Wuya – Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Bindiga