Aminiya:
2025-07-30@23:31:27 GMT

Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’

Published: 13th, February 2025 GMT

An shiga ruɗani bayan da wasu sojoji sun lakaɗa wa wasu ’yan sanda da ke bakin aiki duka a Ƙaramar Hukumar Okpe da ke Jihar Delta.

Rikicin jami’an tsaron ya samo asali ne bayan ’yan sanda sun yi kamen wasu matasa da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

’Yan sanda sun tsare motar matasan ne a yayin wani samame, inda suka kama ɗaya daga cikinsu da loud da wiwi, bayan sauran sun tsere.

Suna tsaka da tafiya da shi zuwa ofis ne suka bi ta wani shigen bincike na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, suka umarce su da su sake shi.

Bayan ’yan sandan sun ƙi amincewa suka nemi a bi ƙa’ida ba ne, rikici ya ɓarke a tsakaninsu. A garin haka ne sojojin suka lakaɗa wa ’yan sandan duka.

Kakakin ’yan sandan Jihar Delta, SP Edafe Bright, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da cin mutunci, mara dalili.

Ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da aiki cikin kyakkyawan alaƙa da sauran hukumomin tsaro.

Jami’in ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike a kan lamarin da nufin ɗaukar mataki da nufin daƙile aukuwar hakan a nan gaba.

Yunƙurin wakilinmu na jin ta bakin rundunar Sojin sama kan lamarin bai yi nasara ba.

Al’ummar gari dai sun bayyana buƙatar sun bukaci jami’an tsaron su kai zuciya nesa tare da kyautata hulɗa a tsakaninsu.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa Ibom

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura
  • ‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 
  • EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa Ibom
  • Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa
  • Araqchi: Tattaunawar Nukiliya Wani Zabi Ne Mai Muhaimmanci Wanda Ya Karfafa Matsayin Iran A Duniya
  • An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja
  • An gano gwawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja