HausaTv:
2025-05-01@16:00:32 GMT

MDD Ta Yi Gargadi Akan Halin Da Ake Ciki A DRC

Published: 6th, February 2025 GMT

Kungiyar M 23 mai samun goyon bayan Rwanda ta kara samun gindin zama  a gabashin kasar DRC, duk da cewa ta sanar da tsagaita wutar yaki ta gefe daya a jiya Laraba.

Mayakan na M 23 sun sanar da kame babban binin gundumar Bukavu.

Wani jami’in MDD wanda ya isa garin Goma ya bayyana cewa, Da akwai  yiyuwar barkewar wani sabon rikici.

 MDD ta ce har yanzu ana ci gaba da yaki tsakanin sojojin gwamnati da kuma  mayakin na kungiyar M 23.

Garin Goma da mayakan na M 23 su ka  kwace iko da shi, yana da  ma’adanai kwance a kasansa da aka yi  kirdadon cewa kudadensa sun kai na biliyoyin daloli.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

HKI Tana Amfani Yunwa A Matsayin Makamin Yaki  A Kan Falasdinawa A Gaza

Wakilin falasdinawa a kutun kasa da kasa ta ICJ da ke birnin Haque na kasar Nerthelands yace HKI tana amfani da hana kayakin agaji daga ciki har da abinci shiga gaza a matsayin makami kan Falasdinawa don kashesu.

Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ammar Hijazi jakadan kasar Faladinu a cibiyoyin MDD a kasashen Turai yana fadar haka a gaban alkalai a kotun ta ICJ a jiya litinin.

Ya ce  HKI tana kisa ta sama da makamai, sannan tana kisa ta kasa da yunwa banda haka tana ci gaba da korar  Falasdinawa daga yankin yamma da kogin Jordan tun fiye da watanni 3 da sua habata.

Kutun ta bude wannan zaman ne bisa bukatar MDD ta shekara ta 2024 na bincike don tabbatar da cewa HKI tana amfani yunwaa a matsayin makami a Gaza. Ammar Hijazi ya kara da cewa banda wannan babban kotun HKI tana goyon bayan amfani da yunwa a matsayin makami a gaza tun fiye da watanni 2 da suka gabata.

Wasu lauyoyi daga kasashe daban–daban wadanda suka hada da Nerthlands da Afirka ta kudu duk sun yi magana sun kuma yi allawadai da HKI kan abinda take aikatawa a Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka Da Ukraine Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyar Da Aka Dade Ana Saurarunta Dangane Da Ma’adinai
  • Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
  • Kar A Mika Wuya Ga “Damisar Takarda”
  • Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
  • Katafaren Jirgin Daukar Jiragen Yaki Na Kasar Amurka Harry Truman Zai Fice Daga Tekun Maliya
  • NEMA Ta Karɓi ‘Yan Nijeriya 203 Da Suka Maƙale A Libya
  • Talauci Da Rashin Ilimi Ne Ya Sa Ayyukan Boko Haram Ke Dawowa – Gwamnan Yobe
  • Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
  • HKI Tana Amfani Yunwa A Matsayin Makamin Yaki  A Kan Falasdinawa A Gaza
  • Makafi 37 Sun Zana Jarabawar JAMB A Bauchi